Wani yaro ɗan shekara ɗaya da haihuwa ya kafa tarihi bayan da Guinness World Record ya tabbatar da shi a matsayin wanda ya fi ƙwarewa a zane-zane na fenti a shekarunsa.
Yaron mai suna Ace-Liam Nana Sam Ankrah asalin ɗan Ghana ne kuma mahaifiyarsa mai suna Chantelle Eghan ita ma tana zane-zanen ta hanyar fenti, ita kuma ta sanar da wannan labarin a shafin sada zumunta.
"Yarona Ace Liam ya zama mai kambun GWR na yaro mafi ƙanƙanta da ya ƙware a zane. Muna godiya Ghana dangane da wannan goyon baya, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
A cewar GWR, Ace-Liam na amfani da dabarar da ta ƙunshi sarrafa fenti na acrylic wurin zane, haka kuma yana amfani da hannaye da jiki don yin zane-zane na musamman.
Muna farin cikin sanar da ku cewa mun karɓi buƙatarku ta yaro (namiji) mafi ƙanƙanta a zane-zane, kuma a yanzu kai ne mai riƙe da kundin tarihin Guinness World Records, '' in ji GWR a cikin sakon taya murna ga Ace.
Kafin ya cancanci samun wannan kyautar, sai da Ace ya yi fenti, sannan ya shiga baje-kolin da yin tallace-tallace sannan kuma ya bayar da shaida na taron, gami da ɗaukar lamarin a kafafen watsa labarai da shafukan zumunta, kamar yadda mahaifiyarsa ta yi bayani.
"Tun bayan zanensa na farko mai suna "The Crawl", ya yi wasu fentin kusan 20 (yana ci gaba da yi)," in ji GWR, waɗanda suka rinƙa saka wa yaron ido a ayyukan da yake yi.
Haka kuma Ace ya soma baje-kolinsa na rukuni na farko, mai suna "The Soundout Premium Exhibition," wanda aka gudanar a Gidan Tarihi na Kimiyya da Fasaha na Ghana, inda ya yi zane-zane har 10 wanda ya samar da su tsakanin lokacin da yake wata shida zuwa shekara da wata huɗu waɗanda aka gabatar da su domin sayarwa.
A baya dai wani ɗan Amurka mai suna Dante Lamb ne ke riƙe da wannan kambun wanda ya samu yana ɗan shekara uku da haihuwa a 2003.