Wani gwarzon ɗan wasan dara, ɗan Nijeriya kuma mai kishin ilimin yara ya buga wasan chess na tsawon awa 58 ba tsayawa a dandalin Times Square na birnin New York City. Hakan yunƙuri ne na kafa sabon tarihi a kundin bajinta na Guinness World Record ajin wanda ya fi daɗewa yana buga wasan chess ba dakatawa.
Tunde Onakoya, ɗan shekara 29, yana fatan tara dala miliyan ɗaya don ilimin yara a faɗin Afirka, ta hanyar yunƙurin kafa tarihin bajinta da ya fara ranar Laraba.
A daidai ƙarfe 2 da rabi na safiyar Asabar ne Tunde ya haura awanni 58, inda hakan ke nufin ya haura tarihin da ake da shi a yanzu na buga chess ba tsayawa, na awa 56, da minti 9 da sakan 37, wanda a 2018 Hallvard Haug Flatebø da Sjur Ferkingstad daga Norway suka kafa.
Zuwa yanzu, hukumar kundin bajinta ta Guinness World Record ba ta fitar da sanarwa ba game da yunƙurin na Tunde. A wasu lokutan yakan ɗauki ƙungiyar makonni kafin ta tabbatar da sabon tarihin bajinta.
Gagarumin goyon baya
Tunde Onakoya ya kara da Shawn Martinez, zakaran wasan chess na Amurka, kamar yadda ƙa'idojin hukumar Guinness World Record suka tanada cewa wajibi ne duk wani yunƙurin kafa tarihi ya haɗa 'yan wasa biyu da za su buga wasa ba tsayawa har na tsawon lokacin.
Tunde na ta samun ƙaruwar magoya baya a intanet da ma dandalin da yake wasan, inda aka ji kiɗan Afirka na tashi don nishaɗantar da 'yan kallo da magoya baya da suke tafi suna jinjina masa.
Yunƙurin kafa sabon tarihin bajintar don “tabbatar da burin miliyoyin yara ne a faɗin Afirka waɗanda ba sa iya zuwa makaranta,” cewar Tunde Onakoya, wanda shi ne ya kafa ƙungiyar sa-kai ta Chess in Slums Africa a shekarar 2018.
Ƙungiyar tana da burin tallafa wa ilimin aƙalla yara miliyan 1 a unguwannin marasa galihu a nahiyar Afirka.
Shinkafa jollof a teburi
Tunde ya faɗa ranar Alhamis bayan ya cika awanni 24 da fara wasan cewa, “Ina jin ƙarfi ɗari bisa ɗari a yanzu, saboda mutanena suna nan suna ba ni goyon baya da kaɗe-kaɗe."
Kayan abincin da Tunde ke ci sun haɗa da: Ruwan sha, da shinkafa jollof, wadda sanannen girki ne na Yammacin Afirka.
Bayan duk awa ɗaya na buga wasa, Tunde da abokin karawarsa suna samun hutun minti biyar kacal. Wani lokacin suna haɗe hutun inda Tunde ke amfani da shi wajen hira da 'yan Nijeriya da 'yan New York da ke ba shi ƙwarin gwiwa. Kuma yakan shiga ya yi rawa tare da su.
An tara jimillar dala dubu $22,000 cikin awannin 20 da fara wasan, in ji Taiwo Adeyemi, manajan Tunde Onakoya.
Tunde ya kuma ce, “Na samu tarin goyon baya daga 'yan Nijeriya a nan Amurka, da shugabanni a faɗin duniya, da taurari da ɗaruruwan masu wucewa ta dandalin nan".
'Yan Nijeriya su ne suke bibiyar yunƙurin na Tunde, inda a can ne ya saba shirya gasar buga chess ga yara da matasa da ke rayuwa a tituna.
Akwai yara sama da miliyan 10 a faɗin ƙasar da ke yammacin Afirka, waɗanda ba sa zuwa makaranta — wanda adadi ne da ke jerin ƙasashen da batun ya fi ƙamari.
Daga cikin waɗanda suka bayyana goyon bayansu, akwai taurari da manyan 'yan siyasa kamar tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo, wanda ya rubuta saƙo ga Onakoya a shafin X cewa, “Ka tuna da kalamanka masu ƙarfi: wato 'Zai yiwu ka cimma babban aiki daga waje ɗan ƙarami.’"