Daga Coletta Wanjohi
Shagon ɗinki na Rachel Anekea da ke rukunin shaguna na Sunbeam da ke kan titin Mfangano a Nairobi ya wuce wurin kasuwanci a gare ta. Wani abin soyayya ne a gare ta.
Tsawon shekara 15, ta yi amfani da zuciyarta da ƙarfinta wurin samar da abin da nan gaba take tunanin zai zama babba. Tsawon lokaci, ta zuba jari kan kekunan ɗinki uku domin biyan buƙatun kwastamominta waɗanda ke ƙaruwa a kullum.
Abubuwa na tafiya lafiya lau a gareta har zuwa 25 ga watan Yunin 2024, bayan wani abin da ba ta yi zato ba ya faru da ita.
A daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga kan ƙarn haraji da aka yi a Kenya, wasu daga cikin ɓata gari waɗanda ba a san ko su wane ne ba sun cinna wuta kan rukunin shagunan da shagon Rachel yake.
A daidai lokacin da rukunin shaguna na Sunbeam ya kama da wuta, wani ya kira ta ya shaida mata abin da ke faruwa. Rachel sai ta fara jin kamar za ta nutse a cikin ƙasa sakamakon girman abin da ta ji.
Rachel sai ta fara jin kamar za ta nutse a cikin ƙasa sakamakon girman abin da ta ji. “Rana ce ta zanga-zangar ƙin jinin haraji wadda matasanmu suka jagoranta, waɗanda suke da kyakyawan buri,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
“A ranar ni kaina na fita domin na shiga cikin tarihin da za a kafa. Wa ya yi tunanin cewa zai rikiɗe zuwa abin da ya faru a rukunin shagunan?
An shaida wa Rachel cewa wasu gungun mutane sun yi ƙoƙarin afkawa cikin rukunin shagunan, wanda yake a kulle a ranar a yunƙurin ɗaukar mataki.
“A lokacin da jami’an tsaro suka hana su shiga, sai suka dawo cikin fushi sosai, inda suka kutsa kai ciki suka zuba fetur a ko ina kafin suka cinna wa ginin wuta,” kamar yadda ta tuna, inda muryarta ke karkarwa a lokacin da take tunawa idonta na hawaye.
“Na rasa kekunan ɗinkina da kuma kayan da kwastamomina suka yi oda. Akwai iyalai kusan 600 waɗanda suka dogara da rayuwa kan kasuwancin da muke yi daga ginin a halin yanzu suna zaune babu hanyar samun kuɗi.
Ba ni da komai.” Baya ga rasa kayayyaki, Rachel da wasu masu kasuwanci da ayyuka a rukunin shagna na Sunbeam na fama da firgici da kaɗuwa sakamakon waɗanda suka rasu a ranar.
Wani shagon sayar da kayayyaki wanda ake kira Quickmart wanda ke a kan layin rukunin shagunan shi ma an sace kayayyakinsa, haka kuma ɓata garin sun far wa wani shagon da ake kira Naivas da ke Moi Avenue da ke tsakiyar birnin.
Akwai sassan Kenya da dama waɗanda suka fuskanci irin wannan rashin dokar. La’akari da halin da ake ciki, wani direba da ke Nairobi David Murage ya damu kan bashin bankin da ya ci a watan da ya gabata.
“A lokacin da na ɗauki bashin domin sakawa a kasuwancina na tasi, alamu sun nuna cewa abubuwa suna kyau sakamakon mun soma kaiwa lokacin da masu yawon buɗe ido na ƙasashen waje da ke zuwa sosai. Sai na ƙara sayen wata mota, ba tare da sanin abin da ke jirana a gaba ba,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Wasu masu yawon buɗe ido waɗanda suka yi mani magana domin tafiya tsakanin Agusta zuwa Satumba sun fasa zuwa. Sun firgita bayan ganin abin da ya faru a ƙasar na tsawon makonni ana zanga-zanga.
Yadda aka lalata wurare da dama
Shugaba William Ruto a taron manema labarai a ranar 30 ga watan Yuni ya shaida cewa kayayyakin jama’a na kusan dalar Amurka miliyan 18.6 an lalata su. “An ƙona ofishin Alƙalin Alƙalai, an ƙona City Hall, da kuma majalisa.
Abin da ke faruwa kenan,” a cewarsa. Zanga-zangar ƙin jinin harajin, wadda wasu matasa suka jagoranta, ta fara ne a ranar 18 ga watan Yuni da farko an bayyana cewa ta lumana ce kuma mai alƙibla.
“Muna zaman lafiya” shi ne taken da suke faɗi a lokacin da masu zanga-zangar suka yi arangama da ‘yan sanda.
Babu rahoton lalata kayayyaki a ranar 25 ga watan Yuni, a lokacin da aka kai hari a majalisa da wasu gine-gine.
A hukumance, sama da mutane 20 ne aka ruwaito sun mutu a arangamar da suka yi da ‘yan sanda a ranar. Sai dai hukumar kare hakkin dan Adam ta Kenya ta ce adadin wadanda suka mutu bai gaza 39 ba.
A ranar 26 ga watan Yuni, Shugaba Ruto ya ce ba zai rattaɓa hannu kan dokar kudi ba. Washegari dai masu zanga-zangar sun fito kan tituna, inda wasu ke neman ya sauka daga mulki.
Kiran da ake yi na murabus ɗin Ruto ya zo dai-dai da yadda lokacin da ake lalata kayayyaki, inda aka rinƙa lalata dukiyoyi a Nairobi.
Shugaba William Ruto ya yi Allah-wadai da tashin hankalin, yana mai cewa “masu aikata laifuka” sun ƙwace zanga-zangar inda ya sha alwashin hukunta su.
Raila Odinga wanda shi ne jagoran haɗakar ‘yan adawa ta Azimio la Umoja, shi ma a ganinsa an ƙwace iko da zanga-zangar.
Ya yi Allah wadai da ita. “Hotunan yadda mutane suke kwasar ganima, barna, sun sha bamban da abin da aka gani a farkon zanga-zangar lokacin da take ƙarƙashin ikon Gen Z,” a cewarsa.
Sashen binciken laifuka na ƙasar ya saka hotunan mutanen da ake zargi da ɓarnata kayayyaki inda kuma suka buƙaci sauran jama’a da su taimaka su nuna sauran.
Ƙirga asara
Ga wasu da dama irin Rachel waɗanda aka lalata musu wuraren sana’a, ba su da tabbaci kan makomar da suke da ita.
Ko da abubuwa za su koma yadda suke a baya, ba a san me za ta gaya wa kwastamominta waɗanda suka biya kuɗin kayansu amma gobara ta lalata su ba.
Haka kuma ta ce ba ta san yadda za ta farfaɗo da kasuwancin da ta shafe shekara 15 tana ginawa ba amma aka lalata a rana guda.
Rachel ta yi nadamar rashin samun inshorar da za ta yi amfani da ita domin taimaka mata rage asara. “Mu ƙananan masu sana’a ne; ba mu taɓa tunanin inshora ba. Ta ya zan sani ko zan rasa kayayyaki na a hannun masu ɓarna?”
Haka kuma mai shagon da take haya a ciki ba ya ɗaukar waya, wanda hakan ya ƙara baƙin ciki ga Rachel. “Ina tsoron rasa aikina. Rayuwata na hannun masu taya ni jimami,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.