Giwayen sun dawo ne sakamakon fatattakar 'yan tawaye daga dajin. Hoto: Getty Images

Daga Kudra Maliro

Rikicin da ya dauki tsawon lokaci tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati da kuma mafarauta ne suka tirsasawa giwaye da dama barin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Congo zuwa filin shakatawa na Sarauniya Elizabeth da ke makociyar kasar Uganda.

'Yan tawaye sun mamaye wuraren da dabbobi ke rayuwa wanda hakan ya sanya su dole su gudu.

A yanzu akwai labari mai faranta rai wanda ke bayyana komawar giwaye sama da 1,000 zuwa dajin Congo, in ji masu bayar da kariya ga dabbobi.

Masu kare dabbobin dawa sun bayyana dawowar giwayen a matsayin labari mai dadi. Hoto: Getty Images

Wannan ya zo ne bayan da a shekarar 2021 sojoji suka kaddamar da farmakan hadin gwiwa don fatattakar 'yan tawayen ADF a lardun Arewacin Kivu da Ituri, wanda hakan ya sanya su suka bar dazukan.

"Mahukunta sun fahimci komawar giwaye a farkon wannan makon inda a yanzu haka sama da giwaye 1,000 ne ake iya gani a dajin, wadanda suke fitowa daga sassa daban-daban," in ji Merdy Baraka, jami'in yada labarai na Hukumar Kare Dabbobi da Gandun Daji ta Kongo.

Gabashin Afirka na da giwaye mafiya yawa a lokacin da adadinsu ke ragu wa a duniya. Hoto: Getty Images

Komawar tawagar giwayen zuwa Virunga, sakamako ne na kokarin da jami'an tsaron Congo suke yi." in ji Emmanuel De Merode, daraktan gandun dajin kasa na Virunga.

An jibge wasu dakarun Uganda 1,700 a dazukan Arewacin Kivu da Ituri. Tare da FARDC, suna kokarin murkushe 'yan bindiga. Dakarun sun riga sun kame iko da yankuna da dama da ke hannun 'yan tawaye a dajin Virunga.

A shekarun 1950 kusan giwaye 8,000 ne keyawo a dajin Virunga. Hoto: Getty Images

Baraka ya ce "Ina kira ga kowa da ya hada hannu da dakarun hadin gwiwa wajen kare dazukan Flora da Fauna, ta hanyar kalubalantar duk wanda ya yi farautar dabbobi a dazukan... Yana da kyau mu hada kawunanmu gaba daya don kare Flora da Fauna."

Wannan abu ya faranta zukatan masu rajin kare dabbobi a ciki da wajen Congo.

"Yana da matukar faranta rai ganin wadannan giwaye na zaune lafiya a dajin Virunga a yanzu haka," in ji Philip Muruthi, mataimakin shugaban kwamitin kula da namun daji na Asusun Dabbobin Dawa na Afirka.

Ana sa ran dawowar giwayen zai habala yawon bude ido. Hoto: Getty Images.

Mr. Muruthi ya ce "Manufarmu ita ce a kalli dukkan filayen shakatawa na Afirka na dauke da giwaye, saboda kubutar da lafiya da rayukansu ne abun da ya fi damun mu, duk da iyakokin da ke tsakanin dazukan.

Muna kuma samar da masu yaki da mafarauta don bai wa giwayen sararin yawo yadda suke so."

A shekarun 1950 kusan giwaye 8,000 ne keyawo a dajin Virunga. Amma farauta da noma ba bisa ka'ida ba da kuma yakin da ake yi tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnati tun 1990 sun jawo kaurarsu.

Mafarauta na harbin giwaye don amfani da haurensu. Hoto: Getty Images.

Jama'ar Congo sun yi maraba da wannan labarin, inda suka yi farin cikin komawar dabbobin zuwa Virunga.

Wani mazaunin Beni da ke kusa da dajin Virunga Mista John Matemuli ya ce "Muna son dawowar giwayen don jan hankalin masu yawon bude ido. Dole gwamnati ta ci gaba da murkushe 'yan tawaye da suke buya a Virunga, ta yadda dabbobin da suka gudu za su dawo."

"Babban abun da muke fata shi ne wadannan giwayen su ji kamar suna gida ne a Congo ko Uganda," in ji Mr. Muruthi.

TRT Afrika