Peter Muchui ya sha jinyar tarin fuka tsawon lokaci.

Peter Muchui ya gane kuskurensa na ƙin shan magani a kan ƙa’ida, inda a ƙarshe ya koma shan ƙwayar magani 16 har tsawon wata 18 bayan da ya kamu da mummunan nau’in cutar tarin fuka na (MDR-TB) da ba yin magani.

Watanni kaɗan bayan tabbatar masa da rabuwa da cutar da kuma samun lafiyarsa, sai aka fara ƙarancin maungunan tarin fuka a asibitocin Kenya.

Ya yi ta kakabin abin da ka iya faruwa da shi da a ce bai warke ba, Muchui ya yi ta gode wa Ubangiji da ya samu ya rayu.

"Maganar da muke a yanzu haka, babu magunguna. Ku ayyana mutumin da yaje shan magani na tsawon wata shida sai a ce ya rasa na kwana ɗaya.

"To tsarin jikin wannan mutumin zai samar masa da nau’in cutar na MDR-TB," Muchui, wanda a yanzu jakadan yaki da cutar TB ne ya shaida wa TRT Afrika.

Muchui wanda ya je ƙasashe 15 daga cikin 47 na Afirka ya yi ta ganawa da marasa lafiya da likitoci, ya san ainihin dalilan da suka jawo taɓarɓarewar al’amura.

“Na ƙirƙiri zaurukan Whatsapp a kowacce ƙasa da na ziyarta. Dukkan waɗannan zaurukan abu ɗaya suke tattaunawa a kai. Babu magungunan tarin fuka,” a cewar Muchui.

Yana jin takaicin yadda yanayin wasu daga cikin marasa lafiyan da ba su warke ba ka iya ta’azzara saboda ƙarancin magani.

“Ba mu da sahihan amsoshi a kan dalilin da ya sa ake ƙarancin muhimman magungunan TB. Na san inda matsalar take kuma na san zafinta. Ina jin takaicin yadda za a iya rasa rayuka da yawa saboda wannan matsalar,” ya koka.

Tsawon lokacin jinya

Marar lafiya kan kamu da nau’in cutar tarin fuka ta MDR-TB ne a yayin da jikinsa ya gaza karɓar matakin farko na magani, lamarin da ka iya sanya mutum a cikin matsanancin yanayi har cutar ta tsananta ta koma matakin ƙin jin magani ta kuma rikide zuwa nau’in XDR-TB.

Daga cikin dalilan da suka sanya cutarTB ba ta jin magani har da tsaikon da ake samu wajen shan maganin, wanda hakan shi ne babban ƙalubalen da kan samu marasa lafiyan da ma likitocin da ke duba su.

Muchui ya tuna da yadda ya dakatar da shan magani a shekarar 2017, mako biyu bayan da ya fara sha, Dalilinsa? “Ji na yi na samu sauƙi,” ya faɗa.

Bayan kammala allurar wata shidan da Muchui ya yi, sai kuma ya ci gaba da shan magunguna Photo: AP

Ashe bai sani ba, tuni nau’in cutar ya rikiɗe zuwa MDR0TB a jikinsa.

“Wannan yanayin ya wahalar da ni sosai. Na yi ta ramewa inda nauyina ya koma 45 daga 65. Duk safiya idan na tashi haka zan ga katifata ta jiƙe sharkaf da gumi; ta yadda za a iya matse ruwa daga jikin shimfiɗata,” ya ba da labari.

A maimakon ya dinga shan ƙwaya uku na maganin da aka fara rubuta masa, sai ga shi ya dawo yana shan fiye da biyar ma.

Sannan kuma aka rubuta masa wata allura da zai dinga yi kullum har tsawon wata shida, inda har sai da ya ɗauki hayar ma’aikacin jinya daga wata unguwa Kasarani da take wajen birnin Nairobi.

“Sai da na gundura sosai da allurar; har na zo ba na gane ko a ɓangaren dama ko a na hagu aka yi ta baya. Na kan yi baccin aƙalla awa biyu bayan kowace allura,” a cewar Muchui.

Bayan kammala allurar wata shidan, sai kuma ya ci gaba da shan magunguna.

Matsala ce da ta mayar da shi can baya inda ya faro. A dole sai da ta’azzarar lamarin ta sa matashin wanda ya karanta ilimin injiniya a jami’a ya dakatar da kasuwancinsa na gwanjo.

Abu ne mai ciwo ga mutumin da ke cikin shekarunsa na 30, wanda bai daɗe da zama uba ba. “Na haƙura da rayuwa. Iyayena sun kai ni wajen wasu ƙwararrun har ma da sakawa ana min addu’o’i na musamman, amma duk da haka rashin lafiyar ta ci gaba da ta’azzara.

Daga ƙarshe dai na koma cikin hayyacina tare da tunatar da kaina ina da iyalan da dole na ciyar da su da kuma ƴar da ke buƙatar renon uba,” ya ce.

“Ko bulaguro zan yi sai na dinga yin bidiyon yadda nake shan magani kullum na aikawa likitana,” Muchui ya fada.

An ayyana shi a matsayin wanda ya warke daga cutar tarin fuka a watan Disamban 2022. Bayan ya yi fama da cutar kusan shekara biyar, sai ya zama mai yaƙi da tarin fuka.

Kalubalen jinya

Sauyawa daga shan maganin tarin fuka na yau da kullun zuwa maganin cutar nau’in MDR-TB yana da ƙalubale, kamar yadda Muchui zai shaida.

Peter Muchui ya zama jakadan yaƙin da cutar TB.

Karancin maganin da ake fama da shi a yanzu yana damun Muchui kan abin da matsalolin biyu za su iya jawowa. "Nan da watanni biyu zuwa uku masu zuwa, ina Kenya za ta kasance?" ya ce. "Kuma mu tuna cewa fa muna gwagwarmaya ne don kawar da tarin fuka nan da shekarar 2030."

The latest Global Tuberculosis Report released by WHO on November 11 shows that an estimated 10.6 million people were diagnosed with the disease worldwide in 2021, up from 10.1 million in 2020 and reversing many years of slow decline.

Wani sabon rahoton cutar tarin fuka da WHO ta fitar a ranar 11 ga watan Nuwamba ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 10.6 ne aka tabbatar da suna dauke da cutar a duk duniya a shekarar 2021 da sama da miliyan 10.1 a shekarar 2020.

Annobar cutar ta yi mummunar tasiri kan samun damar gano cutar tarin fuka da magani da kuma illar cutar tarin fuka, a cewar WHO.

"Ci gaban da aka samu a cikin shekarun da suka gabata har zuwa 2019 ya ragu, ya tsaya ko kuma ya koma baya, kuma manufar kawar da tarin tarin fuka a duniya ta kauce hanya," in ji rahoton.

Babban tasirin da ya fi fitowa fili shi ne an samu raguwar adadin majinyatan da aka tabbatar sun kamu da tarin fuka a cikin 2020 da 2021, wanda ke nuna karuwar alkaluman mutanen da ke dauke da tarin fuka da ba a tantance su ba.

A shekarar 2021, kiyasin adadin wadanda suka mutu da tarin fuka ya ninka adadin da cutar kanjamau ke haifarwa.

"A ɗan gajeren lokaci, tarin fuka na iya sake zama babban sanadin mutuwa a duniya daga ƙwayar cutar guda ɗaya, wadda ta maye gurbin COVID-19," in ji rahoton na WHO.

TRT Afrika