Zane-zanen Victor Omondi suna nuna rayuwar yau-da-kullum a babban birnin Kenya, Nairobi.

Daga Paula Odek

Yayin da duniyar zane-zane ta zamo fagen da kowa ke nuna fasaharsa ta zen, an samu wani hazikin mai zane da ke amfani da kaloli wajen sawwara yadda rayuwa ke wakana a birnin Nairobin Kenya.

Victor Omondi, wanda ya koyi zane da kansa, ya yi suna yanzu a matsayin dan-baiwar zane-zane.

Ya fara sha'awar zane-zane tun yana dan shekara hudu, kuma yana alfahari da abokanan karatunsa, da malamansa na makaranta wadanda suka taimaka masa.

Yadda Victor ke amfani da burushin zane yana kayatarwa, kuma yana fito da basirarsa ta sawwara birnin Nairobi a kan kyalle zayyana.

Salon zane na zamani

Salon zane irin na Victor ya fita daban, kuma ana kiran salon da "mai kama da gaske". Zanen yana nuna wa masu kallo wata duniya da bambancinta da zahiri dan kadan ne. Yana zana gari da mutane tamkar ka taba su.

Victor ya ce, "Ina kashe awa 10 zuwa 60 kan zane daya, amma ba a lokaci guda ba. Ina yin hutu tsakanin aiki. Zanena yana bukatar saka lokaci mai tsayi, da yin aiki a tsanake."

Victor yana samun fikira daga birnin Nairobi kansa, birnin da yake kira gidansa. An haife shi ne a birnin kuma a nan ya girma cikin lungu da sakon garin. Yana iya jin kamshi da numfashin birnin, da kyawu da sirrinsa. Yana fito da abin da ido ba ya faye gani.

Victor Omondi yana da tarin masoya a soshiyal midiya, inda yake nuna yadda yake zane-zanensa.

Victor ya bayyana cewa "Manufata ita ce na fito da kyawun birnin Nairobi ta hanyar zane-zane."

Mafarin harkar zane-zanensa tun a shekarun yarinta ne sanda yana makaranta, wato lokacin da yake dan shekara hudu. Victor yakan tuna zanensa na farko a duniya, inda ya zana wani dan wasan zari-ruga yana tsaka da wasa.

Mafarin tashe

Zanensa na farko ya samu karbuwa wajen malamansa da 'yan ajinsu, wanda daga nan ne ya tunduma fagen zane ka-in da na-in.

Ya ce "Ina tuna farin cikin da na yi lokacin da 'yan ajinmu da malamaina suka kira zane na abin yabo".

Sai dai Victor ya fuskanci wasu kalubale. Fagen gidajen nune-nune suna da wuyar sha'ani, amma dai yana alfari da cewa ya kware a fagensa. A yanayin da soshiyal midiya take da tasiri, Victor ya samu damar baje koli a duniyar intanet.

Harkar zane ta bude masa kofofin samun mabiya a fadin duniya, inda ya gamu da masoya zane da masu siyan zane-zane daga nahiyoyin duniya.

Yayin da Victor ke labarta rayuwarsa ta zane, ya bayyana cewa ya dogare ne kan armashin rayuwar birnin Nairobi. Yana amfani da fasaharsa wajen fito da abubuwan da ba kowa yake lura da su ba.

Ya zabi ajiye aikinsa don ya mayar da hankali kan abin da ya fi sha'awa. Victor Omondi, dan baiwar zane ya zama abin misali na tasirin zane-zane, da fikira, da salon zane da ke fito da ruhin rayuwar garin Nairobi, a zayyane ta yadda zai burge mutane.

TRT Afrika