A 2004 aka fara bikin shekara-shekara na Calabar Carnival. Hoto: Facebook/Cross River State First Lady

Daga Ma'aikacinmu

A cikin watan na Disamba baki daya, kyawawan kaloli na tufafi sun bayyana a kan titunan birnin Calabar da ke kudancin Nijeriya, a yayin da aka fara bukin nuna al'adu na Calabar Carnival. Ana zuwa halartar wannan biki daga wurare daban-daban.

Bikin da ake yi a kan tituna da aka baiwa take 'Battle of Bands', wanda aka fara a ranar 1 ga Disamba don karasa kwanakin shekara, biki ne na ƙololuwar nishadi da yawon bude ido don murnar isa ga karshen shekara.

Bikin na kuma gabatar da wasannin kwallon kafa da tseren jiragen ruwa. Hoto/Facebook/Office of the Cross River State First Lady

Sama da mutum miliyan biyu daga kasashen waje 25 ke halartar bikin inda wasun su ke gabatar da kayan al'adunsu, kamar yadda alkaluman wadanda suka shirya taro.

Babban abin da ya fi bayar da sha'awa ga taron shi ne faretin da ake yi cikin kaloli daban-daban a kan tituna, inda makadan da suka samu nasara suke cin kyautar dala 100,000.

Yara kanana makada da waka sun yi shuhura a wajen bikin. Hoto/Facebook/Office of the Cross River State First Lady

Ana faretin na tsawon kilomita 12, makada da masu rawa 50,000 ke gabatar da gasar kida da wakar biki guda biyar, da kuma guda 10 da ba na gasa ba.

Biki ne da ya cancani a kalle shi, inda dubban daruruwan mutane suke jeruwa don kashe ƙwarƙwatar idanuwansu a yayin da makaɗa da mawaƙa da marayan ke wucewa.

Ana daukar wata guda ana gudanar da bikin. :Hoto/Facebook/Office of the Cross River State First Lady

A yayin da yake kaddamar da wannan bikin na bana, gwamnan jihar Sanata Bassey Otu, ya bayyana cewa yawon bude ido a Afirka na ci gaba da fuskantar mummunar illar Covid-19, amma a hankali yana farfadowa.

"Taken taron na bana ya zo ne bayan nazari da duba ga dukkan bukukuwan da aka yi na baya. Bayan Covid-19, an samu karaya, kuma zukatan mutane sun yi rauni," in ji Otu.

Manufar bikin ita ce a bunkasa yawon bude ido da tattalin arzikin jama'ar yankin. Hoto/Facebook/Cross River State First Lady

Ya kara da cewa "Ko mutane na so ko ba sa so, bayan lokacin shan wahala, yunwa da sauran su, akwai lokacin da zai zo da mutane za su dara, kuma wannan ne lokacin."

A shekarar 2004 aka fara gudanar da bikin inda gwamnan lokacin Donald Duke ya kaddamar da shi d amanufar bunkasa yawon bude ido da tattalin arzikin jihar da ma kasar baki daya.

TRT Afrika