Daga Dayo Yussuf
Ɗaidaikun mutane da ƙungiyoyi har ma da gwamnatocin ƙasashe dun daɗe suna amfani da fagen wasanni irin Olympics wajen bayyana manufofinsu.
Tun daga lokacin Yaƙin Cacar Baka zuwa yanzu, an samu lokutan da aka dinga bayyana manufofin siyasa da na masu fafutuka da ma saƙonnin da ake yaɗawa a wasu Wasanni a Gasar Olympics ko ma a baki ɗaya lokacin gasar.
A wajen Gasar Olympics ta 1936 da aka yi a Berlin, gwamnatin Nazi ta wancan lokacin ta yi ta yaɗa farfaganda inda ta yi ta ƙoƙarin nuna Jamus a matsayin ƙasa mai lumana da kuma ƙarfin iko.
Shekara 30 da suka wuce a wajen Gasar Olympics ta 1968 a Mexico City, 'yan gasar tsere na Amurka Tommie Smith da John Carlos sun dunƙule hannunsu sun yi jinjina don nuna girmamawa ga Baƙar Fata a wajen bikin ba da lambar yabo, lamarin da ya jawo hankali kan batutuwan 'yancin fararen hula da kuma na wariyar launin fara a kan baƙaƙen fata a Amurka.
A Gasar Olympics ta Moscow ta 1980 an ga yadda Amurka ta jagoranci kaurace wa zanga-zangar adawa da mamayar Soviet a Afghanistan. Sama da kasashe 60 ba su shiga wasannin ba.
Tsohuwar Tarayyar Soviet da ƙawayenta sai suka ƙaurace wa wasannin Los Angeles na 1984, wanda ya ƙara jaddada zamanin yaƙin cacar baka.
A shekara ta 2008, Gasar Olympics ta Beijing ta zama dandalin zanga-zangar nuna adawa da zargin da China ke yi na kare hakkin dan'aam, musamman kan Tibet da yadda take mu'amala da kananan kabilu.
Ko a Wasannin Tokyo na 2021 an yi abubuwa masu nasaba da fafutuka. 'Yar wasan kasar Amurka da ta samu lambar azurfa Raven Saunders ta naɗe hannayenta a saman kanta a kan mumbari, tana mai cewa hakan na wakiltar "matsalar inda duk wadanda ake zalunta ke haduwa".
An ci gaba da yin hakan
A Gasar Olympics da aka kammala a birnin Paris kwanan nan, an ga yadda ake nuna ƙyamar Isra'ila da Rasha, wanda ke nuna bambancin ra'ayin dan'adam da kuma ƙarfafa imanin cewa al'amuran gida ko na kan iyaka za su iya samun wani matsayi a fagen wasanni.
Isra'ila Saria, mai sharhi kan wasanni ta shaida wa TRT Afrika cewa, "AMutanen da ba su da dandalin da za a ji muryarsu ko a ga saƙonsu, sun yi amfani da gasar Olympics ne a matsayin wajen da za su jawo hankulan miliyoyin mutane."
"Akwai abubuwa da yawa da ke faruwa a wannan duniyar, kuma mutane da yawa suna nuna bangaranci. Siyasar duniya tana shafar su duka, don haka wace hanya ce mafi kyau fiye da bayyana ra'ayoyinsu a wajen manyan taruka?" Saria ta tambaya.
Ƙungiyoyin wasanni na duniya suna aiki da tsari, tare da takamaiman dokoki da ke tafiyar da wasanni da 'yan wasa, da yanke shawara. Amma waɗannan sau da yawa ana rinjayar su ta hanyar bin manufofin yankuna ko na siyasa.
Kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC) a hukumance ya jaddada matsayinsa na adawa da siyasantar da harkokin wasanni, kamar yadda aka zayyana a cikin kundinsa.
Makonni kadan gabanin gasar Olympics ta Paris, IOC ta ce, "Ganin cewa wasanni na faruwa ne a cikin tsarin al'umma, ya kamata kungiyoyin wasanni masu fafutuka a lokutan Gasar Olympics su dinga yin taka tsantsan a al'amuran siyasa."
"Babban al'amari a cikin wannan tsari shi ne al'adun al'ummar da suka karbi bakuncin," in ji Saria. "Alal misali, Faransa tana da tsarin al'adu da zamantakewa wanda ya bambanta da sauran al'ummomi. Suna da ra'ayi na siyasa na masu tsaurin ra'ayi da masu sassasucin ra'ayi. Don haka, duk wata doka da kuka kafa, kasar da za ta karbi bakuncinta za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta, ko da kuwa hakan yana nufin karya dokokinku," in ji Saria.
Hana Isra'ila zuwa gasar
Gasar Olympics ta Paris ta ci karo da kiraye-kirayen haramta wa tawagar Isra'ila shiga gasar saboda cin zarafin da gwamnatinsu ta yi wa Falasdinawa a Gaza. IOC ba ta kula da waɗancan kiran ba.
Masu shirya gasar sun kuma fuskanci kakkausar suka kan manufofinsu na kaurace wa hijabi ga 'yan wasan Faransa, wanda Musulmai ke kallonsa a matsayin wariya.
Bayan haka, an samu koma-baya bayan bikin bude taron, inda zargin da ake yi na The Last Supper ya saba wa majami'u da kungiyoyin Kiristoci.
A yayin da siyasa ta kunno kai, kuma rigima ta wuce wasanni, tasirin farko kan kasance na kudi da akida.
"Masu daukar nauyin ba sa son a ga ana alakanta su da wani abu na cece-kuce. A birnin Paris, wasu manyan kamfanoni sun janye tallafin bayan da aka samu takaddamar bude taron," Saria ta shaida wa TRT Afrika.
A ƙarshe dai irin wannan cece-kuce kuma ya shafi kowane dan wasa.
Ana samun ƙalubalen ne sakamakon yawan jama'ar da gasar ta ƙunsa. Gasar Olympics ya ƙunshi 'yan wasa sama da 11,000, kuma hakan kan sa ana dinga samun batutuwa daban-daban da ke jawo ce-ce-ku-ce.
Saria ta yi imanin cewa yayin da wasu 'yan wasa ke bayyana ra'ayoyinsu a fili kuma suna samun yabo daga wadanda ke da ra'ayin irin nasu, wasu suna yin taka tsantsan yayin da suke tunanin tasirin ayyukansu musamman game da yarjejeniyar tallafawa.