Wani ɗan Nijeriya mai shekaru 24 ya kafa tarihi kundin bajinta na duniya wajen zama wanda ya kafa tarihi a buga wasan gem na bidiyo a fannin ƙwallon ƙafa na tsawon kwanaki uku.
Matashin mai suna Oside Oluwole ya buga wasan gem na bidiyo mafi daɗewa na tsawon sa’o’i 75, inda ya doke tarihin da aka kafa a baya na sa’o’i 50, wanda David Whitefoot na ƙasar Ingila ya kafa a shekarar 2022.
''Na yi matukar farin ciki da sanarwar da aka yi a hukumance cewa yanzu ni ne mai riƙe da kambin tarihi na duniya GWR (Guinness world record) kan wanda ''ya fi daɗewa a buga wasan gem bidiyo a wasan kwallon kafa''.
"Na yi hakan ne ta amfani da fasahar wasa na Dream League Soccer na 2023 har tsawon sa'o'i 75, wanda ya zarce tarihin da aka kafa a baya na sa'o'i 25!'' kamar yadda Oluwole ya rubuta a shafinsa na Instagram yana mai tabbatar da nasarar cikin farin ciki.
Guinness World Records ma ya tabbatar da wannan nasarar.
''A baya babu wanda ya taba kafa irin wannan tarihi na samun tazara mai yawa kamar Oside.
A shekarar 2010 ne dai aka fara kafa wannan tarihi inda aka samu tsawon sa'o'i 24 a buga wasan, sai kuma daga baya ne adadin lokacin ya yi ta ƙaruwa har zuwa sa'o'i 50" bayan an fafata sau bakwai a cikin shekaru 11," a cewar wata sanarwa da GWR ya fitar a ranar Talata.
Oluwole, wanda aka fi saninsa a duniyar wasan gem da suna "Khoded," ƙwararren masanin kimiyyar halittu ne wanda a halin yanzu yake aiki a matsayin dillalin motoci.
Ya ce, ya gwada gasar ne don tara kudin wani ƙaramin asibiti da ke mahaifarsa na Ijebu Ode da ke yakin kudu maso yammacin Nijeriya.
Oluwole buga wasan ƙwallon ƙafa na fasahar ''Dream League 2023 akan wayarsa ta iPhone, wanda ya haɗa da allon TV, inda ya buga wasanni fiye da 500, in ji GWR.
Kamar kowace 'gasa mafi daɗewa ko tsayi', ya samu minti biyar na hutawa bayan kowace sa'a a yayin wasan, inda zai samu damar cin abinci da kuma barci ko amfani da bayan gida.
"Na ji daɗin buga wasan har tsawon sa'o'i 75 kai tsaye inda na samu hutu wasu 'yan sa'o'i na hutuwa. ko da yake ba abu bane mai sauƙi, amma dole ne in ce na ji daɗi kuma na yi farin ciki, ” Oluwole ya shaidawa GWR.
Oluwole ya ce Chef Hilda Baci ne, wadda ta yi nasarar kafa tarihin girki na tsawon lokaci da ya mamaye Nijeriya a bara ta ba shi kwarin gwiwa tare da zaburar da shi wajen daukar wannan kalubale.
"Nasarar nan ba za ta taba yiwuwa ba, ba tare da goyon bayan dangina da 'yan'uwana ba... yarda da ni da ku ka yi a ko yaushe ya ƙara min azama ta kowane mataki,'' in ji Oluwole.