Kasashen Indonesiya da Malesiya su ne kasashen da za su fi karancin sa'o'i na azumi cikin kasashen

A cikin watan Ramadan Musulmai suna azumi inda suke hakura da ci da sha da jima'i tun daga fitowar alfijir har zuwa fadin rana.

A wasu kasashe za su yi azumin bana cikin yanayi na sanyi ne yayin da a wasu kasashen kuma za su yi azumin cikin zafi bisa ga bangaren da suke a duniya da kuma irin yadda yanayi yake a wurinsu.

Kazalika, sa’o’in da mutane za su shafe suna azumi ya bambanta dangane da irin yadda yanayin kasashen da suke yake da kuma bangaren da suke a duniya a wannan lokacin.

Sa’o’i goma sha biyar da minti ashirin da hudu (15:24) za a yi ana azumi a kasar Iceland, sai dai kuma sa’o’i goma sha biyar da minti ashirin da daya (15:21) za a yi ana azumin watan Ramadan a kasar Greenland.

A kasar Rasha za a yi sa’o’i goma sha hudu da minti talatin da bakwai (14:37) ana azumi.

undefined (AA)

Azumi a Burtaniya da Kanada zai kai sa’o’i goma sha hudu dai-dai (14:00).

A kasar Turkiye kuma sa’o’i goma sha uku da minti hamsin da uku (13:53) za a yi ana azumi.

Sai kuma kasar China inda za a shafe sa’o’i goma sha uku da minti hamsin da biyu (13:52) ana zumi.

A kasar Pakistan za a yi azumi na sa’o’i goma sha uku da minti arba’in da uku (13:43) ne.

A kasar Indiya mai makwabtaka da Pakistan za a yi azumi na sa’o’i goma sha uku da minti talatain da bakwai (13:37).

Za a yi azumin sa’o’i goma sha uku da minti talatin da biyar (13:35)a kasar Austireliya.

undefined (Others)

Azumi a kasar Ajentina da kasar Afirka ta Kudu zai kai sa’o’i goma sha uku da minti talatin da hudu (13:34).

A kasar Saudiyya kuwa sa’o’i goma sha uku da minti talatin da uku (13:33) za a yi ana azumi .

Za a yi sa’o’i goma sha uku da minti ashirin da bakwai (13:27) ana azumi a kasar Amurka.

Azumi a Nijeriya zai kai sa’o’i goma sha uku da miniti ashirin da hudu (13:24), yayin da za a shafe sa’o’i goma sha uku da minti ashirin da uku (13:23) ana azumi a kasar Malasiya.

A kasar Indonesiya wadda ta fi yawan Musulmai a duniya za a yi azumi na tsawon sa’o’i goma sha uku da minti ashirin da biyu (13:22) ne.

An dauki wannan iya lokacin azumin ne ranar 23 ga watan Maris. Tsawon lokacin azumin zai sauya zuwa karshen Ramadan