Akon ya yi alkawarin fara aikin gine-gine a filin ba tare da bata lokaci ba./ Hoto: Reuters

Daga Brian Okoth

Sengal ta bai wa mawaki Akon wa'adin fara gini a kan wani fili mai girman eka 136 da aka ba shi a shekarar 2020, ko kuma a mayar da kaso 90 cikin 100 na filin zuwa ga gwamnati.

Shekaru hudu da suka wuce ne gwamnatin ƙasar Senegal ta bai wa Akon filin don ya bunƙasa shi zuwa birni wanda ke da abubuwan more rayuwa da suka haɗa da asibitoci da wurin shakatawa da jami'a da kantin sayar da kayayyaki da ofishin 'yan sanda da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana da kuma gidajen haya.

Filin dai na daf da yankin Mbodiene da ke gabar teku, mai tazarar kilomita 120 a yankin kudu maso gabas da babban birnin ƙasar Senegal, Dakar.

Akon ya yi alƙawarin fara aikin gine-gine a filin ba tare da ɓata lokaci ba, tare da nufin samar da ayyukan yi da kuma muraɗin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Senegal a ransa.

Aikin biliyoyin daloli

Mawakin ɗan ƙasar Senegal da Amurka ya ce a shekarar 2023 za a kammala kashin farko na aikin wanda zai lakume dalar Amurka biliyan 6.

An dage ranar kammala aikin zuwa shekarar 2025, inda Akon ya ambaci cutar ta COVID-19 a matsayin dalilin jinkirta ginin.

Za a gina sauran garin a hankali, inda aka sanya shekarar 2030 a matsayin lokacin kammala aikin gaba ɗaya.

Har yanzu birnin na Akon city ba a gina shi ba. /Hoto: tayin hoton Akon City 

Akon ya ce bayan kammala aikin, birnin zai zama "wurin zuwa ga 'yan Afirka da Amurka masu neman sake cudanya da tushensu na Afirka."

Tsaiko a tsare-tsare

Har yanzu dai wurin ya kasance ba a gine ba, inda dabbobi suke yawan kiwo a filin ƙasar.

Katanga guda ɗaya ce kawai aka dasa don nuna ginshiƙin ginin aikin a wurin.

Yanayin da ake ciki ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa na intanet, kama daga masu goyon bayan yunkurin gwamnati na karɓe fili da kuma masu adawa da hakan.

"Akon ba shi da adadin kuɗin da zai iya aiwatar da irin wannan gagarumin aikin. Ka da ku bari wani ya yaudare ku. Ya kamata gwamnati ta ƙarɓe filin ta bunkasa," kamar yadda Ynsson ya rubuta a shafin TikTok, wani mai sharhi kan shafukan sada zumunta.

Wani, Nelly Viano, ya ce duk da haka, ina ba da shawarar kar a gaggauta yin aikin.

''A kara masa lokaci. Shekarun Afirka nawa ne da kuke tsammanin mutum ɗaya zai yi abin al'ajabi? Za a ɗauki lokaci kafin a iya cim ma waɗannan abubuwa."

Shi kuwa Victor_official ya yarda da cewa, Akon na buƙatar a tallafa masa ba wai a soke shi ba.

''Waɗannan wasu dalilai ne da ya sa har yanzu Afirka take baya; ba mu yarda da kanmu ba balle mu tallafa wa kanmu. Hatta Burj Khalifa, gwamnatin Dubai ce tare da masu saka hannun jari na duniya ne suka gina ta. A ba Akon dama da lokaci.''

Gaza biyan ƙuɗaɗe

Gwamnatin Senegal ta hannun kamfanin raya yankunan bakin ruwa na SAPCO, ta yi barazanar kwace filin, tana mai cewa Akon ya gaza biyan kuɗaɗen da ya rike filin.

Sai dai mawakin ba shi da takardar mallakar filin.

Tawagar Akon ta yi ikirarin cewa ana ci gaba da koƙarin aikin shara da kuma zayyana filin don aikin gine-gine a ciki.

A shekarar 2020 gwamnatin Senegal ta bai wa Akon eka 136 don gina birnin AKON CITY./ Hoto: Akon Instagram

A karshen shekarar 2023, Akon ya fada a wata hira da BBC cewa aikin da yake yi a Senegal yana tafiya kashi "100 bisa 100" kuma masu sukar sa za su ji kunya.

Sai dai, mutane da dama a yankin kauyen Mbodiene sun cire rai da wannan aiki.

Akon mai shekaru 51 ya ba wai masu saka hannun jari damar haɗa kuɗaɗen da za a gina birnin, sai dai a cewar tawagar Akon, ''ba a maraba da alƙawarin zuba jari.''

An ayyana Julius Mwale na Kenya a matsayin wanda ya jagoranci aikin zuba jari a aikin.

Mutanen yankin Mbodiene sun cire rai a kan aikin / Hoto: Reuters

Ba a dai san takamaiman darajar arziƙin Akon ba, amma rahotanni da dama sun nuna cewa zai iya kai tsakanin dala miliyan 40 zuwa 80.

Uganda ''Akon city''

A daidai lokacin da makomar birnin Akon na ƙasar Senegal ke kwan gaba-kwan baya, haka zalika ana fama da rashin tabbas a Uganda, inda gwamnatin ƙasar ta bai wa Akon wani fili mai girman eka 640 don gina birnin a kan dala biliyan 6.

An gabatar da tayin ga Akon bayan wata ganawa da ya yi da shugaban Yoweri Museveni a Uganda a watan Afrilun 2021.

Mazauna garin Mukono da ke tsakiyar ƙasar Uganda, inda ake shirin gudanar da aikin, sun yi fatali da matakin da gwamnati ta ɗauka na bai wa Akon filin, suna masu cewa kakanninsu ne suka mallaƙi wurin.

Kamar dai a Senegal, har yanzu ba a fara aikin gina birnin Akon na Uganda ba.

Asalin iyayen Akon 'yan Senegal ne, waɗanda daga baya suka koma New Jersey a Amurka daga baya.

TRT Afrika