Taron na baje-kolin wakokin Afirka da wakokin zube da raye-raye da rubuce-rubuce da ake yi a kasar Côte d'Ivoire karkashin Kungiyar MASA shi ne karo na 13.
Taron wanda ake yin mako daya ana yi, zai fara ne daga ranar 20 ga Afrilun kuma kungiyoyin masu fasashohi daban-daban guda 35 ne za su halarci taron daga kasashen duniya 13. A karshe za a yi gasa, wadda wasu alkalai za su sanar da zakaru.
Taron wanda aka fara a shekarar 1993 domin tallata ayyukan fasashohin dabe a idon duniya, yanzu ya rikide zuwa wani gagarumin taron da kasashen nahiyar baki daya suke halarta, sannan kuma ana tsammanin halartar akalla baki guda 150,00, kamar yadda masu shirya taron suka bayyana.
Taron yana samun mahalartar masu fasashohi daban-daban da masu sha'awar harkar daga fadin kasashen Afirka ta Yamma da ma wasu kasashen duniya. Taken taron na bana shi ne: Matasa, kirkira da kasuwanci: Madogarar ci gaban masu fasahohi a Afirka.
Ana tsammanin akalla tarukan baje-koli guda 30 ne za a yi a taron na bana, kamar yadda Yacouba Sangaré, Manajan Sadarwa na MASA ya bayyana a tattaunawarsa da TRT Afrika.
An zakulu su ne daga wadanda suka fara nuna sha'awar shiga taron da suka kai 632 daga kasashe 32.
Tun lokacin da aka assasa taron, MASA ta zama wani dandamali da ke ba matasan masu fasahar damar bayyana baiwarsu tare da karfafa gwiwarsu da karfafa fahimtar juna, wanda hakan ke jawo hadin kai da ci gaban bangaren.
"A bana taron baje-kolin zai cika shekara 30 da farawa," inji Mista Sangaré.
Kungiyar Ecowas ma ta bayyana goyon bayanta ga taron baje-kolin na MASA. Zakarun bangaren wakokin baka za su lashe kyautar Dala 2,000, masu dirama kuma dirama za su lashe kyautar Dala 3,000.
"Ecowas ce ta tallafa da kudi sannan ta ba da gudunmuwa matuka wajen shirya taron na bana na birnin Abidjan. Wannan ya nuna kokarin da jagororin yankin ke yi na amfani da fasashohi da al'adu wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kan yankin," kamar yadda ya bayyanawa TRT Afrika.
An assasa MASA ne domin tallata masu fasashohi da fasashohinsu a Nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.
A shekarun da suka gabata, an samu nasarar shiga kwantiragi tsakanin wasu masu fasashohi da masu tallata ayyukan fasaha sannan an horar da masu fasahar domin su inganta ayyukansu, wadanda suna cikin nasarorin da taron ya samu.
"Burinmu shi ne taron baje-kolin MASA ya sa mu kara alfahari da kasancewarmu 'yan Afrika, ba mu rika tunani ko kwaikwayon wasu kasashen ba," Sangaré.