Daga Pauline Odhiambo
Farkon lokacin da ya fitar da wani bidiyon wasa barkwancinsa a kafofin sadarwa, shi kan shi Seyi Adeyeye bai yi tunanin zai ja hankalin mutane ba, har ya kai ga samu dubban mabiya.
Wasannin barkwancin Seyi, wadanda yake yi a kan yanayin rayuwar marasa aure, yawanci suna zuwa masa ne a dalilin tattaunawar da ya yi da abokansa.
Yawancin abokaina ba su da aure, sannan duk lokacin da muka fita shakatawa, mukan tattauna abubuwan da suka shafi rayuwar marasa aure muna dariya, inji mai wasan barkwancin dan Nijerya a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Bayan kuma tattaunawa da abokansa, Seyi yakan yi amfani da abubuwan da suka faru da shi a rayuwa a matsayinsa na matashi mara aure wajen shirya wasanninsa, inda yake bayyana yadda marasa aure suke ji, da yadda hakan ke zama kalubale ga rayuwarsu.
Abubuwan da ake tattaunawa
Burina shi ne in kirkiri abubuwan da za su rika ba marasa aure dariya idan suka kalla. Ina so ne in rika kawo musu abubuwan da za su rika debe musu kewar rashin aure, inji mazaunin Amurkan, wanda ya fara fitar da bidiyoyin wasan barkwancinsa a kafofin sadarwa a shekarar 2023.
Bidiyoyin Seyi sun yadu sosai, inda daga cikin masu yada su har da jarumar masanaantar fim ta Amurka wato Hollywood, Tiffany Haddish.
“A matsayina na mai wasan barkwanci, aikina shi ne dauko wasu abubuwan da suke wakana, in mayar da su abubuwan nishadi, in ji shi.
Kalubalen shi ne yadda za a mayar da wadannan abubuwan su koma cikin nishadi ba tare da canja sakon ba, ta yadda ba wai wayar da kai za a yi ba kawai, har da karfafa gwiwar mutane.
Wani abu da ya yi wasan barkwanci a kai na kwanan-nan shi ne zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a Nijeriya, inda dubban matasa suka fito a manyan biranen kasar suna kalubalantar gwamnati a kan tsadar rayuwa.
Sai na shirya wasan barkwanci cikin nishadin cewa marasa aure maza za su fita zanga-zangar da niyyar haduwa da wasu marasa auren mata, inji shi, sannan ya kara cikin dariya cewa, yadda abubuwa suka yi tsada yanzu, mutane da dama sun daina zuwa soyayya. Don haka nake tunanin wannan zai zama wata yar damar a gare domin fita zanga-zangar.
Sunan Seyi Buzz da ake kiran mai wasan barkwancin ya samo asali ne daga karfin gwiwar kudar zuma, wadda a cewar masana suke taimakon mutane wajen cigaba da rayuwa ta hanyar samar da abinci. A cewar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Noma ta Majaisar Dinkin Duniya, samar da abinci na duniya na da alaka da zuma.
Sunana Seyi an takaice fadin cewa ne Allah mai iko ko kuma, Aikin Allah ne, wannan ya sa na yi tunanin kara Buzz, wanda shi kuma yake nufin karfin gwiwa.
Seyi wanda ya karanci bangaren kimiyyar kididdiga da inshora, ya koma Amurka daga Nijeriya ne a shekarar 2021 domin kara karatu.
Wannan ya ba shi damar samun aiki a kamfanin Microsoft, inda har yanzu yake aiki.
Samar da daidaito
“Ina wasan barkwanci ne kawai saboda shaawa, sannan ya saka ni farin ciki. Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne yadda ba na iya aikin wasannin a ranakun aiki saboda ba zan samun natsuwar shirya wasan da kuma nadarsa ba.
A 2015 cibiyar kididdiga ta Ibis World ta yi hasashen cewa masanaantar wasan barkwanci a Amurka za ta kai darajar Dala $344.6m a 2020. Masanaantar wasan barkwanci ta duniya kuma yanzu ta kai darajar samar da Dala biliyan 8 kamar yadda kididdigar World Metrics ta nuna.
Seyi yana da kwarin gwiwar shi ma za a dama da shi a wannan fadadar ta masanaantar.
Ina fata watarana wasan barkwancina zai wuce kafofin sadarwa kawai zuwa nishadantar da mutane a wuraren taruka, inda zan ba mutane marasa aure dariya cikin nishadi.
Idan na cigaba da dagewa, watakila watarana zan iya assasa wani shiri a manhajar Netflix inda zan rika fitar da bidiyoyin wasannin barkwanci.
Idan Seyi ya samu dama a karshen mako, yakan yi bidiyoyi kusan 40 wadanda zai rika fitarwa na kusan wata daya a hankali.
Idan wani tunanin wasan barkwanci ya zo min a cikin ranakun mako, sai in rubuta in ajiye domin nadarsa a karshen mako domin gudun kar su dauke hankali daga aikina, wanda hakan ya sa nake iya samar da daidaito.
Amma Seyi ba a ranakun karshen mako kawai yake nishadantar da kansa ba.
Yana buga kwallon kafa da abokansa da sauran harkokin wasannin bayan lokacin aiki.
Za ka iya yin nishadi a kullum idan kana so. Abin takaici shi ne yadda wasu suke farin ciki a ranar Jumaa, sannan su rika bakin ciki da zarar Litinin ta zagayo.
Yawancin mabiya Seyi, wadanda mafi yawansu mazauna Afirka da Amurka ne, suna son kasancewa cikin nishadi ne a kullum.
Kusan kashi 32 na mabiyana a Amurka suke, sannan kusan kashi 35 a Nijeriya. Haka kuma ina da mabiya daga Kenya da Ghana. Sannan akwai wasu daga kasashen Turai irin su Bengium da Netherlands.
Wasu daga cikin mabiyansa suna kuma tambaya suke a kan ko yana da aure, inda suke jiransa ya fitar da bidiyonsa domin tambayarsa.
“Kusan kullum sai wani ya tambaye ni ko ina da aure, idan na amsa da cewa ba ni daure sai su ki yarda. Wasu daga ciki cewa suke yi, idan da gaske ba ka da aure kamar mu, me ya sa kake zolayarmu?
Amma ina ganin ai rashn aure ba wani abu ba ne mara kyau. Ban ga laifi ba don mun mayar da shi wasan barkwanci.
Auren wanda ya dace
Seyi ya yi amannar cewa akwai bukatar mutum ya natsu kafin ya zaba wanda ya kamata ya aure kafin a fara soyayya.
Ni ba mara auren nan mara kangado ba ne. Nima ina da fahimtar irin ta mutanen nan da suke so su natsu wajen zabar matar aure. Sannan zan cigaba da yin wasan barkwanci ko bayan na yi aure saboda masu bibiyata.
Amma Sayi ya bayyana shirinsa na fadada wasannin barkwancinsa zuwa wasu bangarorin na rayuwa.
Shawararsa ga masu wasan barkwanci masu tasowa: Ba dole ba ne sai ka mallaki manyan kayan aiki za ka fara wasan barkwanci. Nishadin ne ke jawo mutane.
Idan kana da wayar da za ta iya nadar bidiyo, za ka iya farawa, sannan kada ka bata lokaci wajen dogon tunani. Kar ka kuma damu da maganganun mutane masu kushe, ka fi mayar da hankalinka a kan wadanda suke karfafa maka gwiwa.