Daga Sylvia Chebet
Za a iya cewa mummunar tarzomar da Ƙudurin Dokar Kuɗi ta Kenya ta shekarar 2024 ta haddasa ta lafa, amma fa ta bar baya da ƙura a ƙasar ta Gabashin Afrika.
Matakin da gwamnatin shugaban ƙasa William Ruto ta yanke na miƙa kai bori ya hau ga masu zanga-zangar nuna ƙin jinin haraji ya janyo Manyan Hukumomin auna bashi na duniya guda uku sun rage matsayin Kenya daga matakin B zuwa na B-.
Rage matsayin na baya nan ya fito ne daga wajen S&P ranar 23 ga watan Agusta, abin da ya tura cikin abin da kasuwar bayar da lamuni ta ke kira da yankin "tarkace".
"Koma-bayan, yana nuni da ra'ayinmu da ke cewa matakin kuɗi da bashi na Kenya zai taɓarɓare biyo bayan matakin da gwamnati ta ɗauka na janye duk matakan haraji da aka gabatar a ƙarƙashin Ƙudurin Dokar Kuɗi na 2024/2025," hukumar auna matsayi ta Amurka ta faɗa.
Raymond Gilpin, babban masanin tattalin arziƙin Kasashen Afrika a Hukumar Kula Da Cigaban Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), ya lura cewa tasirin rage matsayin ba zai taƙaita ga lalitar gwamnati ba kaɗai, har ma shi kansa aljihun talaka zai ji jiki.
"Adadin kuɗin ruwa da Kenya take biya kan bashin da ake bin ta, bisa ga dukkan alamu, zai ƙaru. Waɗanda ke bai wa ƙasa bashi za su kalli lamarin a matsayin kasada, daga nan kuma sai farashin takardun kuɗi ko lamunin da ba ajiyayye ba wataƙila ya yi sama," ya gaya wa TRT Afrika.
Idan kuɗin ruwa ya ƙaru,a galibin lokaci yana da tasiri na bai ɗaya ne, har da mummunan ƙarin farashin kayayyakin masarufi.
Masana tattalin arziƙin sun ma fi damuwa game da girman tanadin gwamnati kan zuba jari domin samar da ayyukan yi da abubuwan more rayuwa kamar kiwon lafiya da ilimi.
"Alƙaluma sun nuna cewa ƴan Afrika mutum 750 suna rayuwa ne a cikin ƙasashen da kuɗin ruwan bashin da suka ƙarfa da suke biya ya fi zuba jari da suke yi a ɓangaren kiwon lafiya da ilimi," a cewar Gilpin.
Yadda ake auna darajar ƙasashe
Masu zuba jari da masu bayar da lamuni sun dogara ne da hukumomin da ke tattara bayanai da bayar da matsayi kan bashi don samun bayanai game da kasada da damarmaki da suke tattare da masu neman bashi.
Alƙaluma kan matsayin bashi na zama mai muhimmanci musamman idan mai zuba jari na waje bai da masaniya game da yanayin da ya keɓanta da ƙasa, abin da galibi tabbas ne a ƙasashe masu tasowa.
UNDP ta bayyana cewa alƙaluman matsayin karɓar bashi da S&P da CD da kuma Fitch suka raba suna da muhimmanci wajen bai wa ƙasashe masu tasowa damar su samu isasshen lamunin da zai ba su sukunin biya musu buƙatun cigabansu.
"Waɗannan ra'ayoyin sune sakamakon nazarin bayanai da aka tattaro kan tattalin arziƙi na manyan buƙatu, da cibiyoyi kuma shugabanci a kan wata ƙasa keɓantacciya, da kuma buƙatar sakamakon lamunin daga cibiyoyi da kuma mutane ɗaiɗaiku da ke aiki a cikin ko tare da ƙasa," Gilpin ya bayyana.
Shin irin wannan tsarin na nufin bayar da damar yin muna-muna ko nuna son rai? UNDP a baya bayan nan ta yi nazarin sakamakon matsayin karɓar bashi a faɗin ƙasashen Afrika don binciken inda aka samu son rai sannan ta sauya mahaɗa tsakanin sakamakon matsayi da matakin cigaba.
