Dakatar da kamun kifin na cikin dokokin da aka tsara a shekarar 2009 domin adana na’ukan kifi da suke neman karewa. Hoto Reuters

Daga Evarist Mapesa

Tafkin Victoria, tafki ne mai ban sha’awa da yake samar da abinci ga miliyoyin mutane a Gabashin Afirka. Tafkin na zagaye ne da duwatsu, da nutsattsun wuraren hutawa da birane masu cike da hada-hadar harkokin yau da kullum.

Tafkin wanda shi ne mafi girma a yankin Kudu da Sahara, wato kasashe masu yanayin zafi, ya yi daruruwan shekaru yana taimaka wa mutanen kasashen Tanzania da Kenya da Uganda wajen samun kudaden shiga ta hanyar ayyuka da suka kunshi kamun kifi da sufuri.

Amma kash! Yanayin sauyin yanayi ya musu tutsu, wanda hakan ya sa dole aka samu tsaiko a harkokin mutanen.

Tun daga watan Fabrairun bana, Gwamnatin Tanzaniya ta ayyana dokar dakatar da kamun kifi a tafkin ta kwana 10 a duk wata, musamman nau’ukan kifin sadin da Furu domin su rika samun damar kara hayayyafa.

Dokar dori ce a kan dokokin da aka tsara a shekarar 2009 ta hana yiwuwar karar da halittun na ruwa baki daya.

Yawaitar kamun kifi da sauyin yanayi sun jawo ragowar kifi sosai a Tafkin Victoria.

Kamar yadda wani bincike na Kungiyar Adana Halittu ta Duniya wato International Organisation for Conservation of Nature (IUCN) na shekarar 2018, ya gano, uku bisa hudun halittun ruwa da ke Tafkin Vitoria na fuskantar barazanar karewa saboda sauyin yanayi da yawaitar kamun kifi.

Dokar hana kamun kifin ta kwana goma duk wata na nufin masunta ba za su yi kamun kifi ba na kwana 120 a shekara.

Duk da cewa masana harkokin adana halittu suna da tunanin dokar za ta taimaka wajen inganta rayuwar albarkatun tafkin, masu kamun kifi a yankin Mwanza da Kagera da Geita da Mara da Simuyu sun bayyana cewa lamarin ya jefa su cikin wani hali.

Harkoki sun tsaya cak

Garuruwan Bwiru da Mswahili da ke Mwanza a Arewa maso Gabashin Tanzania da a da suke cike da hada-hadar mutane masu saya da sayar kifi daga cikin kasar da ma kasashen waje, yanzu sun fara komawa kamar ba su ba.

“Ba mu taba ganin an rufe takin nan ba a baya. Ku magabatanmu ba su taba ganin haka ba. Tafkin ne kadai hanyar samun abincinmu,” kamar yadda wani tsohon masunci da yake kamun kifi a tekun tun a 1982 ya bayyana wa TRT Afrika.

“Muna mamakin yadda gwamnatin ta yi tunanin wai rufe tafkin ne maslaha. Amma yaya makomar masunta irinmu da iyalanmu da suke dogara da mu? Ina za mu je yanzu?”

Tsarin dakatar da kamun kifin na kwana 10 duk wata ya shafi rayuwar daruruwan mutane 

Wani masunci a Mswahili mai suna Robert Charles yana cikin wadanda rayuwa ta musu wahala saboda tsarin, “Ba ni da wani aikin. Magana ce ta rayuwata yanzu,” in ji shi.

A Mwanza, Kungiyar Masunta ta bayyana cewa akalla iyalai 3,000 ne rayuwarsu ta ta’allaka kacokam a kan sana’ar kamun kifi a yankin.

Selemani Alfonce wanda iyalansa suke cikin wadanda suke dogaro da sana’ar ta kamun kifi ya bayyana cewa dole ya rage gudanar wasu muhimman abubuwan saboda yadda samunsa ya ragu sosai bayan dokar ta hana kamun kifi na kwana 10 a duk wata ta fara aiki.

