Daga Firmain Eric
MbadingaTony Stark, wanda aka fi sani da sunan Iron Man, ya gina na’urar da ke samar da makamashi ga mutum-mutumi tare da wani akwati a wani shahararren fim na shekarar 2008.
Injin ne ya samar da makamashi ga rigar silken Iron Man kuma hakan ne ya ba shi damar tsallake tarkon da aka dana masa a wani kogo saboda ya ci gaba da rayuwa don ya ceci duniya ta ci gaba da kasancewa a cikin fim din.
Ko dai a zahiri ko badini, wadannan ne kalaman masanin falsafa Plato - “dole uwar na ki”Dokta Victor Agbégnénou, wani likitan dabbobi ne dan Togo wanda ya kirki abubuwa da dama kuma mutum ne da ya dukufa wajen kirkiran sababbin abubuwa da a baya ba tunanin samar da su a fannin kiwon lafiya da kuma sadarwa.
Daya daga cikin abubuwan da Dokta Agbégnénou ya kirkira ita ce na’urar Polyvalent Wireless Communication System, na’ura ce da ta samar da wani tsarin intanet mai sauri ba tare da an yi amfani hanyar fibre-optic ba.
A nahiya kamar Afirka inda intanet ya zama wani kayan gabas ga mutane da dama, ana ganin na’urar polyvalent za ta samar da gagarumin sauyi.
Sannan masanin ne ya samar da wani tsarin aikin kiwon lafiya a fannin jini da ake kira arteriovenous permutation technique.
“Ana amfani da tsarin ne wajen farfado da wani sassan jiki ta hanyar amfani da hanyoyin jini. Hakan ya bayar da damar cire jini daga sassan jikin da ake so a yi hakan, ” in ji Dokta Agbégnénou kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ya fara kirkire tun yana yaro
Joseph Nye, wani farfesa ne a Jami’ar Harvard bangaren Kennedy School of Government, ya ce kimiyya da fasaha suna da matukar muhimmanci wajen ba kasa karfin fada a ji a zamanance.
Kamar sauran nahiyoyi, Afirka tana kunshe da mutane masu dimbin basira da hazaka wadanda suke aiki tukuru wajen ganin mafarkinta ya cika na samun karfin iko a zamanance.
Dokta Agbégnénou, wanda shi ne jagoran kamfanin fasaha na KA Technologies Group, kuma yana cikin hazikan masana kimiyya wadanda suke kara fito da sunan Afirka ta hanyar ayyukansu na kirkire-kirkire da fasaha.
“Na fara sha’awar bincike-bincike da nazari tun ina karami kuma na yi sa’a ga shi yanzu ina yin hakan,” in ji masanin kimiyyar kamar yadda ya bayyana wa TRT Afrika Hausa.
Dokta Agbégnénou da wasu tawagar masu bincike kimiyya da ke aiki karkashinsa daga kasashe daban-daban su ne suke tafiyar da kamfanin RETICE na kimiyya da fasaha a Afirka wanda yake da burin cike gibi a fannin makamashi da fannin ilimi.
“Har yanzu koyarwa ce ta keke da keke amma hanyoyin koyarwar sun sauya saboda a rage kudin samar da ilimi,” in ji shi.
Tsarin RETICE da ake kira “80/20” yana samar da hanyar da malamai da dalibai suke ganawa ta hanyoyin zamani ba tare da amfani da intanet ba.
“Hanyar sadarwar ta cika kaso 80 cikin 100 na bukatar sadarwar da ake da ita kuma hakan ya sa bukatar da ake da it ana intanet ya ragu da kaso mai yawa.
Wannan ya sa farashin intanet ya ragu. Kuma bukatar sadarwa ta hanyar intanet ya ragu da kaso 20 cikin 100,” in ji Dokta Agbégnénou
RETICE ya fitar tsarin farko da aka yi nasarar gabatar da shi ga jama’a a shekarar 2021 bayan jerin gwaje-gwaje kuma aka yada shi a duniya.
“Mun fara ne da wani karamin shiri da ake kira Université Sans les Murs. Daga nan sai aka fara amfani da abubuwan da muka samar a wasu jami’o’i biyu mallakin gwamnati.
Nasarar da aka samu ta sa Togo ta bayyana aniyyarta ta kai irin wannan tsarin zuwa duka sauran manyan makarantu,” in ji Dokta Agbégnénou.
Kalubalen kudi
Yayin da neman kasuwa ga wadannan sabbin kirkire-kirkire yana tattare da kalubale, samun kyautukan yabo daga cibiyoyi kamar Kungiyar Raya Al’adu da Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO da kuma Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) suna kara karfafa gwiwa ga masu kirkire-kirkiren.
“Muna shan wahala wajen samar da kudin tafiyar da aikace-aikacenmu. Saboda babu kasuwa yana wuya a samu masu zuba jari,” in ji shi.
A halin yanzu Dokta Agbégnénou da abokan aikinsa suna aiki a kan ayyuka da dama ciki har da tsarin daukar jarrabawa ta intanet.
Sannan tawagar masanan suna aikin kirkire-kirkire da samar da bayar horo kan tsarin manhajar karatu ga manyan ma’aikata na ma’aikatar ilimi mai zurfi da bincike-bincike na kasar Togo.
Nijeriya da Burkina Faso da Senegal suna cikin kasashen Afirka da suka bayar da oda na sabbin kirkire-kirkire ko kuma kulla yarjejeniya da cibiyar bincike ta Dokta Agbégnénou. Kazalika wasu kasashe a nahiyar Turai sun kulla yarjejeniya da cibiyar.