A kowace safiya, Mary Muthoni tana zuwa filin kwallon kafa na Kibagare a babban birnin Kenya, Nairobi wanda ya raba wani filin gona daga unguwar da take zama wadda ba hukuma ce ta tsara ta ba.
Matar mai ‘ya’ya uku ta tsallake wani rami domin zuwa sashen da gonarta take. A yau tana kokarin shuka wani irin kayan lambun da ta ce ya fi saurin girma, kuma ya fi saurin samar da riba.
Sama da shekara 20, wannan gonar ta kasance hanyar samun abinci da kuma rufa asiri ga iyalai 40 da ke zama a unguwar. Kowanne na biyan tsakanin dala 50 zuwa dala 100 a kowace shekara biyu domin su yi noma a gonakin wadanda girmansu ya bambanta.
Yawancin filayen kanana ne, a wasu lokutan ba su wuce filayen da kowanne zai samar da buhun masara uku ba.
“Noman kabeji da alayyahu na fi yi, kuma a wasu lokutan ina noman masara. A kowace safiya ina girbe amfanin gona in saka su a cikin amalanke in yi yawo cikin unguwar domin sayar da abin da na samu a ranar,” a cewar Muthoni cikin bayanin da ta yi wa TRT Afrika.
A wani sashe na gonar, wasu mata biyu suna cire alayyahu kuma suna sakawa cikin wani buhu.
Daya daga cikin matan ta ce: “Ba ma noma a nan, amma kullum muna zuwa domin mu cire kayan lambu, sannan mu kira mai gonar da muka girbe amfanin ya gaya mana nawa ne amfanin.”
Misali a kan kilo biyar na alayyahu muna biyan manomi dalar Amurka biyu. Sannan sai a raba alayyayun a kananan dauri kuma a sayar a kasuwar Kangemi da ke Nairobi, inda mai sayarwan zai samu karin ribar dala biyu.
Ana sayar da wasu daga cikin amafanin gonar a rumfuna a kauyen Kibagare, yayin da ake kai wasu unguwar Kangemi mai makwbataka da kuma wasu kasuwannin a cikin birnin.
A gonar, wani mutum ya zo da janareto da dogayen bututun ruwan roba. Da alama yadda hakan ya ja hankalin manoman ne ya sa kowannensu ke kiran mutumin domin ya fara yi musu aiki.
Ba tare da bata lokaci ba mutum zai gane cewa kasancewar Kevin Momina a wurin na da muhimmanci ga wanzuwar gonar. Idan babu shi, zai zame wa manoman dole su rinka diban ruwa da bokiti daga ramin don su bai wa gonakinsu ruwa.
Momina ya saka janareton kusa da ramin, ya hada bututun sannan ya fara ba da ruwa ga bangaren da aka nemi ya bai wa ruwa. Yana karbar kudin da ya kai dala uku zuwa shida dangane da fadin filin.
“A lokacin rani, ya zama dole mu yi amfani da ruwa daga ramin duk da cewa gurbatacce ne. Akwai wani tsaftataccen tushen ruwa da ke kawo ruwan da ke gudana zuwa wasu wurare a wannan unguwar,” in ji Momina a hirarsa da TRT Afrika.
“Wannan ruwan ma na zuwa wannan ramin. Mukan bari ruwan ya cigaba da zuba cikin ramin har sai ya ture dattin, sannan zan tura ruwan da ya fi tsafta cikin gonar.”
Abinci a madadin wani abu
Wata kungiya mai zaman kanta, Farm Africa, wadda take taimaka wa kananan manoma wajen kara yawan amfanin gona, ta ce idan aka yi shi da kyau, noman birni zai iya taimaka wa mutane da yawa samun abinci da kuma kudin shiga.
Sai dai kuma cunkoson jama’a a irin wadannan unguwannin ya janyo karancin abubuwan more rayuwa ga mazauna wurin, wadanda yawancinsu suke iya samun matsalar rashin abinci mai gina jiki da kuma sauran rashin lafiya masu alaka da talauci.
Ramin, wanda shi kadai ne ke ba da ruwa ga gonakin na Kibagare, ya kasance wata hanya da sharar gidaje ke bi ta ciki a kowace rana. Bakin launi, kauri da kuma warin ruwan a ko wace safiya na nuni da irin dattin da ke ckinta.
“Ba mu da wata hanya ta sarrafa dukkan irin shara,” in ji Muthoni. “Muna fadakar da mazauna wannan unguwar da gwamnati ba ta tsara ba ka da su dinga zuba shara a cikin ramin domin mun dogara a kan ruwan ne don ban ruwa ga kayan lambun da muke ci.”
Wata kwararriya kan harhada magunguna (pharmacist) a kauyen Kibagare ta ce mutane na yawan zuwa sayen magani a shagon sayar da magani don samun sauki daga ciwon ciki.
“Yana da wuya mutum ya ce ciwon cikin na da alaka da ruwan ramin da ake amfani da shi wajen ban ruwa ga amfanin gonar da za a ci. Za a iya samun wasu abubauwa daban da ke janyo shi,” kamar yadda Sophie Murage mai harhada magungunan ta shaida wa TRT Afrika.
Wasu matasa irinta suna fitowa su fadakar da mutanen unguwar game da muhimmancin zubar da shara yadda ya kamata.
“Shawara kawai za mu iya bai wa abokan zamanmu kan muhimmancin tsaftataccen tushen ruwa ga wannan gonar domin dukkanmu muna samun abincinmu daga nan ne,” in ji Peter George, daya daga cikin matasan.
“Amma matsalar ita ce idan ba su samu wata hanya ba, mazauna unguwar za su jira zuwa dare domin su zuba shara cikin ramin a lokacin da ba wanda zai gan su.”
Mary Njuguna da ke zama a unguwar ta ce, babu kowa a cikin unguwar da ke iya yin amfani da gonar domin suna kusa da rami mai datti. “Ga mutane da yawa, gonar ta kasance hanyar samun kudi daya tilo, kuma kauyen na bukatar abincin da ke zuwa daga nan.”
A nasa bangaren, Momina, ya yanke shawarar kin amince wa duk wani wanda ya nemi yi masa aiki kafin karfe 9 na safiya, a lokacin da sharar da ke yawo cikin ruwan ta dan ragu kadan.
“Ina zuwa nan da wuri yadda ya kamata, karfe takwas na safe a yawancin lokuta, amma zama kawai nake a kan janaretona har sai na yarda cewa ruwan ya yi hasken da zai sa in iya tura shi da famfo.
Idan ma wani manomi ya nemi kara mini kudi don in yi da wuri, ba zan yi ba, wannan abincinmu ne, saboda haka dole in tabbatar da cewa ruwa mai kyau na tura don ni ma ina sayen kayan lambun nan,” in ji shi.
Mazauna ungwar da gwamnati ba ta tsara ba ta Kibagare sun ce fatansu na samun tsaftataccen ruwa ga gonarsu ya rataya ne kan sabon gwamnan birnin Nairobi.
Sun shiga shafukan sada zumunta kamar mazauna sauran unguwannin da gwamanti ba ta tsara ba a birnin don ganin cewa gwamnan ya cika alkawarin da ya dauka na samar da hanyar kwashe shara yadda ya dace.
Har zuwa dai lokacin da wannan zai samu, alhakin yin abin da ya dace tare da nauyin aiki za su cigaba da kasancewa a kafadun Momina ne.