Daga Sylvia Chebet
A arewa maso gabashin Chadi, dutsen yashi na Ennedi Massif ya samo asali ne bayan ruwa da zaizayar ƙasa sun samar da shi tsawon lokaci, wanda a cikinsa akwai tuddai da kwari da ƙorama wadda ta ratsa ta ciki
Kalmar Ennedi na nufin gida mai kyau a harshen ƙasar. Makiyaya da ke magana da harshen Dazaga suna zaune a yankin. Kuma addinin Musulunci suke bi.
Ennedi na da girman murabba'in kilomita 40,000 kuma shimfidar wurin ta sahara ce.
Ennedi ya kasance wurin da yanayi ya haɗu da tarihi. Haka kuma wuri ne da ke da arziƙin al'adu.
Hukumar Kula Da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta bayyana Ennedi Massif a matsayin wani wuri na al'ada da tarihi.
Mutanen farko da suka yi zama a wurin sun yi kwaliyya da dubban zane-zane kan duwatsu da cikin koguna wanda hakan ya samar ɗaya daga cikin zane-zane na kimiyya kan duwatsu mafi girma a Sahara.