A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan Gasar Sarauniyar Kyau ta Afrika ta Kudu ta 2024 da ke gudana, hankula sun karkata kan ɗaya daga cikin ‘yan takarar a matakin ƙarshe, Chidinma Vannesa Onwe Adetshina.
A cikin bidiyonta na shiga gasar, dalibar koyon shari'a ta Kwalejin Varsity ta Afirka ta Kudu ta gabatar da kanta a matsayin 'yar shekara 23 daga Cape Town.
Duk da haka wasu 'yan Afirka ta Kudu ba su gamsu da cewa 'yar asalin ƙasar ba ce kuma suna son a hana ta.
Wasu masu amfani da kafofin sada zumunta kuam watsi suka yi da sunanta, wanda na 'yan Nijeriya ne.
Ta rubuta a shafinta na X cewa "Kiyayyar da ake nuna wa yan Nijeriya abun takaici ne wanda bai dace ba... zagin da ake min a wannan kafar ya yi yawa....'yan Afirka su zauna lafiya su haɗa kai!!!"
Da take mayar da martani kan wulaƙncin da ake mata, Adetshina ta kare tushenta, inda ta ce ta cika sharuddan takarar neman kambun kyau na Miss SA.
“Ni 'yar ƙasar Afirka ta Kudu ce, kuma na cika dukkan sharuddan shiga Gasar Sarauniyar Kyau ta Miss SA. Kasancewar mahaifina ɗan Nijeriya ne bai hana ni zama 'yar Afirka ta Kudu ba, mahaifiyata ‘yar kasar Afirka ta Kudu ce, kuma a kasar nan aka haife ni kuma na girma,” in ji ta.
Masu shirya Gasar Miss South Africa sun tabbatar da cewa Adetshina ta cika dukkan sharuddan shiga gasar
“Duk takardun da masu shiga gasar suka bayar an tantance su. Chidinma ‘yar kasar Afirka ta Kudu ce kuma ta cika dukkan sharuddan shiga Gasar Miss South Africa.
Mahaifiyarta ‘yar Afirka ta Kudu ce (Zulu), mahaifinta ɗan Nijeriya ne, ” kamar yadda masu shirya gasar suka fada wa IOL, wani dandalin labarai na dijital na Afirka ta Kudu.
A cewar kungiyar shirya gasar, don samun cancantar shiga gasar, dole ne 'yar takara ta kasance 'yar ƙasar Afirka ta Kudu kuma ta mallaki ingantaccen fasfo ko shaidar zama 'yar ƙasa.
Idan mai takara tana riƙe da shaidar zama 'yar ƙasa biyu, dole ne a samar da takardun da suka shafi duka biyun.
Bugu da ƙari, a cikin dokar zama 'yar ƙasa ta Afirka ta Kudu da aka gyara, ana iya samun 'yar ƙasa ta dalilin haihuwa ko zuriya, ko ba da izinin zama.