Wata 'yar Nijeriya Chidinma Modupe Okafor ta shiga kundin bajinta na Guiness World Record GWR a matsayin wacce ta fi daɗewa tana saƙar kwarashi a duniya, inda ta shafe sa'a 72 tana yi.
Kundin bajinta na GWR ya ce Okafor mai shekara 30, ta saƙa wata farar riga ta zuwa liyafa a cikin kwana ukun da ta shafe tana ƙoƙarin shiga kafa tarihi.
Ana amfani da ulu da kibiyar kwarashi ne wajen saƙa kaya musamman irin na sanyi ko na kwalliyar kujeru da sauran su.
Okafor ta karya tarihin da Alessandra Hayden 'yar Amurka ta kafa na wacce ta daɗe tana saƙar kwarashi a duniya, inda ta taɓa shafe awa 34 da minti bakwai.
Sha'awar abin tun ƙuruciya
Tun tana ƙarama Chidinma take saƙa kaya da kwarashi saboda abin da take so ne.
Ta ce ta fara burin shiga kundin bajintar ne saboda sha'awar saƙa da take da ita tun tana ƙarama.
"Ina da burin nuna fasaha da jajircewa da ke cikin wannan sana'a da kuma wayar da kan jama'a game da sana'ar kwarashi da fa'idarsa," in ji Okafor.
Don ta samu tabbatuwar nasararta daga kundin GWR, Chidinma ta dage don cimma muradinta na kai wa ga ci.
Dokoki masu tsauri
An bai wa Chidinma izinin hutawa na tsawo awa biyu a duk rana, wato ma'ana minti biyar bayan kowace awa ɗaya tana saƙa.
A waɗannan lokuta na hutu ne kawai za ta iya cin abinci ta yi barci, ta zagaya banɗaki ko sauya tufafinta, in ji GWR a cikin jawabin karramawa da suka yi.
"Har ila yau, lamarin yana buƙatar juriya ta jiki da kuma dabara don kiyaye daidaiton taki tare da rage gajiya," Okafor ta bayyana.
Da farko dai rigar aure Chidinma ta fara saƙwa, amma da lokaci ya ƙure kuma ta fara gajiya, sai ta yanke shawarar mayar da ita rigar zuwa liyafa.
"Na kasa ƙara awanni," ta bayyana.
Ta samu ƙwarin gwiwa daga ‘yar kasarta Hilda Baci, wacce a shekarar da ta gabata ta kafa tarihi na wacce ta fi daɗewa tana girki a duniya.