Gerard Motondi ƙwararren mai sassaƙa wanda ya ƙera masu zane na tarihi a duniya/ Hoto: Motondi  

Daga Pauline Odhiambo

Kenya, wadda ke da dadaɗɗiyar tarihin samar da zakaru a wasannin Olympic a fegen guje-guje da tsalle-tsalle, ta samu wani gwarzo a wasannin 2008 da aka yi a birnin Beijing.

Gerard Motondi, ƙwararre a fannin sassaƙa kuma malami da ya taba lashe ƙyautar wasannin Torch Olympic a gasar zane-zane da kwamitin wasannin Olympic na duniya ya shirya a gefen wasannin.

Aikin sassaƙar Motondi mai tsawon mita biyu "Inseparable", ya nuna wani nau'in kifi da aka lulluɓe jikinsa, ya wakilci zaman lafiya a matsayin jigon wasannin, wanda ya kaɗa alhalan cikin mamaki.

Shekaru goma shida bayan ya ɗoke masu izane-zane 10,000 a gasar, wasannin Olymppics ta Paris na 2024 ya saka tuni da sunan Motondi a shafikan sada zumunta a ƙasarsa ta Kenya.

Kan wane Dalili? Wasu aikin sassaƙa guda uku da wasu masu zane-zane suka saɗaukar don karrama zakarun 'yan wasan ƙasar.

Ƙwararren mai fasahar sassaƙa

A yayin da 'yan ƙasar suka fusata bisa zargin wani zane mai kama da dodo a da ya mamaye kafofin intanet a matsayin sassaƙa, da dama daga cikin mutane sun yi tagging din Mtondi mai shekaru 59, suna mamakin dalilan da suka sa ba a zaɓi ƙwararren mai sassaƙa a aikin ba.

''Abin da ake ta yada wa shi ne: Ta yaya za a yarda irin wannan abu ya faru?'' kamar yadda Motondi ya shaida wa TRT Afirka. '' Amma ni a lokacin, babu wani daga gwamnati ko ma'aikatar wasanni da ya ƙira ni don na ƙera mutum-mutumi don girmama 'yan wasanmu."

An kaddamar da wasu aikin sassaƙa uku masu cike da cece-kuce a taron bikin martaba birnin Eldoret, inda mafi yawan manyan 'yan wasan Kenya suka fito.

Mutane sun yi ta ƙira kan a cire sassaƙan, 'yan Kenya da dama sun yi ta kwatance da mutum-mutumi a Amurka da sauran ƙasashe don girmama 'yan wasan Kenya da aikin da aka yi na rashi ƙwarewa a Eldoret.

Bayan an sauƙe mutum-mutumin da aka sassaƙa, an yi wani sabon ƙira kan a ba Motondi alhaƙin aikin sassaƙar da zai maye gurɓin mutum-mutumin da ya dace don ƙarrama 'yan wasan asar.

Tuni dai jami'an gwamnati suka nemi fitaccen mai sassaƙar don ƙirkiro zane-zane da za su yi adalci wajen martaba ‘yan wasan kasar da ba zai taba tsufa ba ta hanyar amfani da dutse.

Motondi na iya ƙirƙira sassaƙa daga ƙarfe da sauran wasu abaɓe amma ya fi son yin aiki da dutse: Hoto: Motondi

Stepping stones

An haifi Motondi ne a Tabaka a Kisii, sanannen cibiyar fararen duwatsu kuma a ƙasar da ke yankin gabashin Afirka kana ɗaya daga cikin tsofin masana'antun hannu na gargajiya.

Lokacin yana yaro, Motondi ya koyi aikin sassaƙa ta farar dutsen ta hanyar yin samfurin tsuntsaye da kifi da sauran wasu dabbobi. Har ilau dutse shi ne kayan aikin da ya fi son amfani.

"Dutse abu ne da ake samu a ƙasa; ba zai iya gurɓata muhalli ba kuma zai iya kwashe tsawon miliyoyin shekaru bai baci ba,'' in ji shi.

''Kazalika, dutse ba shi da wani daraja a gari, wanda hakan zai hana lalata shi, ba kamar yanda za a aije sassaƙar ƙarara ba a wuraren taruwar jama'a.

Sannan, yana da juriya ga sauyin yanayi kuma ba za a iya lalata shi da wuta ba."

Motondi ya lashe ƙyautar Torch Olympic a gasar fasahar zane-zane a wasannin Olympics ta Beijing a 2008. Hoto: Motondi

A tsakiyar shekarun 1980, Motondi yana daga cikin rukunin farko na malamai a ƙasar waɗanda za su taimaka wajen gabatar da darasin zane-zane ga yara a matsayin wani ɓangare na tsarin karatun ƙasa, kuma har yanzu ya kasance malami mai himma da azama.

Sauya al'adu

A al'adar Kisii na gargajiya, an hana mata sassaƙa farar dutse. Rawar da suke takawa galibi ya ta'allaka ne wajen samar wa da kuma jigilar duwatsu.

Motondi ya kuɗuri aniyar sauya wannan al'adar, tare da shawo kan shingen al'adu ta hanyar horar da mata da dama kan sassaƙa da tabbatar da suma ana damawa da su.

"Mata suna yin zane-zane masu kyau, kuma ana sayan zanensu fiye da na kasuwannin yawon buɗe ido," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. "Sassaƙa da mata ke yi ya kuma kara kuɗaden shiga ga gidaje da dama."

Wani sassaƙar zane da Motondi ya yi da aka sanya masa suna da  'sister Cities' a birnin Chengdu na lardin Sichuan China. Hoto: Motondi

A shekarar 2011, Motondi ya shirya taron al'adu mai suna "African Stones Talk", inda matan gida za su baje kolin fasaharsu da horar da wasu ƙwararru a wannan fanni.

Ya kuma horar da ma'aikatan hakar ma'adinai ta hanyar "hade fanonin ilimi da al'adu da kuma kasuwanci", ya zama mai kaffara wa a wanna a fannin.

Motondi ya yi zanen sassaƙ kusan 25 a duniya ciki har a Turkiyya da Rasha / Hoto: Motondi

Kazalika ya kasance cikin tawagar masu fasaha da aka gayyata zuwa Dubai daga sassa daban-daban na duniya don ƙirƙirar sassaka na marmara a shekarar 2008 wurin da aka kra gini mafi tsayi a duniya - Burj Khalifa - yake a yanzu.

"A duk ƙasashen da na yi aiki a ciki, zane-zane na nuna tarihi da al'adu da kuma irin nasarorin da mutanen wuraren suka samu," in ji shi.

A shekara ta 2013, ya samu tallafi daga gwamnatin Kenya don ƙirƙirar hoton Mashujaa a lambun Uhuru na Nairobi, inda aka fara daga tutar Kenya a shekarar 1963 don nuna 'yancin kai daga mulkin mallaka.

Bayan shekaru biyu, ya ƙirƙiri wani zane mai suna "Love for the Nation," wanda aka sanya a wuri ɗaya.

A yanzu haka dai Motondi yana kan aikin wani Sassaƙa a birinin Tatu na Kenya. Hoto: Motondi

"Buri na shi ne in ci gaba da samar da sassaka da abubuwan tarihi wadanda za su iya ƙawata birane a duk fadin duniya," in ji Motondi.

Burin Motondi shi ne ya ƙera ƙarin wasu sassaƙa don awata birane a faɗin duniya/ Hoto: Motondi
TRT Afrika