Yakin Sudan ya cika shekara daya da farawa, wanda ya yi sanadiyar raba kusan mutum miliyan biyar daga muhallansu a birnin Khartoum, inda yakin ya fi kamari. Hoto: Reuters      

Daga

Sylvia Chebet

Shekara daya kenan da fara gwabza yaƙi tsakanin sojojin Sudan da jami'an tsarin RSF masu adawa da gwamnati.

A ranar 15 ga Afrilun shekarar 2023 ce aka fara gwabza yakin, wanda tun daga lokacin ake cigaba da jefa bama-bamai da musayar wuta a birnin, wanda yake kusa da Kudancin Tekun Nil.

Lokacin da Jill Lawler, Babbar Jami'ar Aikace-aikace na Asusun UNICEF a Sudan ta ziyarci birnin Khartoum da makwabciyarta Omdurman bayan kusan shekara daya, ta yi mamakin abin da ta gani na yadda biranen suka fara zama kufai.

Ofishin Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya kiyasta cewa mutanen Khartoum, wanda a da ke dauke da kusan mutum miliyan shida a bara, yanzu ba su wuce mutum miliyan daya ba.

"Yadda aka ragargaza birnin abin takaici ne. Kunci da aka jefa wa mutanen birnin ya yi kamari," inji Lawler.

A game da ziyayar aikinta a Omdurman, Lawler da ma'aikatanta sun ziyarci asibitin da aka yanke wa mutum 300 kafa a wata daya. Sun ga yadda majinyata biyu suke kwanciya a gado daya domin marasa lafiya su samu gado.

A Darfur, wanda ya dade yana cikin rikicin kabilanci na kusan shekara 20, wannan rikicin ya kara dawo musu da abin jiya.

Hukumomin agaji sun ce yawancin wadanda suka tsira sun tsallaka kasashe masu makwabtaka da kasar irin su Chad domin tsira da rasuwarsu.

Mutanen kasar Sudan da suka tsere saboda yaki suna samun mafaka a kasar Chad. Hoto: Reuters

Yawan amfani da salon yakin sunkuru da ake kire "scorched-earth policy", inda ake lahanta duk wani da ake tunanin makiyi zai yi amfani da shi ya kara ta'azzara barnar da aka samu.

"Abun takaici ne matuka a ga kasar da ke habaka tana samun hadin kai ta sauya zuwa wani babban bala'i."

"Na tuna lokacin da nake fada wa abokan aikina cewa ban taba tunanin za a iya yin yaki a Sudan ba- ba a Darfur kawai ba, inda na fara aiki, har da Khartoum da sauran bangarorin kasar," inji Edem Wosornu, daraktan Aikace-aikace a OCHA, a tattaunawarta da TRT Afrika.

"Akwai ban takaici da bakin ciki ganin yadda kasar take daidaicewa."

Gudun neman tsira

Yakin wanda aka kwashe shekara ana yi, ya sa kasar Sudan ta zama wuri mai wahalar rayuwa musamman ga wadanda suke rayuwa a kasar a yanzu a cikin yakin, duk da cewa wasunsu dole ya sa suke zama.

Kusan mutanen Sudan miliyan tara ne suka bar garuruwansu a kasar, inda daga cikinsu miliyan biyu suka tsallaka zuwa wasu kasashen.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa an kashe akalla fararen hula 12,000 a yakin zuwa karshen shekarar 2023, duk da cewa ana tunanin wadanda aka kashe sun haura hakan. kuma har yanzu ana cigaba da gwabza yakin, wanda babu alamar sararawa nan kusa.

"Shekara daya ke nan, shin yaushe yakin zai kare? Shin za mu cigaba da zura ido ne Sudan na wargajewa? Me ya sa duniya ba za ta yi wani abu ba? Me ya sa ba mu samu tallafin da za mu taimaki mutanen kasar ba?" Inji Wosornu cikin alhini.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Dala biliyan 2.7 domin ayyukan jin kai a Sudan. Hoto: AP

Ba wai tana alhinin rashin samun tallafin a kan lokaci ba ne, har ma da yadda kasashen duniya suka zura ido ba tare da daukar wani mataki ba.

"Idan na ce mun gaza wajen yin abin da ya dace a Sudan, ina nufin abin takaicin yadda kasashen duniya suka kasar ganin abin da ke faruwa a Sudan din ne. Wasu sun ce ai hankalin duniya ba a kan Sudan yake ba," inji Wosornu.

Bukatar ayyukan jinƙai

Akwai yunwa matukar gaske a duk fadin kasar, inda miliyoyin mutane suke neman agaji.

A jawabinta na kwanakin baya a taron tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Wosornu ta fayyace yadda kasar ke fama da matsanancin kunci.

"Mutanen Sudan na matukar bukatar agajin gaggawa. Akwai bukatar kasashen duniya su kai agaji cikin sauri," inji ta, a madadin shugaban OCHA Martins Griffiths.

"A takaice dai mun wofantar da mutanen Sudan."

Edem Wosornu, daraktan aikace-aikace a ofishin kodinetan Ayyukan Jin Kai a Majalisar Dinkin Duniya tana jawabi a game da matsalar da Sudan ke ciki. Hoto: UN

Yakin na Sudan wanda ya ki, ya ki cinyewa ya jefa kusan kananan yara miliyan 24 cikin mawuyacin hali kamar yadda UNICEF ya bayyana. Akalla yara miliyan 14 daga cikinsu na bukatar agajin gaggawa.

"Ka duba ka gani: Kananan yara miliyan 24 suna fuskantar yaki, daga cikinsu miliyan 19 ba sa zuwa makaranta. Mun shiga wata shekarar yanzu haka amma makarantu suna kulle. Nan da wasu shekaru, zai zama wasu yaran sun kasance sun kwashe shekara hudu a jere ba sa zuwa makaranta," in ji Lawler.

Kamar 'yan uwansu da suke Gaza, kananan yaran Sudan suna fama da rashin abinci mai gina jika saboda yadda kasar ke fama da yakin da ba su san mene ne dalilinsa ba.

Akalla kananan yaran Sudan miliyan 14 ne suke bukatar agajin gaggawa. Hoto: Others

"Bai kamata a ce yara suna fuskantar wannan kuncin ba; ba su cancanci fara jin kararrakin bama-bamai ba," in ji Lawler.

"Wasu iyalan sun yi kaura sau uku ko hudu. Misali, wasu iyalan sun bar Khartoum suka koma Al Jazira, aka tarwatsa su a can din ma a watan Disamba, inda suka koma wani wajen daban. Don haka sun dade suna wahala, tare da kasancewa cikin yaki da ya kamata a ce an kawo karshensa."

Abubuwan da suke faruwa kamar kullun jiya-i-yau ake. A yanzu da yakin ya kai shekara daya ana gwabzawa, har babu wata alamar tsagaita wutar da mutanen kasar suke fata.

TRT Afrika