Kidan Rhumba na Congo: Salon wakar da ke samun karbuwa a fadin duniya

Kidan Rhumba na Congo: Salon wakar da ke samun karbuwa a fadin duniya

Waƙa ce da ta zarce shingen al'adu da yanki, wadda ke ratsa zuƙatan miliyoyin mutane a duniya.
Kiɗan Rhumba na Congo, wanda ake kira rumba a ƙasar, wata alama ce ta al'adun Afirka da ke burge duka 'yan gida da baƙi na waje. / Photo: Getty Images

Daga Kudra Maliro

Akwai wani kiɗa mai ƙayatarwa da ke tashi a titunan birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wanda yake tsuma mutane musamman ma a karshen mako da kuma lokacin ayyukan matasa.

Kiɗan Rhumba na Congo, wanda ake kira rumba a ƙasar, wata alama ce ta al'adun Afirka da ke burge duka 'yan gida da baƙi na waje.

Tun daga asalinsa da ke da tushe a tarihin ƙasar zuwa yadda ya samu ci gaba a tsawon lokaci, rhumba ya kasance ginshiƙi na kiɗan Afirka.

Salomon Ngima mai shekara 39, mawaƙi ne daga garin Beni da ke gabashin kasar, ya ce yana son kiɗan rhumba tun yana ƙarami, kuma ya yi ikirarin cewa masu fasaha irin su Werrason da J.B M'piana ne suka zaburar da shi a shekara ta 2000.

Salomon Ngima ya shaida wa TRT Afrika cewa "Kiɗanmu na Congo wata hanya ce ta zamantakewa tsakanin al'ummar Congo saboda yana saka mu alfahari."

Asali

Don fahimtar ainihin asalin humba, dole ne ku koma shekarun 1930 lokacin da mawakan gida suka fara haɗa waƙoƙin gargajiya na Afirka tare da sautin kayan kida na Ƙasashen Yamma kamar jita.

Wannan gauraya ta musamman ta haifar da sabon nau'in kiɗa: rhumba na Congo, wanda da sauri ya zama tamkar ruhin Congo a fagen kiɗa.

Majagaba na wannan kiɗa sun haɗa da fitattun sunaye irin su Wendo Kolosoy da Franco Luambo.

Majagaba na wannan kiɗa sun haɗa da fitattun sunaye irin su Wendo Kolosoy da Franco Luambo. Wakokinsu sun ratsa zukatan al’umma baki daya, suna sanya farin ciki da bege ga kasar da ke fama da yaki da rashin zaman lafiya.

Rhumba ya zama wani abu na gama-gari a tsakanin al'ummar Congo daban-daban, wanda ya haifar da fahimta da hadin kai a tsakanin mabambantan ƙabilu.

"Zan iya cewa rhumba shi ne asalin ƙasarmu, saboda a duk lokacin da na gabatar da kaina a matsayin ɗan Cango, mutane suna gane ni kai tsaye, godiya ga rhumba. Na kasance mawaƙi kusan shekaru 10 yanzu kuma ina samun rayuwata ta yin waƙar Kongo," in ji Mr. Ngima.

A cikin shekaru da yawa, rhumba na Congo ya samo asali don haɗa tasirin Afro-Cuban, godiya ta musamman ga zuwan mawakan Cuba a Kinshasa.

Abu mai haɗa kan mutane

Ƙarin waƙoƙin Latin sun kawo sabon salo ga wannan kiɗa, wanda ya ya aka san shi fiye da nahiyar Afirka.

Manazarta sun ce wannan waƙa na taimakawa wajen hada kan ƙabilu fiye da 450 a kasar. 

Masu fasaha irin su Papa Wemba da Koffi Olomide sun sabunta rhumba na Congo ta hanyar haɗa shi da sauran nau'ikan kiɗa na ƙasashen waje irin su soukous da zouk.

Manazarta sun ce wannan waƙa na taimakawa wajen hada kan ƙabilu fiye da 450 a kasar.

Aboubakar Kalunga Jingo, wani dan jarida kuma mai sharhi kan wakokin kasar Congo a gidan rediyon Radiotélévision Muungano Beni, wata tasha a garin Beni, ya ce rhumba shi ne salon kiɗan da aka fi sauraro a Kongo, kuma ya zarce tsara.

Kalunga ya shaida wa TRT Afrika cewa "Rhumba kida ne da ba ya taba tsufa, domin tun a shekarun 1930 ya kasance kamar yadda yake duk da tarin bayanan kida da aka yi."

’Yan jaridan fanni kiɗe-kaɗe kamar Kalunga suna buga waƙoƙi ɗari ko fiye don nishadantar da masoya rhumba.

Sakonnin zamantakewa da siyasa

Rhumba na Congo ya zarce kiɗa kawai. Yana sauye-sauyen da ake samu a a cikin al'umma. Wakokin wadannan kaɗe-kaɗe galibi suna dauke da sakonnin zamantakewa da na siyasa, wadanda ke magance batutuwan da suka hada da soyayya da talauci da cin hanci da rashawa da neman adalci.

Rumba na Congo wata hanya ce da masu fasahar Congo za su ba da murya ga jama'a, don bayyana matsalolin al'ummarsu da samun mafita.

A yau, rumba na Congo yana ci gaba da haɓaka, tare da goyon bayan sababbin masu fasaha.

Ana yawan saka kiɗan a wajen shagulgula da taruka.

Rumba na Congo ya yi zarra a jiya da yau. Ya ƙunshi haɗin kai da girman kai na al'umma, yana ba da murya ga waɗanda sukan yi shiru.

Waka ce da ta zarce shingen al'adu da yanki, wadda ke ratsa zukatan miliyoyin mutane a duniya.

Rumba na Congo ya wuce waƙa kawai, salon kiɗa ne na gado da ke ci gaba da haskawa yau da gobe.

Ko a kan titunan Kinshasa ko kuma a kan matakai na kasa da kasa, wannan salon kade-kade wani abu ne mai tasiri da ke gaba da bai wa mutane da yawa mamaki.

TRT Afrika