Daga
Charles Mgbolu
Dawakai suna tayar da kura yayin da suke wasa a jere, bakinsu a wage yayin da mahaya sanye da farin rawani sukan hanbari dawakai a daidai lokacin da ake harba bindigar toka.
Bikin Yacoub el Mansour na birnin Rabat a kasar Maroko, biki ne mai kayatarwa wanda ke ba mahaya dawakai sanye da rawani muhimmanci.
Bikin wanda aka fara a karni na 15 ya samo asali ne daga al'adar mutanen Maroko ta hawa rakuma kuma kalmar "baroud" ta samu asali ne daga kalmar bindigar toka a harshen Larabci, wadda al'ada ce da ta shahara a Maroko lokacin bukukuwan addini da bikin 'yanci kasa da bukukuwan da ake yi a gidaje.
Ana wannan al'adar ce da wasan tseren dawaki yayin da mahaya dawakin suke sukuwa irin wadda sojoji suke yi a lokacin baya idan suna yaki da abokan gaba.
Ana shirya bikin Tbourida a kowace shekara a kowane yanki a kasar Maroko. Ana bai wa wadanda suka yi nasara kofi wanda suke dagawa sama a karshen wasan a matsayin abin martabawa.
Gasar Tbourida ta kunshi tsere da juriya da nuna kwarewa. Akwai tawaga da ke wakiltar kowane yanki wadda ake kira "Sorba" kuma ta kunshi fitattun dawaki da shahararrun mahaya.
Tawagar mahaya da dawakan da ake amfani da su lokacin bikin Tbourida ta kunshi mahaya 11 zuwa 15 karkashin jagorancin "Mqadem", wanda yake tsayawa a tsakiya kuma yake tsara tafiyar mutane da dawakan. Bikin Thourida babban bikin al'ada ne da ake yi kuma 'yan baya ma za su ci gaba da yi.
Hukumar Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta sanya bikin cikin manyan bukukuwan al'adu na duniya a shekarar 2021, inda hatta mata ma suna shiga bikin.