A ɓangaren ƙwarewa, Yolanda Hickson Asumu wadda ake yi wa laƙabi da "mai mafarauta" - wata wadda ke taimaka wa ƙungiyoyi ko wuraren aiki nemo matasa waɗanda ke da basira domin ba su damar aiki.
Wannn wani aiki ne da ke da alaƙa da zaƙulo masu basira da horar da su da kuma miƙa su ga kamfanoni da masu ɗaukar aiki. Haka kuma aikin nata ya shafi taimaka wa mutane masu baiwa samun kuɗi ta hanyar amfani da baiwar da suke da ita.
Yolanda ta kafa shafinta na intanet mai suna Icubefarm.com a shekarar 2015 wanda masu baiwa da basira daban-daban za su iya shiga kyauta.
"Muna ta aiki domin tabbatar da tsaron wannan shafin, wanda zai zama tsani mai ƙarfi a tsakanin masu neman aiki da kamfanonin da ke ɗaukar aiki a nahiyar," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
'Uwa ga masu neman aiki'
A tsawon lokaci, ta samu wannan laƙabin na "uwa ga masu neman aiki" kamar yadda waɗanda suka yi tarayya da ita sannan suka amfana da shafinta suke kiranta.
"Bayan na kammala jami'a, na soma neman aiki ban samu ba, sai dai wata rana wata ƙawata ta turo mani shafin icubefarm. Ta haka ne na yi rajista da su inda nake zuwa shafin a kullum domin ganin ko akwai wani aiki da ke da alaƙa da abin da na karanta.
"Sai wata safiya na ga ana tallata wani aiki a shafin. Bayan na nemi aikin sai aka kira ni domin interview, wanda na yi nasara ga ni kuma a nan ina aiki a matsayin mai horaswa a wani kamfani tsawon watanni a yanzu," in ji Sandra Sibacha Bosepa, wadda ke da baiwa a ɓangaren tallace-tallace ta intanet da kuma zane-zane.
Da alama Icubefarm na gogayya da wasu manyan shafukan ɗaukar aiki waɗanda yawancinsu na ƙasashen yamma ne.
"Da gaske ne gogayya na da wahala, amma iliminmu na tattalin arziki na gida da 'yan kasuwa, da kuma kusancinmu da masu son aikin wani babban kadari ne a gare mu," kamar yadda Yolanda ya bayyana.
Ta bayyana cewa shafin nata na intanet na ƙara faɗaɗa ayyukansa waɗanda ya shafi duka ayyukan da ake buƙata na ayyukan bil adama, kamar yadda ta ƙara da cewa.
"Da Icubefarm.com, ana ɗaukar masu neman aiki dangane da wata ƙwarewa wadda suke da ita bayan an tabbatar, kamar iliminsu ko kuma ƙwarewarsu," kamar yadda ta bayyana.
Yadda yake aiki
A yadda yake, masu neman aiki za su yi rajista tare da saka bayanansu a kyauta, inda za su saka duka wasu abubuwa da suka shafe su na aiki.
"Sai su duba jerin ayyukan da ke da akwai a kamfanoni sai su nema," kamar yadda ta ƙara da cewa.
A ɓangarensu, manajojin kula da sha'anin jama'a waɗanda ke ɗaukar aiki suna yanke shawara dangane da irin bayanan da ke da akwai na masu neman aikin.
Sai dai kamar yadda Yolanda ta bayyana; "tantance bayanan ya ta'allaƙa ne ga kamfanin, kuma suna da damar ɗaukar mutumin da ya cancanta aiki."
Yolanda ta bayyana cewa abin da ya ja ra'ayinta ta kafa wannan shafin ya biyo bayan irin ƙorafin da take ji ana yi kan "rashin adalci" wurin ɗaukar aiki.
Sai ba da jimawa ba, kamar yadda wasu ƙasashen Afirka suke yi, masu neman aiki a Equatorial Guinea suna bi ta hanyar kamfanonin da ke shiga tsakani wurin ɗaukar aiki domin taimakonsu samun gurbi.
Wannan dangantakar kai tsaye a buɗe take ga cin zarafi da samar da ƙiyayya.
"Ta hanyar bin hanyoyin da ba a bayar da shawarar binsu, kamfanoni a wani lokacin suna ɗaukar mutanen da ba su cancanta ba. Sanayya tana zama abin da ake dubawa ba cancanta ba," kamar yadda Yolanda ya bayyana.
Idan da buƙata, Icubefarm.com na taimaka wa masu amfani da internet wurin baje kolin bayanansu domin tallata kansu
"Ta hanyar kundin adireshi wanda sashen ayyuka ya tsara, shafin kuma a fakaice yana ba kamfanoni damar tallata kansu ga abokan ciniki, masu kaya, da masu siyarwa," kamar yadda ta ƙara da cewa.
A halin yanzu, samun bayanai a icubefarm.com kyauta ne ga masu neman aiki da 'yan kasuwa. "Sai dai a abin da nake fata a nan gaba a daidai lokacin da jama'a suka ƙaru, za a ware wani sashe na tallatace-tallace da kuma ayyuka", kamar yadda ta ce.
Haskakawa gaba da Equatorial Guinea
Tun da farko, an kafa Icubefarm ga masu amfani da intanet a Equatorial Guinea. Sai dai shafin wanda aka ƙirƙira a Malabo a halin yanzu ya samu gindin zama, godiya ga irin haɗakar da aka yi da wasu manyan kamfanoni na ƙasar.
Sai dai sakamakon adadin jama'ar ƙasar da ba su wuce miliyan ɗaya ba, Equatorial Guinea ba babbar kasuwa ba ce ga wannan. Adadin rashin aikin yi a ƙasar na da yawa, duk da cewa ma'aikatar ƙwadago ta ƙasar ta ce adadin bai wuce kaso 10 cikin 100 ba.
Tun bayan da muka fara, Icube, ya yi wa sama da masu neman aiki 17,000 rajista da kuma taimakawa wurin samar da ayyuka 4,500. Mun taimaka wa sama da kamfanoni 1,600 wurin samar musu masu neman aiki," kamar yadda Yolanda ta shaida wa TRT Afrika.
Baya ga ƙasarta ta gado, Yolanda na ƙara jawo hankalin masu ɗaukar aiki daga wasu ƙasashe da zummar biyan buƙatun na ɗumbin matasan Afirka da ke neman aiki.
Tun daga shekarar 2017, ta bude ofishi a kasar Kamaru, inda shafinta ke da tsari mai bayar da ƙarfin gwiwa. A Masar, Habasha da Najeriya, alal misali, Yolanda na yin kamfen don faɗaɗa kamfaninta.
Baya ga mu'amala ta intanet, Yolanda ta fito da tsarin shirya wasannin motsa jiki da ke hada ɗumbin matasan Afirka da shugabannin kamfanonin Afirka, tsarin da kuma ake ganin yana haifar da ɗa mai ido.