Daga Charles Mgbolu
Labarin mai dafa abinci dan Ghana na yadda ya shiga Kundin Bajinta na Duniya a bajintar girki mafi dadewa ya fara canja zane.
A ranar Talata ce gidajen jarida a kasar Ghana suka yi ta yada labarin cewa Smith ya karya tarihin mutumin da ya fi dadewa yana girki.
Smith ya bayyana wa yan jarida a Accra cewa, Wannan rana ce da ba zan taba mantawa ba. Ina matukar alfahari da jin dadin tsayawa a gabanku a matsayin mai rike da kambun Kundin Bajinta ta Duniya.
Haka kuma Smith ya nuna satifiket, daga Kundin Bajintar na tabbatar da nasararsa, wanda hakan ya sa labarin ya karade koina cikin kankanin lokaci.
Amma a wani lamari mai kama da alamara, wanda ya sa murnar masoyansa ya fara komawa ciki, Kundin Bajintar ta Duniya sun fito sun karyata batun.
Haka kuma kundin sun kara da cewa satifiket da Smith ya nuna wa yan jarida na bogi ne.
Wannan ba gaskiya ba ne. Ba shi da kambun bajinta, sannan satifiket da yake nunawa ba namu ba ne. Har yanzu mai rike da kambun girki mafi dadewa shi ne Alan Fisher dan kasar Ireland, wanda ya yi girki na tsawon awa 119 da minti 57 da dakika 16 a Matsue da ke yankin Shimane na kasar Japan, a girkin da ya yi a tsakanin ranar 28 ga Satumba zuwa 3 ga Oktoban 2023, inji kundin a sanarwar da suka fitar.
Shi dai Smith ya ce ya samu nasarar ce bayan ya yi girki na tsawon awa 820 da minti 25 daga ranar 1 ga Fabrairu zuwa 6 ga Maris din 2024.
A shafin intanet na Kundin Bajinta na Duniya, har yanzu, wanda ya yi girki mafi dadewa shi ne Alan Fisher wanda ya dauki awa 119 da minti 57 da dakika 16 yana girki a Matsue da ke yankin Shimane na kasar Japan a girkin da ya yi a tsakanin ranar 28 ga Satumba zuwa 3 ga Oktoban 2023.
Haka kuma kundin bajintar sun dakatar da yunkurin kafa bajintar girki mafi dadewa, inda suka rubuta a shafinsu na intanet cewa, a yanzu mun dakatar da yunkurin kafa tarihin girki mafi dadewa.
Mai dafa abinci Ebenezer Smith ya gaza ne wajen kafa wannan yunkurin bayan wata mai dafa abincin ita ma daga Ghanan mai suna Failatu Abdul Razak ta gwada, ta gaza.
A wata tattaunawa da tashar FM ta Hitz da ke Accra a ranar 3 ga Yulin 2024, manajan Smith, Benny ya ce ba shi da masaniya a kan abin karyata bajintar Smith da kundin bajintar suka yi, inda ya nanata cewa suna da kwafin sakon imel da kundin suka turo na tabbatar da Smith a matsayin sabon mai bajintar girki mafi dadewa a duniya.