Daga Firmain Eric Mbadinga
Gidan adana kayan tarihi na Dar Gnawa Museum yana nuna fasahohi da kayan tarihi na al'ummar da ta samo asali daga yankin Afirka kudu da Sahara, waɗanda a baya bayi ne da ke rayuwa a yankin Maghreb tun shekarun ƙarni na 19.
Wani abin kiɗa mai suna Guembri, wanda ke da zare kuma yake ba da sauti daban-daban, abu ne da ke wakiltar salon biki da raye-raye na al'adun Gnawa.
Al'ummar Gnawa waɗanda ke da asali daga Afirka kudu da Sahara ana samun su aduka yankin Maghreb, daga Tunisia zuwa Algeria, da kuma Morocco.
Miliyoyin mata da maza na wannan al'umma suna alfaharin yaɗa al'adarsu, wadda ta ƙunshi cike da tasirin al'adun ƙabilun Barber, da Larabawa Musulmai.
An kafa gidan tarihin Dar Gnawa Museum a shekarar 1860 a garin Derb jdid na Marrakech, da manufar nuna wa duniya faɗin al'adun wannan jama'a.
Oussama Elasri ɗan wannan al'umma ne. Kuma mai kulawa ne kuma mataimakin daraktan wannan gidan tarihin. Yana yawan faɗa wa masoya fasaha cewa, Dar Gnawa cike yake da al'adu.

"Wannan gidan tarihin yana ba da mahanga zuwa tarihi daɗaɗɗe, da labaran alaƙar Afirka kudu da Sahara da yankin Maghreb, musamman da Morocco," cewar Oussama Elasri da yake zantawa da TRT Afrika.
Tun bayan buɗe ta ranar 1 ga janairun 2024, bayan an mata gyare-gyare, cibiyar ta saka burin adanawa da bayyana tarihin Gnawa.
Gidan tarihin yana ɗauke da kayayyaki kiɗa, kamar guembri, da tufafin al'ada da na yau-da-kullum da mutanen Gnawa ke sakawa.

''Wannan ya nuna faɗin tasirin wannan al'adar tsakanin ɓangarorin Afirka African, wanda ke ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashe,'' in ji Oussama Elasri, a hirarsu da TRT Afrika.
Baya ga nune-nune, gidan tarihin yana shirya nunin fim, da film, da kaɗe-kaɗe, da wasan kwaikwayo da bukukuwa.
Masu bincike da ɗalibai suna ziyarta cibiyar kan batutuwa kamar yadda ake ƙera guembri, da rawar bori da alaƙar al'adun Gnawa da al'adun Afirka.
Cibiyar ta Dar Gnawa ta dace da cigaban zmani a Morocco kamar yadda ƙasar da ke ƙarƙashin Sarki Mohamed VI, tana da kishin raya al'adu.
Ɗaukaka manufofin cibiyar tarihin yana da tasiri wajen nuna damarmakin cigaban tattalin arziƙi da yawon buɗe-ido da Morocco ke da shi.