Daga Sylvia Chebet
A cikin manyan dazuzzukan Kongo masu lullube da koren ciyayi, mafarauta ne suke tana tarkonsu a rassa daban-daban yayin da suke jiran ganimarsu na dabbobi su sauka.
A halin da ake ciki kuma a arewacin yankin budadden dazuzzuka da ciyayi na yankin Yammaci da tsakiyar Afirka, wasu mafarauta suma sun bi sawu inda suke tonon rami suna tono rami tare da tsaga budadden kututturan dabino.
Burinsu shi ne su kamo mesan macizi, nau'in halittar da ke da hatsari da kuma Nau'in Aku mai launin toka na Afirka. Masu tara ire-iren dabbobi masu ban sha'awa suna neman nau'in halittun dabbobin biyu a fadin duniya.
Ana son Aku mai launin toka na Afirka ba kawai don yanayin gashin jikinsa ba amma har da hankali da basirarsa, An fi sanin nau'in halittar da iya furta kalamai daidai da na yaro mai shekaru biyar da haddace kalmomi har zuwa 200.
Hukumar kare hakkin dabbobi ta Duniya ta yi kiyasin cewa ana kama dubban namun daji kowace rana a Afirka kuma ana sayar da su a kasuwanni kan farashin biliyoyin daloli a duniya a matsayin dabbobi masu ban sha'awa.
"Muna magana ne game da aku miliyan goma sha biyu na Afirka masu launin toka da kuma mesan macizai kusan miliyan hudu da aka yi safarar su daga Afirka a tsawon shekaru 40 da suka gabata,'' kamar yadda Edith Kabesiime shugaban kungiyar da ke raji kan namun daji na ya shaidawa TRT Afrika.
Kuddade masu yawa
A yanzu haka, darajar cinikin namun daji a duniya a duk shekara ya kai dalar Amurka biliyan 30 zuwa 42.8, wanda aka kiyasta cewa dala biliyan 20 na cinikin namun daji ana yin su ne ba bisa ka'ida ba.
Hukumar kare Dabbobi ta Duniya ta nuna damuwarta game yadda kasuwanci na farautar dabbobi ke kara haifar da bukatar neman dabbobi masu sha'awa.
"A al'adata, za a iya kyamatar mutum tare da yin nesa da shi idan ka ajiye namun daji. Amma muna samun mutanen da suke ganin yana da kyau a ajiye namun daji a gida kuma a yi kwalisa da su," in ji Kabesiime.
Bisa ga yarjejeniyar cinikayya ta duniya kan nau'o'in halittu masu hadari, manyan kasuwannin dabbobi masu ban sha'awa suna Amurka da Kanada da Turai (Jamus da Birtaniya da kuma Faransa) da wasu kasashen Asiya, musamman Japan.
Samun fasaha ta intanet a duniya da tafiye-tafiyen ta jiragen sama zuwa ketare na kara habaka sha'awar samar da namun daji.
Ba abin mamaki ba ne ka ga hotunan mutanen sun dauki hoto da mesan maciji ko kumbiya ko kuma kunama a shafukan Instagram da Facebook.
Wasu nau'ikan namun daji da dama da suka hada da hawainiya da kunkuru na daga cikin haramtattun halittun da ake safararsu, kana wasu daga cikin wadannan dabbobi sun fito ne daga Kenya.
Bayan ga dabbobi masu rarrafe da tsuntsaye, Kabesiime ta bayyana cewa ana dada samun bukatu na neman namun daji kamar zakuna da damisa daga masu tara dabbobi, tana ganin hakan a matsayin wani yanayi da ke kara bukatun kasuwar.
"Yawancin iyalai masu wadata a yankin Gabas ta Tsakiya sun yi imanin cewa ajiye zakuna da damisa ko a cikin gidan mutum wani tabbaci ne da ke nuna mutun ya isa kuma yana da daraja," kamar yadda Kabesiime ya shaida wa TRT Afrika.
Kashi 10 cikin 100 na wadannan dabbobin da aka kama su ba bisa ka'ida ba sun isa inda aka nufa kai su bayan an kama su.
"Ta fuskar samar da kariya, idan aka yi asarar kusan kashi 90 cikin 100 na dabbobin da aka kama daga daji, hakan yana nufin muna ciyar da masana'antar da ke kamanceceniya da wani rami mara tushe." in ji Kabesiime.
Barazanar bacewa
Masu rajin kare namun daji sun ce sana’ar sayar da dabbobin na daya daga cikin manyan barazana ga nau’ikan namun daji da ake da su.
Hukumar kare dabbobi ta duniya ta bayar da rahoton cewa kashi 99 cikin 100 an shafe irin nau'in Akun Afirka masu launin toka a Ghana, kuma tuni dai nau'in ya bace a kasar Togo.
Daga lokacin da aka kama su, Namun dajin za su fara fuskantar tafiya ta cin zarafi.
Kabesiime ta bayyana cewa da zarar masu fataucin sun kama aku mai launin toka na Afirka, sai su sare gashin fuka-fukan don kada tsuntsayen su tsere. Daga nan za a saka su cikin kananan akwatuna ko keji don safararsu.
Su kuwa kunkuru da macizai, ciki har da manya nau'in kwallo na mesa da suka kai girman kafa biyar, ana cusa su ne cikin akwati.
Wadanda suka tsira da ransu daga tsawon balaguron da aka yi da su suna rayuwa ne cikin wahala ta sassan jiki da ta kwakwalwa har tsawon rayuwarsu.
"Ga babbar dabbar daji, rayuwa a matsayin dabba mai ban sha'awa tamkar hukuncin daurin rai da rai ne," in ji Kabesiime.
Fadakarwa da tsare-tsare
A matsayinta na shugabar kungiyar rajin kare dabbobi da namun daji na Duniya, Kabesiime ta kasance a sahun gaba a kokarin da ake yi na kawo sauyi a wannan yanayin.
A 2017, kungiyar ta kaddamar da wani yaki da aka yi lakabi da "Namun daji. Ba Dabbobin ban sha'awa ba ne" don ceton namun daji daga tsare su da ake yi a cikin gidaje a matsayin dabbobi masu ban sha'awa.
"Mun yi aiki tare da kafa kamar Facebook da Instagram don tabbatar da cewa ba a yi amfani da wadannan tashoshi ba don zaluntar dabbobi da sunan dabbobi masu ban sha'awa," in ji Kabesiime.
Hukumar kare dabbobi ta Duniya ta kuma samu manyan kamfanonin jiragen sama da su himmatu wajen samar da takunkumin hana namun daji da jiragensu ke jigilarsu a duniya.
Ana ci gaba da gangami kan shawo kan majiyoyi da masu wucewa wasu kasashe kan su dakatar da fitar da dabbobi zuwa kasashen waje.
Ana kara matsawa Amurka da Turai da wasu kasashen Asiya da Gabas ta Tsakiya lamba don dakile shigo da namun daji.
Kamar yadda Kabesiime ya jaddada, lokaci ya yi da ya kamata a ajiye namun daji a inda ya kamace su .
Hukumar kare dabbobi ta Duniya ta kuma samu manyan kamfanonin jiragen sama da su himmatu wajen samar da takunkumin hana namun daji da jiragensu ke jigilarsu a duniya.