Yawancin bidiyoyin da Maya ke wallafawa na tafiye-tafiyensa a kan kalle su aƙalla sau miliyan 204. Hoto: Wode Maya/Instagram

Daga Pauline Odhiambo

Dan ƙasar Ghana da ya shahara a amfani da shafin Youtube Berthold Kobina Winkler Ackon, wanda aka fi sani da Wode Maya, kan yi tafiye-tafiye a faɗin nahiyar wasu lokutan ma har gaba da nan don ya yi bidiyoyi da nufin daƙile irin labarai marasa dadi da ake yaɗawa a kan Afirka.

Buri ne da ba wai ya ta'allaƙa ne a kan yin bulaguro don kashe ƙwarƙwatar ido ko shaƙatawa ba, Maya yana wannana bin ne don ilimintar da mutane da kuma wayar da kai.

Idan aka kalli yawan mabiyan matashin mai shekara 34 a Youtube da suka kai miliyan 1.65 a matsayin abin da ya jawo masa yin suna, to sanya wa wani titi da ke birnin Legas na Nijeriya irin sunansa ma wani abu ne da ya sake fito da irin shahararsa da tasirin da saƙonsa ke yi a kan al'umma.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa ranar 31 ga watan Janairu ya ce — "Na ga an saka wa wani titi a Nijeriya sunana" — lamarin da ya matuƙar sanya Maya mamaki da farin ciki a yayin da yake nuna yadda aka ƙaddamar da titin mai ɗauke da sunansa.

"Wannan girmamawa ce sosai da aka sanya wa wani titi a Legas na Nijeriya, sunana," ya rubuta a shafin Facebook, inda ya wallafa hotonsa da ya ɗauka a jikin allon da ke ɗauke da sunan titin wanda aka ƙaddamar ranar 27 ga watan Janairu.

Cikin waɗanda suka halarci taron har da wani fitaccen mai amfani da Youtube ɗan Nijeriya Steven Ndukwu. Daga baya ya yaɗa wani hotonsa shi da Maya a Instagram.

"Na ji daɗin raka abokin aWode Maya wajen ƙaddamar da sabon titin da aka saka wa sunansa a Legas, duk da cewa shi ɗan Ghana ne," in ji Ndukwu, inda shi kuma Maya ya mayar da martani da cewa, "Yanzu na zama ɗan Nijeriya ni ma, ɗan'uwa!"

Martani masu daɗi

Yawancin bidiyoyin da Maya ke wallafawa na tafiye-tafiyensa a kan kalle su aƙalla sau miliyan 204.

"A bidiyoyinmu na Youtube muna ƙoƙarin sauya yadda mutane ke kallon rayuwa ta hanyar mayar da hankali kan ƙasa ɗaya a lokaci ɗaya. Idan har 'yan Afirka ba su fara bayar da tarihin Afirka d akansu ba, to ba za a daina ganin labaran kama-karya ba!" kamar yadda ya rubuta a wani bidiyo da ya wallafa kwanan nan kan wani malami a Lesotho da ke kiwon awaki.

Maya ya samu kyaututtuka na karramawa da dama a ƙasarsa da Afirka. Hoto: Wode Maya/Instagram

Mataki da aka ɗauka na girmama Maya wajen sanya wa wani titi sunansa a ƙasar da ba tasa ba ya janyo mutane sun ji daɗin hakan, inda da yawa suka dinga taya shi murna kan gudunmawar da yake bai wa kafafen watsa labarai da al'adun Afirka.

"Shi din ya nuna cewa kowa ma zai iya cim ma duk irin burin da ke ransu," in ji Agnes Wangeci, ɗaya daga cikin masu bibiyar Maya daga Kenya.

Tamuel Sol, wani masoyinsa daga Nijeriya ya yi amanna cewa ayyukan Maya sun zarce iyakoki, inda ya zama jakadan nahiyarsa ba wai ɗan cikinta ba kawai,

"Maya ya cancanci a saka wa titi sunansa a kowace ƙsa ta Afirka. Na ji dadi da aka yi haka a ƙasata Nijeriya," kamar yadda Sol ya shaida wa TRT Afrika.

Masu amfani da shafukan sada zumunta

Akwai dumbin mutane a Afirka da ke amfani da shafukan sada zumunta wajen wallafa abubuawa don wayar da kan mutane a kan nahiyar.

Ana lissafa Maya a cikin mutanen da suka fi tasiri tun daga shekarar 2017 da ya fara samun shahara lojacun yana karatun injiniyan jirgin sama a China yake kuma wallafa abubuwa a kan ilimin da yake samu. Daga baya ya bar aikinsa da yake yi ya koma wallafa bidiyoyi kawai,

Maya ya samu kyaututtuka na karramawa da dama a ƙasarsa da Afirka.

Yana da cikin fitattun masu amfani da Youtube shida da aka gayyata zuwa Taron Tattalin Arziki na Duniya a shekarar 2023. Ya kuma halarci Babban Taron TSaro na Duniya na Munich da ake yi a Jamus duka a 2023.

TRT Afrika