Daga Edward Qorro
Kauyen Nadosoito da ke mazabar Muriet na yankin Arusha wani kauye ne da ke karkashin lemar Dutsen Meru a kasar Tanzaniya da ke nuna wani irin yanayi mai ni’ima da yanayi na zaman lafiya.
A kauyen, kullum Lightness Mollel tana cikin kai-komo ne wajen kula da jakunanta, wanda take yi cikin jin dadi.
Da zarar yamma ta fara yi, Lightness mai ’ya’ya uku sai ta nemo bokiti ta debo ruwa domin shayar da jakunan, bayan dadewa da suka yi suna aiki a rana. Sai ta dan bugi bayansu cikin nishadi, kamar dai irin na nuna kauna.
Jakunan su ne abokan rayuwar Lightness, inda sukan daukar mata buhun gawayi daga kauyen Mirongoine zuwa titunan Arusha, inda take sayarwa ga kwastomominta.
Jigilar gawayin wanda jakunan suke yi mai tsawon kilomita 16 kullum yakan jawo musu raunuka, wadanda ke barinsu da tabo a bayansu da bindinsu.
Idan ta kalle yanayin tabon da ke jikinsu, Lightness takan ji wani iri, amma babu yadda za ta yi.
Haka ma wasu matan yankin Maasai na kasar Tanzania suke, wadanda rayuwarsu ke ta’allaka da amfani da jakuna domin jigila.
“Haka muke rayuwa-Kullum cikin fafutikar nema muke domin ciyar da iyalanmu,” inji Lightness a tattaunawarta da TRT Afrika.
Amma ba kamar Lightness ba, ba duk matan yankin ba ne suke ba dabbobin kular da suke bukata.
A yankin Arusha, ba abin mamaki ba ne ka ga jaki mai rauni yana tafiya da kyar jibge da kaya a bayansa. Alamar raunuka a bayyane suna nuna yadda ake cutar da dabbobin masu hakuri da juriya.
“Jaki na da muhimmanci matuka a rayuwarmu. Sai dai abin takaicin shi ne yadda mutane da dama suka kasa gane muhimmancin kula da lafiyarsu,” inji Livingstone Masija, Babban Daraktan Kungiyar Kula da Dabbobi na Aruwa wato Arusha Society for the Protection of Animals (ASPA).
Safarar fatun dabbar ta bayan fage
Duk da yanayin amfanin da jakuna suke da shi a yankin, ana yanka su domin safarar fatunsu.
Kungiyar mai kula da dabbobi, wadda take mayar da hankali a kan jakuna ta ruwaito cewa akalla jakuna miliyan 5.9 ne ake yankawa duk shekara domin hada maganin ejiao, wanda wani magani ne da kamfanonin China ke hadawa da sinadarin collagen da ake tatsowa daga fatar dabbar. Wadannan alkaluman, wanda kungiyar ta ce hasashe ne kawai, zai iya kai wa miliyan 6.7 a shekarar 2027.
Kamfanin maganin na ejiao yana samun habaka sosai a goman shekarun da suka gabata. Ana kwaba sinadarin collagen din ne da wasu saiwoyin ganyayyaki da wasu sinadaran domin hada maganin wanda yake zuwa a kwaya da na ruwa ko kuma a hada wasu kayayyakin kwalliya.
A tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016, maganin ejiao da ake hadawa a shekara ya karu daga tan 3,200 zuwa tan 5,600, wanda ke nuni da karuwar kashi 20. Alkaluman kamfanoni sun nuna cewa sana’anta ejiao ya karu da kashi 160 daga shekarar 2016 zuwa 2021.
Wannan sabon kididdigar ya bayyana a rahoton yanayin kasuwancin jakuna a duniya, wanda ya ba da shawara a kan yadda gwamnatoci da kamfanoni za su tsara yadda za su kawo karshen kasuwancin dabbobin.
Lura da yanayin raguwar jakuna a China, wakilan safarar fatun dabbobin suna zuwa kasashen Afirka da wasu sassan duniya da suke ta’allaka da dabbobin domin rayuwa.
“Kasashen Afirka ne suka fi fuskantar wannan barazana bayan Amurka ta Kudu,” inji Masija.
"African countries bear the brunt of this threat, besides South America," Masija explains.
Yanayin yadda kashe jakunan ka karuwa ne Kungiyar Tarayyar Afirka ta hana safarar fatun jakuna a watan Fabrailun bana, wanda ya kawo karshen dubban shekaru ana yanka dabbobin a nahiyar Afirka.
Hanin ya zo ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen kungiyar suka hadu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha domin taron kungiyar karo na 37.
“Mun amince da matakin na Kungiyar Tarayyar Afirka. Yanzu ya rage gare mu ne mu wayar da kan mutanenmu a kan muhimmancin kula da wadannan dabbobin,” inji Masija.
Sirdin daukar kaya
ASPA ta kirkiro wasu tsare-tsare domin ba jakunan kariya daga cutarwa.
Kungiyar tana horar da masu jakuna irin su Lightness hanyoyin hada sirdunan zuba kayayyaki da za su ba jakunan kariya daga samun rauni a yayin daukar kayayyaki masu nauyi.
Daura kayayyaki a bayan jaki ba tare da gammo ko sirdin ba yana jawo raunuka ga dabbobin wadanda suke barazana ga rayuwarsu.
“An horar da mu yadda za mu hada wadannan sirdunan zuba kayan, kuma ina farin cikin yadda suke taimaka mana wajen ba jakunanmu kariya daga raunuka,” inji Lightness, wadda ke kokarin wayar da kan mutane kan kula da jakunan a kauyensu.
Bayan hada sirdunan zuba kayan da take yi na jakunanta, Lightness ta fara hadawa tare da kasuwancin sirdunan wanda take sayarwa a kan shillings 10,000 ko kuma Dalar Amurka 4.
“Abin farin ciki ne yadda mutane suke karbar wannan tsarin. Yanzu ba mu cika damuwa da yanayin da jakunan za su shiga saboda daukar kayayyaki masu nauyi saboda wannan tsarin na amfani da sirdi,” inji ta a tattaunawarta da TR Afirka.