Daga Abdulwasiu Hassan
Ibrahim Garba Wala ya kasa farfaɗowa daga kaɗuwar da ya shiga na ganin yadda cikin 'yan mintina wasu ɓata-gari suka rusa masa kasuwancin da ya dauki tsawon shekaru yana ginawa cikin jajircewa da fafutuka.
Ɗan kasuwar mazaunin Kano, mamallakin wani kamfanin inatent na ShawaliNG.com da kuma FundME da ke sayar da kwamfutoci da harkar datar wata, ba shi kadai ke ƙidayar asarar da ya yi ba a daidai lokacin da Nijeriya ta gama ganin tashe-tashen hankula a titunan kasar, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ta janyo cire tallafin man fetur.
"Mun yi asarar komai da ke cikin shagon nan wanda ya kasance shi ne hedikwatarmu," Wala ya shaida wa TRT Afrika.
"Kayan katako na gida da kwamfutoci da firij da makuroweb da disfensa ta ruwa da takardunmu - kai sai da aka sace komai aka kuma lalata wajen, Hatta da tagogi da ƙyamare sai daka cire."
An yi zanga-zangar ne da nufin jawo hankalin gwamnati a kan halin da mutane ke ciki a faɗin ƙsar sakamakon hauhawar farashi.
Maimakon haka, cikin sauri tashin hankalin ya rikiɗe zuwa wata ɓarna da ta haɗa da yadda gungun jama'a suka dinga afkawa kan dukiyoyin gwamnati da masu zaman kansu.
A wani jawabi da ya gabatar ga ‘yan Nijeriya, Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a daƙile zanga-zangar, yana mai cewa gwamnati ta lura da koke-koken jama’a.
“Zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu sassan kasarmu, ta haifar da raɗaɗi da asarar da ba za a iya misaltAwa ba, musamman ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu,” in ji shi. "An lalata dukiyoyin al'umma da na ƙasa a yayin da muke sake gina abin da aka lalata."
Mummunar ɓarna
Sabuwar Cibiyar Harkokin Dijital wato Digital Industrial Park da aka gina a jihar Kano, wadda Hukumar Sadarwa ta Nijeriya NCC ta samar da ita a matsayin cibiyar kirkire-kirkire da inganta harkokin kasuwanci da sabbin sana’o’in zamani, na daga cikin manyan kadarorin gwamnati da ɓata-garin suka kai wa hari.
Yadda aka dinga gani ɓaro-ɓaro mutane suna kwashe kwamfutocin da aka tanada don haɓaka fasaha ya nuna ƙamarin da sace-sacen ya yi.
“Abin baƙin ciki ne da muka samu labarin cewa masu zanga-zangar sun ƙone tare da sace kayayyakin da ke cikin cibiyar Digital Innovation da ke Kano wadda aka shirya ƙaddamar da ita a mako mai zuwa don tallafa wa fannin fasaha,” in ji ministan sadarwa da kirkire-kirkire da tattalin arziki na dijital a Nijeriya a shafinsa na X ranar 1 ga Agusta.
An yi ta yaɗa hotunan sace-sacen a kafofin sada zumunta na wasu daga cikin jihohin da abin ya shafa da suka hada da Kaduna da Gombe.
Ya zuwa ranar 4 ga Agusta, adadin asarar da aka yi a fadin kasar a hukumance ya kai Naira biliyan biyar (dalar Amurka miliyan 31). Ministan masana'antu da kasuwanci da saka hannun jari Dr Doris Nkiruka Uzoka-Anite ya kira hakan da "yi wa tattalin arziki ƙafar ungulu".
Kamfanoni irinsu Barakat Stores, wani babban kanti a Kano da wasu ’yan daba suka kai hari, sun ce ɓarnar da aka yi musu za ta yi zai kai biliyoyin naira fiye da yadda aka yi kiyasin tun farko.
"Muna neman taimakon Allah da gwamnati don ganin an shawo kan lamarin," kamar yadda wakilin Barakat ya shaida wa TRT Afrika.
Har yanzu dai Wala na kokarin yin ƙiyasin ƙimar kayan daki da na’urorin kwamfuta da na’urorin lantarki da sauran abubuwan da aka lalata ko aka sace. Wani masanin inshora ya ƙiyasta adadin kadarorin a kan sama da naira miliyan 75.
Marasa aikin yi da yawa
Yawancin mutanen da ke aiki a kamfanoni masu zaman kansu da aka wawashe sun yi asarar dukiyoyinsu.
"Abin da ya fi tayar da hankali a cikin abin da ya faru tun farkon watan Agusta shi ne yawan iyalan da suka rasa hanyar samun kudin shiga. Ta yaya za ku iya ci gaba da ɗaukar ma'aikata idan kasuwanci ya mutu?" Wala ya shaida wa TRT Afrika.
Ɗan kasuwar yana da ma’aikata 30 da wakilai sama da 100 a Kano da sauran jihohin da abin ya shafa.
A dole Barakat Stores suka sallami ma'aikata saboda mummunar asarar da suka tafka.
“Kafin a yi wannan ɓarnar, sama da mutum 300 ne ke samun abin dogaro da kai ta shagon,” in ji wani jami’in Barakat Stores. "Yanzu mutane da yawa sun koma 'yan ƙwadago saboda ba su da tsayayyen aiki."
Tsoron sake zuba jari
'Yan kasuwar da suka tafka asara a lokacin zanga-zangar a yanzu suna jin tsoron sake zuba jari don farfaɗo da kasuwancinsu saboda rashin tabbas da suke da shi.
Wala ya shaida wa TRT Afrika cewa "A gaskiya na rasa ƙwarin gwiwa wajen saka hannun jari a Kano ko kuma wani wuri a Nijeriya.
Masu Barakat Stores suna da wannan ra’ayi, duk da cewa kasuwancinsu a iya Kano ya tsaya.
“A duk lokacin da irin wannan abu ya faru, hakan zai hana mutane fitowa su zuba jari da gina sana’o’i ko kasuwanci da samar da ayyukan yi. Daga karshe jihar za ta yi ta samun koma baya da rashin ci gaba, kuma za a samu ƙarin mutane marasa aikin yi a inda dama can aikin ya yi ƙaranci," in ji wani jami'i.
Wala ya yi niyyar canza dabarunsa idan da lokacin da ya yanke shawarar sake saka hannun jari ya yi.
"Zan guje wa jihohin da ke da rauni ta fuskar tsaro. Har ma ina tunanin mayar da harkokin kasuwancina zuwa wajen ƙasar nan a halin yanzu domin mu gudanar da ayyuka daga nesa," in ji shi.
Ko ta yaya dai, masu kasuwanci suna fatan gwamnati za ta kiyaye yanayin tattalin arziki da kuma yin shiri sosai don kawo cikas.
Wasu 'yan kasuwar na ganin ya zama wajibi gwamnati ta tabbatar da cewa a duk inda ake kasuwanci akwai bukatar a ba da kariya, me ya sa ake jiran 'yan kasuwa su nemi tsaro da kansu? Ya kamata a samar musu da shi ne.