Banton ya bayyana cewa shi ɗan ƙabilar Igbo ne a Nijeriya. / Hoto: Buju Banton/ Instagram

Mawaƙin nan wanda ya taɓa cin kyautar Grammy ɗan Jamaica, Buju Banton, ya tabbatar da cewa shi asalin ɗan Nijeriya ne.

Banton, wanda sunansa na asali shi ne Mark Myrie, ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a matsayin baƙo a wani shirin podcast wanda N.O.R.E. da kuma DJ EFN suka jagoranci gabatar da shi.

Ya bayyana cewa an bi salsalar asalinsa kuma an gano shi ɗan ƙabilar Igbo ne, wadda ƙabila ce da ta fi yawa a kudu maso gabashin Nijeriya.

"Dangina asalinsu 'yan Nijeriya ne. Ni ɗan ƙabilar Igbo ne kamar yadda asalina ya nuna," kamar yadda ya bayyana a hirar.

Sai dai babban abin da ya ja hankali a hirar tasa ita ce batun da ya yi dangane da yadda kiɗan Afrobeats ke ƙara tasiri a cikin al'umma.

Banton ya yi haɗaka da mawaƙin nan na Nijeriya na Reggae kuma mai rawa kan dandamali wato Patoranking. / Hoto: Buju Banton

"Akwai buƙatar mawaƙan Afirka su rinƙa yin tasiri da waƙoƙin da suke yi. Babu wata waƙa ta Afrobeats guda ɗaya da zan iya bayar da misali da ita.

"Mawaƙan da nake girmamawa a Afirka sun haɗa da Fela Kuti da Youssou N’Dour da Lucky Dube daga Afirka ta Kudu da Salif Keita da kuma Baaba Maal.

Ya soki mawaƙan Afrobeats da yanke hulɗa da 'yan Jamaica a yunƙurin da suke yi na haɗa kai da sauran sassan duniya duk da jin daɗi da samun kwarin gwiwa daga reggae da kiɗan dancehall.

A shekarar 2011, Banton ya samu kyautar Grammy ta mawaƙin Reggae wanda kundinsa ya fi shahara a kyautar Grammy ta 53 a Los Angeles.

TRT Afrika