Daga Brian Okoth
Sarauniyar Kyau ta Botswana ta shekarar 2022, wadda kuma ita ce Sarauniyar Kyau ta Duniya ta Afirka a 2024, Lesego Chombo ta zama sabuwar ministar matasa da harkokin jinsi ta Botsawana.
A ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba Shugaban Ƙasa Duma Boko ya naɗa matashiyar Chombo mai shekara 26.
Sarauniyar Kyan tana daga cikin ministoci shida da aka naɗa a sabuwar gwamnatin ta Shugaba Boko, inda har yanzu ba a naɗa sauran ministoci 12 ba.
Shugaban Ƙasar, wanda ya yi wa 'yan jarida bayani a Gaborone, babban birnin Botswana a ranar Litinin, ya ce nan ba da daɗewa ba za a sanar da sauran naɗe-naɗen.
Ministan Lafiya mai shekara 30
Mataimakin Shugaban Ƙasa Ndaba Gaolathe shi aka ba wa muƙamin ministan kuɗi.
Gaolathe, wanda ke cikin shekarunsa na 50, yana da digiri a fannin lissafi daga wata jami'ar Amurka, sai kuma digir na biyu a fannin harkokin kasuwanci ita ma daga wata jami'ar a Amurka.
Stephen Modise, wani likita da ya yi karatunsa a ƙasar waje, shi aka bai wa muƙamin ministan lafiya. Modise, wanda zaɓaɓɓen ɗan majalisar dokoki ne, yana cikin shekarunsa na 30.
Sai kuma ƙaramin ministan lafiya na Botsawana Lawrence Ookeditse, wanda shi ma ɗan majalisar dokoki ne daga mazaɓar Nata-Gweta.
UNICEF ta yaba wa sabuwar ma'aikatar
Micus Chimbombi, wanda dan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazabar Kgalagadi ta Kudu, zai kasance ministan filaye da noma na Botswana.
Shi kuwa Edwin Dikoloti, ɗan majalisa mai zaman kansa da ke wakiltar mazaɓun Good hope/Mmathete, zai zama ƙaramin ministan filaye.
Shugaba Boko ya kuma naɗa Dr. Nono Kgafela-Mokoka mai shekara 59 a matsayin ministan sabuwar ma'aikatar walwalar yara da ilimi a matsakin farko.
Asusun Kula da Yara na MDD, UNICEF ya yaba wa shugaban ƙasar kan ƙirƙirar sabuwar ma'aikatar, yana mai cewa a ranar Litiin: "Wannan abu zai taimaka ƙwarai wajen tabbatar da cewa batun hakkokin yara zai ci gaba da kasancewa a cikin muradun ƙasar."
Zaɓar matashiya kamar Chombo ya ƙayatar
An nada Dr. Phenyo Butale, dan majalisar wakilai mai wakiltar Gaborone ta tsakiya, kuma masani a fannin adabi, a matsayin ministan huldar kasa da kasa na Botswana, kwatankwacin ma'aikatar harkokin waje a wasu kasashe.
Ministoci da mataimakan ministoci da aka naɗa sun fara aiki nan take.
Yayin da gwamnatin Shugaba Boko ta fara aiki, an yaba wa nadin matashiyar Lesego Chombo a matsayin minista daga bangarori daban-daban ciki har da hukumar kula da mata da jinsi da matasa ta Tarayyar Afirka.
Kungiyar ta wallafa a shafin X cewa nadin ya samar da "dandali ga matasa don jagoranci, kuma su kasance a sahun gaba wajen tsara manufofi."
'Tasirin yi wa al'umma hidima'
Shugaba Boko ya ce ya bai wa Chombo muƙamin ministar matasa da harkokin jinsi saboda tasirinta na "ayyukan al'umma."
Ayyukanta sun haɗa da kare hakkin yara da walwala, da kuma yin magana game da cin zarafin mata.
A lokacin da yake kaddamar da Chombo a matsayin sabuwar ministar matasa, Shugaba Boko ya ce: "Ban san ta ba, ban gana da ita ba sai na dan takaitaccen lokaci bayan da aka tabbatar da ita a matsayin zababbiyar 'yar majalisa ta musamman. Kuma na ce mata: 'Ni da ke ba mu san juna ba sai a yanzu da muka hadu'."
Chombo, wadda ta kammala karatunta a Jami'ar Botswana, tana da digirin farko a fannin shari'a, kuma lauya ce a Babbar Kotun Ƙasar Botswana.
Sarauniyar Kyawun Afirka
Ta ci gasar Sarauniyar Kyau ta Miss Botswana ta 2022 daga rukunin masu takara 30 a watan Oktoba na wannan shekarar.
Ta wakilci kasarta a Gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya ta 2024 a birnin Mumbai na Indiya a watan Maris.
A fafatawar, ta fito a cikin hudun farko, bayan masu takara daga Jamhuriyar Czech da Lebanon, da Trinidad da Tobago.
Da yake ita ce babbar wakiliyar Afirka, an ba ta kambin Sarauniyar Kyau ta Duniya ta Afirka ta 2024.
A Botswana, ana zabi ministocin gwamnati daga majalisar dokoki, tare da wasu kadan daga wajen majalisar.