“Rufe tekun na kwana 10 duk wata ba zai kara yawan kifi ba,” in ji Alfonce, sannan ya kara da cewa, “Amma tabbas zai kara jefa mu cikin talauci.”

Ra’ayoyi mabambanta

Tambayar ita ce shin rufe tafkin na kwana goma duk wata ya taimaka wajen samun karuwar kifin?

Wannan tambaya ce da ta samu amsoshi mabambanta daga masu ruwa da tsaki a harkar. Akwai wadanda suke ganin cewa tsarin gwamnatin zai taimaka wajen hayayyafar nau’ukan kifin, akwai kuma masu ganin ko da kuwa tsarin na da amfani, jefa mutane cikin talauci da ya yi, ya danne amfaninsa.

Samwel Nyerembe yana daya daga cikin wadanda suke goyon bayan gwamnati, ya ce tun yanzu an fara ganin amfanin tsarin, domin a cewarsa, ‘Nau’ukan kifin sun hayayyafa sosai’ a Tafkin Victoria a ’yan watannin da suka gabata.

“Kifin irin su Sadin da nau’in perch suna karuwa sosai idan ka kwatanta da lokacin da ba a fara tsarin rufe tekun ga masunta ba,” in ji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Nyerembe ya ce idan aka kwatanta kifin da aka samu a lokacin da ake rufe tafkin, da kafin a fara rufewar ne za a gane bambancin.

Wata mai kamun kifi mai suna Christina Petro ba ta yi gardamar abin da ta bayyana da ‘niyya mai kyau ta gwamnati’ ba na kokarin ganin na’ukan kifin sun hayayyafa, amma ta cewa tsarin na jefa mutane cikin kunci.

“Kwana goma sun yi yawa, ni din nan da nake magana ina fuskantar matsaloli. Idan ban je Mswahili ba, ba zan samu komai ba. Ina da iyali, ’ya’yana suna makaranta, sannan ba ni wata sana’ar bayan kamun kifi,” in ji Christina.

Christina Petro ta bayyana cewa kudaden da take samu a sana’ar sun yi baya sosai saboda tsarin.

Ta ce akwai bukatar gwamnati ta sake duba lamarin, da zimmar duba yiwuwar rage kwanakin.

Eva Mwasole mai sayen kifin daga Mswahili ya sayar a yankuna daban-daban na Tanzania ya ce tsarin bai yi wa kowa dadi ba.

Sara Joseph mazaunin Kitangili ya ce a duk lokacin da takun ke rufe, farashin kayayyaki kamar nama da kayayyakin lambu duk suna tashi.

Matsayar gwamnati

Furah Bulongo jami’in da ke kula da kula albarkatun ruwa na Tafkin Victoria ya kafa hujja da Dokokin Kula da Albarkatun Ruwa na 2009, doka mai lamba ta 66.1NN wadda ta ayyana datakar da kamun kifin na wani dan lokaci a duk wata domin kifin su samu watayawa su yi kwai da yawa.

Mahukunta sun ce tsarin ya taimaka wajen karuwar kifi a ruwan.

Ya ce tsarin dakatarwar ta wani dan lokaci a duk wata ba kara yawan kifin kawai ya yi ba kawai, ya kuma rage yawan rikici a tsakanin masuntan masu dimbin yawa.

“Da dokar kamun nau’in kifin sardin aka fara a matsayin gwaji. Idan muka samu sakamako mai kyau, za mu fadada dokar zuwa sauran nau’ukan kifi irin su perch da Sato,” kamar yadda Bulongo ya shaida wa TRT Afrika.

“Idan ka lura da kyau, za ka ga kifin sun karu a kasuwanni. Datakarwar ta ba halittun ruwan damar hutawa. Wannan ma wata nasara ce da muka dade muna nema.”

TRT Afrika