Jinsin halittar dabba ta Farar karkanda na fusknatar matsin lamba. / Hoto: Getty 

Daga Charles Mgbolu

A shekaru 10 masu zuwa kungiyar kare dabbobi ta Afirka Parks tare da hadin gwiwar gwamnatin Afirka ta Kudu za su gudanar da aikin sake maido da nau'in dabbar farar karkanda 2,000 zuwa manyan dazuka.

Wannan yunkuri zai zama daya daga cikin ayyuka mafi girma da nahiyar za ta yi a kokarinta na sake dawowa da wata dabba a 'yan shekarun nan.

Africa Parks ta ce za a karkasa tsarin kiwon, sannan za a kawo karshen aikin ne da zarar an sako karkanda zuwa cikin dazuka.

Tsarin na tattare da kalubale masu tarin yawa, inda masu rajin kare namun daji za su himmamtu wajen tabbatar da cewa ba a tabka kura-kurai a aikin sake maido da kudancin farar karkanda wadda nau'inta ta kusan shafe da daga doron kasa.

Nau'in dabbar farar karkanda na fuskantar tsananin matsin lamba, musamman a kasar Afirka ta Kudu, saboda ayyukan mafarauta.

Masu kula namun daji suna aiki don tabbatar da cewa ba a samu kurakurai a tsarin halkinta dabbar ba. Hoto:  Getty

“Kungiyar Afrika Parks ba ta da niyyar daukar nauyin aikin kiwon karkanda har 2,000 waɗanda za a killacesu.

Duk da yake, mun fahimci alfanun neman mafita ga wadannan dabbobin domin su sake taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantaccen yanayin muhalli," a cewar wata sanarwa da Peter Fearnhead Shugaban kungiyar African Parks ya fitar.

"Ma'aunin wannan aikin yana da girma sosai, don haka yana da ban tsoro, Amma duk da hakan yana ɗaya daga cikin ayyukan mafi ban sha'awa da kuma dama ta dabarun kare namun daji a duniya, "in ji Fearnhead.

Abun ban sha'awa anan shine, aikin sake maido da nau'in dabbar farar karkanda.

Dabarar samar da cikakkiyar, ƙungiyar yawon buɗe ido ta kare namun daji a Afirka ta Kudu, ta bayyana shirin da za a bi wajen cimma wannan tsarin.

Bayan cikakken bayani game da abubuwan da za a yi da waɗanda ba za a yi ba, an tura tawagar da ta ƙunshi likitocin dabbobi da masana kimiyyar halittu da masu kare dabbobi da masu kula da su zuwa yankin da aka ga rukunin karkanda (masu hatsari), galibi daga sama aka hango su.

An yi amfani da jirgin helikofta da dabarun matukin jirgin wajen hango halittun, ana ware nau'in karkanda da aka zaɓa don raba su da sauran nau'in sannan sai a harba kan dabbar.

Da zarar harbin ya kai ga gabar da aka harba, karkanda za ta ci gaba da gudu na kusan mintuna 6 zuwa 8 kafin ta tsaya ta kwanta.

Sai tawagar kasa ta matso.

An dauke iskar da dabbar Rhinos ke shaƙa: Hoto Getty

Daga wannan lokacin, dole duk wanda ke kasa ya yi gaggauta zuwa wajen.

Ana lulluɓe idon karkandan sannan a sanya wani safa a cikin kunnuwansu don hana su jin wani motsi kafin a iya tattara bayanai, kamar DNA da sauran alamomin halitta, don su taimaka a iya gano nau'in karkandan a cikin daji tare da kimanta nasarar da aka samu na tsarin sake maido da dabbar.

A ƙarshe, ana sanya wata na'urar bin diddigi a jikin dabbar kafin a ɗauke ta zuwa inda za a ajiye ta.

Farar karkanda na kudu ɗaya ne daga cikin nau'ikan farar karkanda biyu da suka rage; daya nau'in ita ce farar karkanda ta arewa, wadda mata biyu kacal suka rage, hakan ya sa nau'in dabbar ta bace, in ji Africa Parks.

Kungiyar Africa Parks ta ce za a mayar da kowace karkanda zuwa yankunan da aka kayyade a fadin nahiyar Afirka domin bayar da gudunmawa ga muhallin dazuka ta hanyar samar da sinadari mai gina jiki, da adana sinadarin carbon da kuma kara kudaden shiga na yawon bude ido ga jama'ar yankin.

Ana lulluɓe idon karkandan sannan a sanya wani safa a cikin kunnuwansu don hana su jin wani motsi kafin a iya tattara bayanai, kamar DNA da sauran alamomin halitta, don su taimaka a iya gano nau'in karkandan a cikin daji tare da kimanta nasarar da aka samu na tsarin sake maido da dabbar.

A ƙarshe, ana sanya wata na'urar bin diddigi a jikin dabbar kafin a ɗauke ta zuwa inda za a aije ta.

Farar karkanda na kudu ɗaya ne daga cikin nau'ikan farar karkanda biyu da suka rage; daya nau'in ita ce farar karkanda ta arewa, wadda mata biyu kacal suka rage, hakan ya sa nau'in dabbar ta bace, in ji Africa Parks.

Kungiyar Africa Parks ta ce za a mayar da kowace karkanda zuwa yankunan da aka kayyade a fadin nahiyar Afirka domin bayar da gudunmawa ga muhallin dazuka ta hanyar samar da sinadari mai gina jiki, da adana sinadarin carbon da kuma ƙara kudaden shiga na yawon bude ido ga jama'ar yankin.

TRT Afrika