Daga Pauline Odhiambo
Uniko Chikomo ya yi digiri na biyu a bangaren shari'ar kasuwancin kasa da kasa, amma sai ya kasance harkar da ya taso yana sha'awa, ita ce ta zama sana'arsa.
Kamar sauran matasa a kasar na Zimbabwe, Uniko ya sha fama da kalubalen neman aikin gwamnati, wanda hakan ya sa ya koma noma maimakon jiran samun aikin gwamnati. Abin ban mamaki, inda yake samun karfin gwiwa kuma shi ne kafofin sadarwa, inda ba a taba tunanin za a samu hakan ba.
A gonarsa mai girman eka 100 da ke da nisan kilomita 20 daga Babban Birnin Harare, Uniko yana noma lattas da wake da dankali da kabeji da sauransu. Amma noman kabeji ne ya fi kawo masa kudi.
"A bara, na girbi kabeji guda 300,000," kamar yadda ya bayyana wa TRT Afrika.
"Na fi sayar da abin da na girba a kasuwanninmu na cikin gida da masu sayar da abinci. Amma ina sayar da kadan a kasashen waje."
Uniko, wanda ya fara harkokin noma tun a shekarar 2019, yana cikin Kungiyar Matasan Manoma ta Zimbabwe, wadda ke taimakon manoma wajen tallata abin da suka noma ta kafofin sadarwa da sauransu.
Kasuwancin kayan gona ta Whatsapp
Uniko ya bayyana cewa yawancin nasarorin da ya samu suna da alaka ne da amfani da yake yi da kafofin sadarwa, inda a nan ne yawanci ya koyi hanyoyin tallata amfanin gonarsa a kasuwanni a ciki da wajen kasarsa.
"Muna da zaurukan Whatsapp inda muke tattaunawa yadda ake ba manoma tallafi da kuma yanayin kasuwannin da za mu kai amfanin gonarmu. Wasu daga cikinmu sukan tallata kayayyakinmu zuwa ga kamfanoni da suke bukatar kayayyakin abinci kai-tsaye daga manoma, sannan sukan yada bayanan kayayyakin noma na zamani da taraktoci da yadda ake noman rani a zamanance da sauransu," in ji shi.
"Muna kuma tattauna yadda za mu kare gonakinmu daga barayi da kuma yadda za mu bunkasa harkokin noma."
Kasancewar Uniko a zaurukan sada zumunta da dama sun taimaka wa Uniko tallata amfanin gonarsa zuwa kasuwanni a Turai da Dubai, inda nan na yawancin matasan manoman Zimbabwe suka fi kai amfanin da suka girba.
Yadda suke kara wa juna sani ya taimaka wa matashin mai shekara 31 wajen sanin kamfanoni da suke bukatar hatsi.
"Muna taimakon junanmu ne ta hanyar kara wa juna sani da nemo kwantiragin kamfanoni masu bukatar amfanin gona."
Da yawa daga cikin zaurukan suna da wakilai daga Ma'aikatar Noma, wanda hakan ya kara saukaka wa manoman hanyoyin samun bayanan da suke bukatar kai-tsaye.
"Muna kuma shirya ziyarar gonakin juna, inda muke zuwa mu ga yadda mutum yake aikinsa, sannan mu shawarci juna a kan yadda zai inganta aikinsa," in ji Uniko.
Karancin gonaki
Samun kayayyakin aikin noma na zamani da kuma sayar da amfanin gona da daraja ba abu ba ne mai sauki. Matasan manoman sukan fuskanci wasu matsalolin wadanda kafofin sadarwa kadai ba za su iya magance musu ba, ciki har da gano kasar da za ta fi kyau da noma.
"Babbar matsalarmu ita ce karancin gonaki a Zimbabwe. Matasan manoma da dama hayar gonaki suke yi na iyayensu ko 'yan uwa da abokai," inji Dokta Prince Kuipa, masanin harkokin noma, kuma daraktan aikaya a Kungiyar Manoman Zimbabwe a tattaunawarsa da TRT Afrika.
