Kenya na sa ran soma samar da rigakafin da za ta rinƙa fitarwa tsakanin 2026 zuwa 2027. / Hoto: AP

Daga Sylvia Chebet

Annobar korona ba wai bala’i ce kawai da ta shafi ɓangaren lafiya na duniya ba, ta kasance wani ɓangaren darasi ga kowa, musamman waɗanda suka zama ƙashin baya wurin samun rigakafin annobar wadda manyan kamfanonin samar da magunguna da wasu ƙasashen ke iko da su.

Dangane da wannan lamari da ya faru, sai Kenya ta ƙudiri aniyar kawar da dogaro da wata ƙasa ko kamfani dangane da batun rigakafi a nan gaba.

Ƙasar da ke Gabashin Afirka ta shiga Cibiyar Ƙasar da Ƙasa ta Rigakafi ta Duniya wato IVI a matsayin mamba a watan Yunin nan, wanda lamari ne da Shugaba William Ruto ya jinjina wa a matsayin wani mataki na dogaro da kai ta ɓangaren kiwon lafiya.

Ruto, wanda ya ɗaga tutar Kenya a lokacin buɗe taron a birnin Seoul da ke Koriya ta Kudu, ya ce Kenya ta koyi darasi dangane daga irin ƙalubalen da ta fuskanta a lokacin annobar.

“Lokaci ya zo ga Afirka ta samu ‘yanci ta ɓangaren lafiya ta hanyar cire kanta daga dogaro da abubuwa marasa ɗorewa da kuma zabura domin ta wadata ta hanyar samar da rigakafi,” in ji shi.

Susan Nakhumicha, wadda ita ce ministar kiwon lafiya ta Kenya, ta ce zaman ƙasar mamba a ƙungiyar IVI zai matuƙar taimakawa domin taimaka wa ƙasar samar wurin bincike da samar da rigakafi mai kyau a kuɗi mai rahusa.

“Bugu da ƙari, Kenya za ta fita daga jerin masu jiran taimako zuwa mai zaman kanta ta ɓangaren samar da rigakafi,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Kenya ta zama mamba a IVI a Yunin 2024. / Hoto: Statehouse, Nairobi

Musayar fasaha

A matsayin mamba a ƙungiyar IVI, Kenya a halin yanzu tana da damar mu’amala da kamfanoni da dama na duniya kuma za ta iya samun musayar fasaha daga kamfanonin.

A lokacin bikin wanda aka tabbatar da shigar Kenya IVI, Shugaba Ruto ya jaddada buƙatar a ba ƙasashe dama samun rigakafi ba wai don yadda ƙasashen suke ko kuma matsayinsu ba.

“A ɓangaren samar da rigakafi, babu wanda ke cikin aminci har sai kowa ya kasance cikin aminci,” in ji shi.

A ɓangarensa, darakta janar na IVI, Jerome Kim ya tabbatar da aniyar ƙungiyarsa wurin samar da rigakafi mai inganci da kuma ci gaban kimiyya wadda za ta kiyaye kamuwa da cututtuka da kuma ceto rayuka.

“A daidai lokacin da muke tunanin samun wadatacciyar rigakafi, dole ne mu yi niyyar hakan kuma mu ƙarfafa hakan,” in ji shi.

Ma’aikatar lafiya ta ce IVI za ta yi haɗin gwiwa da abokiyar haɗakarta Kenya BioVax da kuma abokiyar bincikenta KEMRI domin magance matsalolin cututtuka.

Abokan hulɗan uku za su haɗa kai domin gudanar da gwaje-gwaje na asibiti da kuma bayar tabbatar da cewa sun kai ingancin hukumar WHO, da kuma sa ido kan sayar da kayayyakin.

Shugaba Ruto ya buƙaci IVI ta ci gaba ƙoƙarin ƙirƙira da kuma inganta ɓangaren bincike domin gina tsarin kiwon lafiya mai inganci.

Rigakafin da ake son samarwa

Sakamakon irin waɗannan abubuwa da ke ƙasa, ministar kiwon lafiyar ta bayyana cewa Kenya tana da yaƙinin cewa Kenya ta shirya tsaf domin samar da rigakafin wata cuta da za ta iya ɓarkewa nan gaba.

Rigakafi dangane da kwalara da ƙyanda da rubella da typhoid na daga cikin waɗanda ake sa ran samarwa.

“Wannan zai ƙara haɓaka ɓangaren kiwon lafiya a matakin farko na Kenya da kuma tallafa wa kiyaye cututtuka,” kamar yadda Nahkumicha ta bayyana.

Jarirai sabbin haihuwa da kuma waɗanda suka ɗan girma sun zama suna cikin barazana sakamakon ƙarancin rigakafi waɗanda suka haɗa da na ƙyanda da rubella da oral polio da tetanus-diphtheria da kuma BCG.

Kasashen Afirka na fama da ƙarancin rigakafin. / Hoto: Others

Cibiyar nahiya

Kenya na da burin zama wata cibiya ta nahiya wadda za ta ƙware kan harkar samar da kayayyakin kiwon lafiya musamman rigakafi ga yara da mata masu tasowa da kuma rigakafin haihuwa.

Ma’aikatar lafiya ta Kenya ta yi ƙiyasin cewa ƙasashen Gabashin Afirka na neman aƙalla rigakafi ta kusan miliyan 150 a duk shekara ga yara da mata masu tasowa da yaran da aka haifa.

Masana kiwon lafiya sun yi ƙiyasin cewa sakamakon yadda ake samun ƙaruwar haihuwa da kaso 2.3 cikin 100 a duk shekara, buƙatar da ake da ita ta rigakafi za ta ƙaru.

TRT Afrika