Kalmomi 10 na wasu yarukan Afirka da suka zagaye duniya

Kalmomi 10 na wasu yarukan Afirka da suka zagaye duniya

Akwai dubban yaruka da harsuna a nahiyar Afirka, kuma wasu daga cikinsu sun yi fice a duniya.

Duk da cewa wasu daga cikin harsunan kan aro kalmominsu daga wasu manyan yarukan na duniya, kamar Turanci da Larabci da Faransanci, to a yanzu haka da duniya ke ƙara fadada, ita ma Afirka akwai wasu kalmomi na wasu yarukanta da suka shahara a wasu sassan duniyar.

A wannan makalar, za mu yi duba ne kan irin wasu kalmomi biyar da suka kusan mamaye duniya amma asalinsu daga Afirka ne.

Ko kun san cewa asalin kalmomin ‘cola’ da ‘tango’ da ake yawan amfani da su sun samo asali ne daga Afirka?

COLA

Kalmar ‘cola’ dai za a iya cewa ta zama gama-gari a duniyar nan. Misali na kurkusa shi ne lemon coca-cola da babu lungu da sakon da ba a san shi ba.

Daga nahiyar Amurka ta arewa zuwa Latin Amurka, a nausa Turai har a bulla Asiya a kuma gangaro Gabas ta Tsakiya, kalmar cola ta yi tashen da da wuya ka ambae ta ba tare da an samu wanda zai je bai taba jin ta ba.

Kalmar ta samo asali ne daga wani sunan Yammacin Afirka da aka malkwasa shi a yaren Latin, da yake nufin wasu kananan kwarran bishiyoyi da aka gabatar da su a sabbin batutuwan duniya.

VUVUZELA

Wannan kalma ta “vuvuzela an fara amfani da ita a karon farko a Afirka kuma ta samo asali ne daga yarukan Nguni.

To me take nufi? Wani dogon kaho ne da magoya bayan ‘yan kwallo suke busawa a yayin da ake wasan tamaula a Afirka ta Kudu.

Yawanci idan dai ƙungiyoyin Afirka ta Kudu na wasa ko da a gasannin duniya ne to har a kammala magoya baya kan yi ta busa kahon na Vuvuzela.

A dalilin hakan ne ma ya shahara a duniya har kalmar ta zama gama-gari.

SAFARI

Safari wata kalma ce da ta samo asali daga yaren Swahili a yankin Gabashin Afirka.

Ana yawan amfani da ita ne don bayyana yadda ake kallon farautar dabbobin daji.

A yau kalmar Safari ta karade duniya har wasu ke zaton daga Turanci ta samo asali.

Duk inda gandun daji yake to za a ji kalmar Safari na tasiri a wajen.

An san Turawa da matukar kaunar zuwa yawon bude ido Afirka inda a nan ne aka fi samun dabbobin daji.

JUKEBOX

Asali kalmar “jook” ta samu ne daga Gullah --- yaren Creole da ake amfani da shi a wasu sassan Jojiya, Florida da Carolina ta Kudu --- kuma ana nufin “mugu” ko “wanda ba shi da kirki”.

Amma wasu sun gano asalinta daga kalmar yaren Wolof da Bambara ta “dzug” ce da ke nufin “mara dadi”.

KWASHIORKOR

Kwashiorkor na daga cikin kalmomin wasu yarukan Afirka da suka shahara a duniya.

Asalinta daga Ghana ne kuma tana daga cikin fitattun kalmomin harsunan Afirka da aka fi amfani su.

Tana nufin tsananin tamowa a jikin yara a yankunan da suke fama da tsananin talauci.

Kamus da dama na Turanci sun sanya wannan kalma ta yadda har ta zamo zagaya duniya.

TANGO

“Tango”, wata salon rawa ce da ake alakanta ta da yankin Latin Amurka, kuma wai ta samo asali ne daga kabilar Ibibio, yaren Benue-Congo da ake magana da shi a kudu maso kudancin Najeriya.

An ce an samo kalmar daga kalmar Ibibio ta “tamgu” da ke nufin “a yi rawa”.

JUJU

Wannan kalma ce mai alakanta batun dodo ko tsafi ko ma aljanu a wasu lokutan.

Daga Afirka ta samo asali kuma yaren Yarbanci a Najeriya, amma a yau ta karade ko ina a duniya.

Ko a kamus-kamus ma wannan kalmar na nan ana amfani da ita.

VOODOO

Kalmar ta samo asali daga yarukan Gbe, yaren Niger-Congo da ake magana da shi a wasu yankunan Gana, Togo da Benin.

A wadannan yaruka ana furta kalmar da “vudun”.

HAKUNA MATATA

Ita ma wannan kalma fitacciya ce a duniya. A wasu lokutan ma wasu kan dauka kalmar Faransanci ce, amma asalinta ta yaren Swahili ne a gabashin Afirka.

Kalmar ta fara yaduwa ne tun bayan amfani da ita a fim din “The Lion King” na kamfanin Disney.

Hakuna Matata na nufin „babu damuwa”.

Kamfanin Disney ya ce ya tsinto kalmar ne a yayin wata ziyarar yawon bde ido da suka je a gandun daji a Kenya.

MUMBO JUMBO

Kalmar Mumbo Jumbo ma na daga cikin fitattun kalmomin Afirka da ake amfani da su a fadin duniya.

Asalin Kalmar daga yaren Mandinka aka samo ta. Ana samun masu magana da wannan harshe a kasashen Mali da gabashin Guinea da Gambiya a yankin Afirka ta yamma.

A wani kaulin na ce kalmar na nufin wani mutum mai rawa da ke rufe fuskarsa a yayin wasu bukukuwan addini.

Wata fassarar kuma da aka bai wa Kalmar it ace wani surkulle da aka yi da nufin kawo rudani.

TRT Afrika