Babu tsarin shari'a kafin zama mashawarci kan tafiyar da rayuwa. / Hoto: Getty Images

Daga Firmain Eric Mbadinga

Shin mashawarci kan tafiyar da rayuwa zai iya jagorantar ka zuwa nasara ko farin ciki? Da yawa cikin 'yan soshiyal midiya a Afirka sun yadda da hakan, don haka suke ziyarta su don inganta rayuwarsu da ayyukansu.

Aikin mashawarta kan tafiyar da rayuwa yana da faɗi, inda ya shafi kusan duka harkar lafiyar jiki da ruhin mutum. Amma soshiyal midiya ta ba da dama harkar ta yi tashe, inda take ɗaukaka kima da arziƙin mashawartan.

Waɗannan mutanen suna da ɗimbin mabiya a Instagram, da Facebook, da YouTube da TikTok. Kuma sakamakon biyan kuɗi da kamfanonin sadarwa suke yi, sukan samu kuɗi saboda ayyukansu kan shafukan sadarwar.

Sai dai kuma, salon yadda harkar take yakan janyo tambayoyi game da inganci da sahihancin ayyukansu.

Rashin ɗa'a ga doka

Baya ga janyo cecekuce da zuzutawa, wasu dabarun da mashawarci kan tafiyar da rayuwa suke bai wa mutane yaka haifar wa mabiyansu shiga haɗarin abubuwa kamar bayanan ƙarya da zamba.

Dandalin soshiyal midiya sun ba wa mashawarci kan tafiyar da rayuwa su samu tarin mabiya. / Hoto: AFP

Wasu masu sharhi sun ce wasu cikin mashawarci kan tafiyar da rayuwa suna shiga fagen da ke da sarƙaƙiya a kimiyyance, kuma hakan zai iya haifar da tasgaron ilimi, da yaɗa bayanan bogi ga mabiyansu.

Sahihancewar ƙwararru

Masu sharhin sun ƙara da cewa, akwai buƙatar ƙwararrun hukumomi da za su yi kyakkyawar tantancewa kan mashawarci kan tafiyar da rayuwa.

Sylvère Boussamba ya ce yan zurfafa iliminsa don cigaba da zaman mai tasiri. / Hoto: TRT Afrika

Wani masanin fasahar hada-hadar kuɗaɗe, Sylvère Boussamba shahararren mutum ne a fagen fasahar kwamfuta. Tun yana shekara 11, ya fara ƙwarewa kan ilimin kwamfuta, kuma bayan shekaru 40 yanzu ya zamo babban ɗan kasuwa a birnin Libreville, Gabon.

Duk da mabiyansa a soshiyal midiya ba su da yawa idan aka kwatanta da sauran mashawarci kan tafiyar da rayuwa, amma Boussamba ƙwararren mashawarci kan tafiyar da rayuwa da yake da shedar ƙwarewa. Ya fi mai da hankali kan shawara kan ɗabia da kuma ta dijital.

Ya bayyana cewa, 'Na samu horo a cibiyar John C. Maxwell Academy a Amurka. Kuma na fito a matsayin mashawarci kan tafiyar da rayuwa mai shaidar ƙwarewa, mai ba da horo, kuma malami."

'Boussamba ya ce, 'Ba ka daina fahimtar kanka, da sauran mutane, da abin da ke faruwa a duniya da sabbin salo da dabaru, ko dai na fasaha, ko na daban. Na ware wani ɓangare na lokacina don koyo. Na shiga kwasakwasai don diadaita yadda nake aiki".

TRT Afrika ta tuntuɓi wasu sanannun mashawarta kan tafiyar da rayuwa da ke asashen Afrika masu amfani da Faransanci don tattauna buƙatar saka ƙa'idoji a harkar. Wasu sun ƙi amincewa su ce komai saboda dalilan ƙashin-kai.

Cirille Nyeck ya nanata cewa mashawarta kan tafiyar da rayuwasuna buƙatar samun horo. / Hoto: Afrika

Cirille Nyeck, wani limamin Katolika kuma mashawarci kan tafiyar da rayuwa da ke da shaidar ƙwarewa daga Kamaru, yana cikin waɗanda suka amince su yi magana kan batun. A ra'ayinsa, ba a iya zama mashawarci kan tafiyar da rayuwa ta ɓarauniyar hanya.

Ya bayyana cewa, "'Shawara kan tafiyar da rayuwa fage ne na ɗabi'a don samar da tallafi don cimma wani buri. Manufar ita ce mashawarcin zai tafiyar da wanda ke neman shawararsa zuwa hanyar da zai fayyace wani buri da ya dogar kansa, ko dai na rayuwarsa, wato wanda zai yi la'akari da kyawawa ko munanan sakamako".

Nyeck masanin kimiyyar shirya ƙwaƙwalwa kwamfuta da harsuna ne, kuma a yanzu yana aiki kan kundin bincike na kimiyyar siyasa.

Ya ce mai neman shawara yana da duka albarkatu a karan-kansa don cimma manufofinsa.

Ya ƙara da, "Harkar shawara kan tafiyar da rayuwa aiki ne da ke buƙatar ingancin tunani da ƙwarewa. Kana buƙatar samun horo sosai."

Samun kuɗi ta soshiyal midiya

Wani salo da mashawarci kan tafiyar da rayuwa suke yi don samun kuɗi daga kamfanonin sadarwar zamani, ko dai ƙwararru ko ba ƙwararru ba, sun haɗa da buɗe tashar YouTube, Facebook ko TikTok a wajen Afirka don a biya su kuɗi mafi daraja.

Ga misali, a TikTok dole sai bidiyo ya samu aƙalla 'yan kallo 100,000, kuma mai asusun yana da dubban mabiya kafin ya samu kuɗi.

Masu sharhi sun ce, sharuɗɗa irin waɗannan sukan saka mashawarci kan tafiyar da rayuwa da suka wallafa bidiyo su mayar da hankali kan tara bidiyoyi maimakon ingancin aikinsu.

Za ka ji suna yawan maimaita kalmomi a wallafe-wallafensu kamar "taɓa, sharhi, da yaɗa kai-tsaye", wanda masu kallonsu suke yawan ji.

TRT Afrika