Daga Firmain Eric Mbadinga
Wani da bai kammala karatun makarantar gaba da sakandare ba Alhssane Thiam, mai sana'ar walda kuma mai sha'awar ƙirƙire ƙirƙire, ya kwashe lokaci yana mamakin ya rayuwa za ta kasance a gare shi da matsalar kuɗin da ta tilasta masa dakatawa da karatunsa ba ta bujuro ba.
A maimakon haka, wannan matashin ɗan asalin Mbar, wani ƙauye a yankin Fatick ta yamma maso tsakiyar Senegal, ya zaɓi ya yi amfani da baiwarsa da hazaƙarsa kan wata ƙirƙira da ta sauya yadda mutane a yankunan karkara suke amfani da mai wajen girki.
Rishon Alhassane mai amfani da mataccen mai an ƙirƙire shi ne kan yin amfani da abin da ke hannu - baƙin mai na mota da aka yi juyensa - domin samar da ingantacciyar masalaha wajen girki ga al'umomin karkara.
Tuni ake kallon ƙirƙirar tasa a matsayin abin da ya kawo sauyi a kauyuka inda makamashin girki irin itace da gas imma suna da wahalar samu ko kuma suna da tsada.
A Mbar, rishon Alhssane ya amfani mazauna yankin kimanin 26,000 waɗanda tsawon lokaci suke rayuwa kan kiwo da noma.
"Ina matuƙar alfahari idan na tuna cewa abin da na ƙirƙira yana bai wa mutane damar tsimin ƴan wasu kuɗaɗe daga man girki. Wannan shi ne sakamako mafi girma," ya gaya wa TRT Afrika.
Masarrafi mai sauƙi
Rishon yana da wani mafeshi da kuma tanki da ke ajiye mataccen mai, ainihin man mota da ya tashi daga aiki da ake samowa daga gareji kan kuɗi kaɗan ko ma kyauta.
Rishon yana ɗauke da wata kunama da wasu musarrafai. Yana hura iska ciki, abin da ke sa wa wutar ta ci gaba da ci. Akwai bututu guda biyu - ɗaya yana zagawa da man idan aka buɗe shi, ɗayan kuma yana bai wa iska damar wucewa.
Idan ana son kunna rishon, akwai buƙatar masu amfani da shi su kunna shi sannan su buɗe kunamar, don tabbatar da zagawar iska da gudanar mai akai akai.
Game da aiki, ana kwatanta rishon da rishon gargajiya, sai dai shi wannan yana da sauƙi sosai kan gas ɗin girki, itace da wutar lantarki.
Tsarin sayen nagari mai da kuɗi gida
Alhssane ya ƙuduri aniyar ƙirƙirar risho mai amfani da mataccen mai sai ya yi makwafinsa a shagon walda na mahaifinsa,cike da shauƙin samar da wani abu da zai amfani al'ummarsa kuma za a iya yin nasara.
"Tunanin ya zo min ne sakamakon buri da nake da shi na sauƙaƙa rayuwar iyayenmu mata, waɗanda a galibin lokaci suke Fafutikar neman mai don girki. A al'ummata, abu mai wahala ne su samu itacen girki. Shi kuwa gas,ya fi ƙarfin aljihun galibin gidaje," ya sheda wa TRT Afrika.
Alhssane na samun mataccen baƙin mai kyauta daga gareji. Idan mai gareji ya buƙaci a saya, farashin ya kai kimanin CFA 40 (US $0.065) lita ɗaya.
"Da mataccen man CFA franc 200, mai amfani da risho mai amfani da mataccen mai zai dafa abinci aƙalla sau uku kullum na tsawon wata ɗaya," ya bayyana.
Iyalai masu masu bayar da goyon baya
Mahaifin Alhassane, Sheikh Thiam kullum ya san ɗansa yana da baiwa da ke buƙatar a bunƙasa ta.
Yayin da ba zai iya jure ɗawainiyar makaranta ba, Sheikh ya saka Alhssane a cibiyar koyar da aikin walda.
Matashin ya tafi can Touba, mil da dama nesa da ƙauyensu, domin ya inganta baiwarsa sannan ya dawo gida kamar ba shi ba.
Kasantuwar yana da ilimin walda, sai ya fara haɗa rishon da zai zamar da shi mashahuri a Mbar da ma gaba da nan.
"Kowa na mamakin yadda rishon nawa yake da sauƙin sarrafawa da tasiri. Ka kunna wuta, ka matsa kunamar, shikenan," Alhssane ya ce.
Tsarin kasuwancinsa ya ƙunshi yin amfani da tsarin tallata abu mafi daɗewa a duniya: furtawa da baki.
Tuni ana neman rishon Alhssane ido rufe, abin da ya zaburar da shi ya ƙara girman aikin samar da kayan da kuma raba ƙafa wajen ƙerawa.
Yanzu ya ɗauki ƙarin ma'aikata da za su taimaka masa ya ƙera ƙarin kayayyakin sannan kuma su yi amfani da irin wannan tsarin a kayayyakin aikin gona, tantan da babura masu ƙafa uku.
"Muna sauya farashi da ke ba mu damar mayar da kuɗinmu da muka kashe, kuma a lokaci guda mu taimaki iyalan da ba su da ƙarfi sosai. Muna sayar da risho mai kai ɗaya kan farashin CFA franc 75,000 ($120) mai kawuna biyu kuwa ninkin farashin mai kai ɗayan, a cewar Alhssane.
Rashin samun digirinsa yanzu ba ya damun shi, saboda ya tsunduma cikin wani fagen ta hanyar ƙera ƙofofin ƙarfe da sauran kayayyakin da ake samar da su ta hanyar walda, Alhssane na da burin samar da aikin yi ga ƙarin mutane kuma ya amfanar da al'ummarsa.
"Ina fatan samun tallafi imma daga wajen gwamnati ko haɗin guiwa da ƴan kasuwa masu zaman kansu don na tallata hajata a babban mataki, musamman rishona mai amfani da mataccen mai,"ya sheda wa TRT Afrika.