Maganin ya shiga tarihi a matsayin na farko da ke maganin cutar malaria da aka samar a Afirka, musamman a Tanzania.  / Hoto: Reuters

Daga Edward Qorro

Dan kasar Birtaniya da ya lashe kambin Nobel, Sir Ronald Ross bai yi azarɓaɓi ba a lokacin da ya kira cutar zazzabin cizon sauro da cuta mai kashe miliyoyin mutane, bayan ya gano cewar sauro ne ke saka wa ɗan' adam a 1897.

Sama da shekaru 100, cutar malaria na ci gaba da kashe mutane, inda Afirka ce ke kan gaba wajen yawan mace-macen.

A yayin da maganin cutar a kan lokaci ke tasiri, alamunta kuma duk iri guda a kan kusan kowa. Hakan ya sanya ake neman hanyoyi daban-daban na magance ta.

Wani kokari da cibiyar NM Africa mai binciken Kimiyya da fasaha a Tanzania (NM-AIST) ya yi ya samar da kwayar maganin cutar malaria.

Wannan magani na gargajiya da aka samar, an samar da shi ne daga ciyawar Cedrela odorata, wata ciyawa da ta fito daga dangin tsirran chinaberry, tana bayar da fata nigari na maganin cutar kuma babu wata illa da yawa.

“Magani ne tsantsa na gargajiya da ba ya dauke da wani sinadari, ba kamar magungunan da aka saba amfani da su na Bature ba,” in ji Dr. Shadrack Daniel, mai bincike a NM-AIST, yayin tttaunawa da Afirka.

Maganin, wanda har yanzu na bukatar tantancewa kafin a fara gwajin amfani da shi, zannan za a yi amfani da na’ura mai kwakwalwa da injina wajen tantance salon inganci wadannan tsirrai.

Maganin ya shiga tarihi a matsayin na farko da ke maganin cutar malaria da aka samar a Afirka, musamman a Tanzania.

Sauro ne yake sabbaba cutar maleriya. Hoto: Reuters 

Tare da hadin gwiwa da likitoci daga Cibiyar Binciken Magunguna ta Kenya (KEMRI) da Afirka ta Kudu, tawagar a cibiyar da ke Arusha sun samu nasara a watan Yulin nan bayan bincike da ayyuka na shekaru uku.

“Mun hada bangarori biyu don gano mene ne ake aiki kuma ta yaya,” in ji Dr. Daniel.

Kadara mai daraja

Cedrela odorata, tsirran da ya fi shuhura a Yammacin India da Tsakiya da Kudancin Amurka, ciki har da dajin Amazon, bishiya ce da ke da manyan gangar jiki da ke girma da sauri.

An kai ta kasashen yankin tsibiran Pacific da Afirka ta Kudu da dama, sai ta zama ta mamaye wasu yankunan.

Alkaluman Tsirran da Ake Magani da su a duniya sun bayyana cewar bishiyar na iya yin tsayin mita 40. Ganyayenta kuma ganyenta na iya yin tsayin santimita 80, yana fitar da wani wari mai kama da na albasa da tafarnuwa.

An fi amfani da bishiuyar a matsayin katako, wajen samar da kayan gado, kofofi da tagogi.

Biniken da ake ci gaba da yi a NM-AIST ya kara sabon abu, a yanzu bihiyar Cedrela odorata ta samu matsayi a likitance.

“Muna kan hanya tare da gwaji, kafin mu bayyana adadin da za a yi amfani da maganin don samun waraka daga cutar malaria,” Dr, Danirl ya fada wa TRT Afirka.

Ya yi amanna da cewa da zarar an fitar da maganin kasuwanni, maganin na gargajiya zai tamaka wa kasashen Afirka wajen maganin cutar malaria ta hanyar da ba ta da illa sosai. “Ba wai magani ne kawai ba; zai iya bayar da kariya daga kamuwa da cutar.”

Yayin da ake jiran amincewa, za a fara amfani da maganin na tsirrai a Tanzaniya kafin a kai ga sauran sassan nahiyar da ke fama da matsalar zazzabin cizon sauro.

An fara fafutukar wannan bincike ne a cikin shekarar 2021, wanda Shugaban Binciken O R Tambo na Afirka ya ba da tallafi kan gwaje-gwajen fasaha wajen isar da magungunan zazzabin cizon sauro.

NM-AIST ta sami dala miliyan ɗaya a matsayin tallafin ta wannan tsari.

Tare da haɗin gwiwa da Hukumar UNESCO ta Tanzaniya da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Ifakara, wannan bincike ya jagoranci saka hannun jari don gano magungunan zazzabin cizon sauro, da nufin kafa cibiyoyi da kuma tallafa wa kasuwancin magungunan zazzabin cizon sauro.

Matsalar nahiya

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), an yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 236 ne suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro (kashi 95 cikin 100 na masu cutar a duniya) da kuma 590,935 da suka mutu (kashi 97% na adadin duniya) a kasashen Afirka a shekarar 2022.

Dokta Shadrack Daniel mai bincike ne a kan wannan aikin. Hoto: Wasu

Gamayyar ƙungiyar shugabannin kasashen Afirka a kan Maleriya ta ce kasashe hudu da suka hada da Nijeriya da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Uganda da kuma Mozambik ne ke da kusan rabin masu fama da zazzabin cizon sauro a duniya.

Ana ci gaba da samun ci gaba wajen rage yawan kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, lamarin da ya sa nahiyar ta bar baya da ƙura wajen kawar da cutar nan da shekarar 2030.

Tun daga shekarar 2015, kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ya ragu da kashi 7.6 cikin 100, yayin da mace-mace ya ragu da kashi 11.3 cikin 100, sai dai dukkansu ba su kai ga cimma muradun wucin gadi na Ƙungiyar Tarayyar Afirka ba, na rage kashi 40 cikin 100 nan da shekarar 2020 da kuma kashi 70 cikin 100 nan da 2025.

Daga cikin kasashe mambobi 46 da ke bayar da rahoton bullar cutar zazzabin cizon sauro, bakwai sun samu raguwar kashi 40 cikin 100 na kamuwa da cutar ko kuma mace-mace.

TRT Afrika