Binciken ya ce ba a nuna son rai wajen bayar da matsayi kan karɓar bashi a ƙasashen Afrika saboda hanyar tantancewa ta bai ɗaya da ake amfani da ita a faɗin duniya. al'amurra masu wuyan sha'ani
Binciken na UNDP ya nuna cewa ƙasashe masu tasowa sun tasirantu sosai da mummunan koma-baya da suka samu a matsayin karɓar bashinsu, abin da ya yi sanadiyar ƙarin ɗawainiyar neman bashi da kuma ƙaruwar kasadar ɗorewar bashi.
Kimanin kaso 95% na koma-bayan ya faru ne a ƙasashe masu tasowa, abin da UNDP ta yarda cewa ya yi mummunan tasiri kan ƙoƙarinsu na samar da sabon jari da kuma ci gaba da wanda ake kai.
Binciken ya bayyana cewa kafin a samu madaidaiciyar matsaya, hukumomi masu raba matsayi game da bashi na buƙatar bayanai sosai da kuma ikon aiwatarwa, abin da suka rasa yayin da suke aiki a ƙasashen Afrika da dama.
"Idan ba su da bayanai dole su yanke danyen hukunci", inji Gilpin.
"Lokacin da mu a UNDP muka gudanar da bincike a ƙasashen Afrika 19 don ganin mene ne shi wannan asarar da rashin sanin dahir ke jawowa, an samu dala biliyan $94. Wannan ya fi abin da ɗaukacin ƙasashen Afrika ke samu a matsayin tallafi kowace shekara.
Wannan daidai yake da kaso 80% na zuba jari a buƙatun ababan more rayuwa na shekara a Afrika, wanda aka yi ƙiyasin ya kai dala biliyan $93.
Dalar Amurka $74.5 jimillar kuɗaɗen ruwa da aka karɓa kan basussuka da ɗaukar nauyi ne da waɗannan ƙasashe 19 suka bari.
Wannan somin-taɓi ne kawai, ganin cewa binciken bai shafi sama da ƙasashe 30 a nahiyar ba.
"Waɗannan sune matsalolin da za mu iya magancewa kuma dole mu magance," a cewar Gilpin.
"Alhaki ne da rataya a wuyanmu mu kare makomar tattalin arziƙinmu," UNDP na aiki tare da wasu hukumomin da yawa domin bunƙasa ikon gudanar da bincike a ƙasashen Afrika, don tabbatar da cewa matakan tantance matsayinsu ta fuskar karɓar bashi an yi adalci, ba wai kawai an yi su ne bisa ra'ayoyin wasu marubuta da ba a nahiyar suke rayuwa ba.
Gilpin ya nanata cewa sanarwa tana da muhimmanci "Idan an rage wa wata ƙasa matsayi saboda kaza ko kaza, akwai buƙatar ƙasar ta sani domin su gyara," ya faɗa.
Dama ta sake samuwa
A Kenya, gwamnatin shugaban ƙasa Ruto na fama da bashin dala biliyan $78, inda ministan kuɗi, tun da farko a wannan watan, ke nuni da cewa, gwamnati ta yi shirin samar da kimanin dala biliyan $1.2 ta hanyar sake dawo da wasu harajin da suka yi baƙin jini.
Yayin da ƙasar na iya fuskantar koma-baya saboda rage matsayin a bangaren karɓar bashi na baya bayan nan, Gilpin ya hango haske a gaba.
“Rage matsayin na iya nuni da cewa adadi da girman jari za su shiga halin ha'ula'i, amma kuma ina masa kallon cewa abu ne mai kyau da gwamnatin Kenya ke yin sabon nazari game da ƙudirin dokar kuɗin - domin ganin abubuwan da za a iya ɗagawa da waɗanda za a iya cirewa domin daidaita kasafin," ya bayyana.
"Wannan ba lokacin yanke ƙauna ba ne. Lokaci ne na daidaita mummunar shimfiɗar da aka yi wa tattalin arziƙin Kenya."
S&P ta ce matsayin Kenya ba abin damuwa ba ne duk da koma-bayan, tana cewa ana sa rai da "kyakkyawar bunƙasar tattalin arziƙi da kuma ci gaba da samun tallafin kuɗaɗe daga waje".