Daga Pauline Odhiambo
Idan da a ce farin ciki zabi ne, to mai zane dan kasar Uganda Bwambale Wesely na yin nasa farin cikin yayinda yake zana hotunan manyan mata.
Mafi yawan zanensa sun kasance na mahaifiyarsa da yayyensa mata da suka taimaka wajen rainon sa a gundumar Kasese ta Uganda da a nan ne labarin zanensa ya faro.
"Zane na na bayar da labarin yadda na yi nisa, da kuma matan da suka taimaka min na kai inda na ke a yau," Bwambale ya fada wa TRT Afirka.
Zane na zamani wata inuwa ce ta nau'ikan zanen yau da baya-bayan nan, ba wai wani nau'i na sana'ar zanen ba.
Zanen masu rasjin kare mata a gefe guda na bayyana gwagwarmayar da aka fara tun karni na 20, wanda ke bayyana gudunmowa da kwarewar mata a siyasance da zamantakewa, kamar yadda shafin Art Forum ya bayyana.
A shekarun 1960 da 1970, ta hanyar gwagwarmayar masu kare mata, mata da dama sun fara kalubalantar rawar da ake sa ran mata su taka a bangarorin al'umma daban-daban, ciki har da zane-zane da maza suka mamaye.
Manufar gwagwarmayar ita ce a kawo sauyi ga duniya, har ta kai ga samar da daidaito da 'yantar da mata.
Alkawari tsakanin mata
Zane a Afirka na d afadi kuma da tarihin da ke koma wa ga zamanin da babu tarihi, inda ake da zane-zane daban-daban, ciki har da na mutane, tufafi, da fenti.
Amma a yayinda ra'ayin daidaita mata da maza ke ci gaba da yaduwa, sai duniyar zane ta fadada, ta sanya muryoyi da ra'ayoyi, ciki har da na maza masu zane a Afirka irin su Bwambale, wanda zanensa ke bayyana kimar mata.
"Labaran da ke tattare da zanen da na ke yi na da ma'ana sosai," in ji shi "Na yi zane a wurare da dama, har ma da wajen da mata ke bayani, inda 'yan uwana mata a wasu lokutan suke bayyana sirrinsu."
Aikin zanen Bwambale na zane na mayar da mutane ga tunanin wani zamani ko yanayi da ya shude; zanensa na hakaitowa mutum shekarun 1970 da aka fara gwagwarmayar 'yantar da mata a Afirka da waus sassan duniya.
Yayyensa mata uku, wadanda yake yawan zana su, na yawan bayyana a zane-zanensa. Nutsuwa da kwarjininsu na kira ga masu kallo su yi kawance da su da mayar da hankali kan hotunansu.
"Na ga yayyena mata na shan wahala amma na kuma gan su suna farin ciki. Labaransu sun karfafa min gwiwa wajen yin zanen labaran mata da dama da suka fuskanci kalubale da yawa a rayuwa," in ji mai zanen da ke zaune a birnin Kampala.
Karfin gwiwa daga mata
Duk da cewar karfin gwiwar zanensa ya zo daga labaran masu dadi da dama na rayuwarsa ta yarinta, da fari iyalinsa sun yi tantama kan hukuncin da ya yanke na fara sana'ar zane.
"A yankunan Uganda da dama, ana yi wa kallon zane kallon a matsayin basira kawai, ba wai abinda za a nemi abinci da shi ba," in ji mai zanen dan shekara 30. "Da fari na yi tantamar yin karatin Injiniya amma sai kawia na yanke shawarar yin abinda na ke sha'awa tun ina yaro karami."
Bwambale ya yi karatu a kwalejin Michelangelo da ke Uganda inda ya kammala diploma a fannin zane. Daga baya ya yi digiri a jami'ar Kyambogo.
Ya ce "Na fito daga gidan da ake yin kasuwanci, saboda hakan bayan na kammala jami'a, sai na fara kasuwancin sayar da tufafi na maza, amma ba na jin dadin kasuwancin gaba daya, sai na koma harkar zane tun daga wannan lokacin."
Ya fara gwaji da hotunan wasu inda daga baya kuma ya tsunduma gaba daya ga amfani da goyon bayan da mata ke ba shi.
Shafin Instagram
Ya je wurare da dama a yankinsa amma suke nuna masa ba za su karbi sabbon hotuna da wajen sabon mai zane ba. Sai Bwambale ya juya ga shafin Instagram don yada zanensa a duniya.
“Instagram ya taimaka min wajen haduwa da mashahuran masu sayar da hotuna a Amurka da Birtaniya," ya fada wa TRT Afirka.
"Na samu dama ta yadda aka nuna ayyuka na a wajen baje-kolin zane-zane a Landan a Daapah Gallery da kuma a Thierry Gallery da ke Amurka."
Haka zalika a California ma an nuna ayyukansa a yayin baje-kolin hotuna na Band of Vices.
Wani rahoto da Art basel suka fitar ya bayyana cewa sama da ayyuka 2,700 na masu zane a Afirka ne aka yi gwanjonsu a 2023 - kusan ninkin wadanda aka sayar a 2020.
A 2022 kawai, ayyukan masu zane na Afirka ya samar da dala miliyan $63 a wajen gwanjonsu, inda a 2021 aka samu dala miliyan $47.
An dinga sayar da kayan zanen Bwambale kan kudi $2,000 zuwa $6,000 a kasuwannin kasa da kasa, wanda hakan ke kara karfafa masa gwiwa.
"Shawarata ga masu zanen da ke taso wa shi ne su yarda da kawunansu, kuma su yi amfani da shafukan sada zumunta wajen tallata hajojinsu. Aiki da koyo a wajen masu zane daban-daban na sanya kwarewa."