"Wasu sukan ba da hayar gonakin da suka jingina daga gwamnati ga wasu, wanda haka kan jawo asarar amfanin gona saboda tashinsu da a kan yi ba shiri."
An fara shirin ba da jinginar gonaki na gwamanti ne a shekarar 2000 domin mayar da gonakin wadanda a baya mallakin Turawa ne ga 'yan kasa bakaken fata. Sai dai duk da haka, shirin na samun cikas saboda matasa da dama sun gaza cika sharudan da aka gindaya saboda rashin kudi.
A karkashin shirin na yi wa harkokin filayen garambawul, an ware daya bisa uku domin matasan manoma, amma akwai bukatar masu sha'awa su nuna cewa za su iya yin noman ta hanyar nuna shaidar hada-hadar kudin asusun bakinsu, da kuma nuna shaidar mallakar wajen kiwo, idan kiwo za su yi.
"Wadannan sharudan sun dan yi tsauri domin sun fi karfin matasan manoma da dama wadanda ba su da karfin," in ji Dokta Kuipa.
Wannan ya sa matasan manoma da dama ba sa iya samun bashi da su zuba jari a gonakinsu.
"Sannan wata matsalar ita ce akwai karancin filaye a kasar, wanda hakan ya sa yawancin filayen kasar akwai masu su. Filayen kadan kawai ya rage da za a iya ba matasan,' in ji Dokta Kuipa.
Guguwar sauyi
Tun bayan da ya dare karagar mulki a shekarar 2017, Shugaban Kasa Emmerson Mnangagwa ya fara assasa wasu dokoki da za su ja hankalin matasa zuwa harkokin noma.
Tsare-tsaren gwamnati da suke goyon bayan harkokin noma suna kunshe ne a cikin shirin gwamnatin da ake kira "Pfumvudza" ko kuma guguwar sauyi a bangaren noma. A shirin, ana ba matasan manoma tallafi.
"Shirin Pfumvudza yana cikin shirye-shiryen tallafin kudi da gwamnatin ta alkawarta wa kananan manoma, amma duk da haka akwai sauran rina a kaba, musamman kasancewar ana wani yanayi na tabarbarewar tattalin arziki," in ji Dokta Kuipa, sannan ya kara da cewa, 'Yawancin manoman da ba su samu tallafin gwamantin ba, da kudinsu suke daukar nauyin komai."
Haka kuma kudin ruwan da ake daurawa a bashin ya yi yawa, inda yanzu ake biyan tsakanin kashi 12 zuwa kashi 15.
Noman hadaka
Dokta Kuipa ya shawarci matasan manoma da suke fuskantar matsalar rashin kudi da su hada hannun jari, su yi noma tare.
"Manoma da suke da gona amma ba su da isassun kudi, sai su hada hannu da wadanda suke da kudi domin a noma gonakin," in ji shi.
"Akwai Turawa da suka rasa gonakinsu bayan yi wa dokokin mallakar filayen garambawul. Wannan gyarar ta yi tasiri."
Aikin noma na hadaka ana yi ne ta hanyar yin yarjejeniya a karkashin kulawar Ma'aikatar Fili da Sufiyo.
Dokta Kuipa ya ce matasan manoma da suke sha'awar noma amma ba su da gona, za su iya shiga wani bangaren na harkokin noma irin su sayar da maganin feshi da kayan noman rani da sauransu.
Kafofin sadarwa na zamani sun taimaka. Misali, Kungiyar Manoman Zimbabwe suna amfani da kafofin sadarwa irin su Facebook da Whatsapp da Twitter da Instagram domin gano matasa masu harkokin noma da kuma koyar da su hanyoyin tallata amfanin gonakinsu.
"Wannan ne yake kara karfafa musu gwiwa domin cigaba da noma duk da kalubalen da suke fuskanta," kamar yadda Dokta Kuipa ya bayyana wa TRT Afrika.