Wannan dai shi ne karo na uku da aka taba samun rahoton haihuwar tagwayen giwaye a Kenya a cikin shekaru uku da suka gabata / Hoto: Reuters

Daga Charles Mgbolu

Wani yanayi mai ban sha'awa da ba kasafai aka saba gani ba ya faru a Kenya a sabuwar shekarar nan, inda aka ga wata giwa da tagwayen 'ya'yanta a gandun daji na ƙasa na Shimba Hills.

Hukumar kula da namun daji ta Kenya (KWS) ta yaɗa labarin a shafinta na sada zumunta, inda ta bayyana ''farin cikinta bisa ga wannan kyauta ta tagwaye daga Allah.''

''Kyauta biyu masu albarka daga Allah! An ga wata giwa tare da tagwayen 'ya'yanta a gandun namun dajin Shimba Hills na ƙasa - An shiga sabuwar shekara da wani lamari mai ban sha'awa da ba saba gani, kamar yadda KWS ta sanar a shafinta na sada zumunta.''

Wannan dai shi ne karo na uku da aka taba samun rahoton haihuwar tagwayen giwaye a Kenya a cikin shekaru uku da suka gabata, wani lamari da ba a saba gani ba.

Gidauniyar namun daji ta Afirka ta bayyana cewa, "An nuna damuwa game da rashin nau'in giwayen Afirka (Loxodonta africana) sakamakon yawan farautar haurensu da ake yi a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980, yanayin da ya sa aka ƙara ba da fifiko wajen kare nau'in halittar.

Don haka samun labarin haihuwar tagwaye giwayen yana da matukar muhimmanci, inda aka kiyasta irin wannan haihuwa da ba kasafai ake samu ba da ƙasa da kashi ɗaya cikin 100 a dukkan haihuwar da giwaye suke yi, a cewar hukumar KWS.

Ƙalubalen tagwaye

Abubuwa da dama da suka hada da na ilimin halittu da na muhalli suna taka rawa wajen ƙarancin samun cikin tagwayen giwaye.

Giwaye suna da mafi tsawon lokacin daukar ciki fiye da kowace dabba da ke shayarwa a duniya, inda suke daukar ciki na tsawon watanni 18 zuwa 22.

Ɗaukar cikin tagwaye a lokaci guda yana da matukar wahala ga Uwar. Ciyar da 'ya'ya biyu masu na bukatar albarkatu masu yawa, lamarin da ka iya zama babban kalubale, musamman a wuraren da abinci da ruwa ba su da yawa, in ji gidauniyar namun daji ta Afirka.

Kazalika, girman giwayen da aka haifa kara haifar da wahala haihuwar tagwaye wahala.

TRT Afrika