Koffi Mensah Agbelessessi

Daga Firmain Eric Mbadinga

Ga farin ciki a dadandalin rawa, ƙafufuwa na jujjuyawa tare da bin kiɗan ganga, kuma fuskoki na murmushi da annushuwa.

Yaran Kungiyar Kpadomeviwo du Togo (AKDT) na yin rawa da manyan maraya shahararru, duk wata rawa da za a yi shaida ce ta irin kokari da jajircewar su.

A bayan fage, wani labari ne na daban. Ana fara shirin rawar ne da yadda yaran masu shekaru daga shiga zuwa ashirin ke musayar tufafinsu da a yawancin lokuta suka yi wa junansu yawa. Murmushinsu ne kadai ke wanzuwa, yana rufe irin wahalar da suke sha a rayuwa.

A yayin da suke haskawa, ga wani mutum a tsaye a kansu a matsayin mai ba su horo - Koffi Mensah Agbelessessi dan shekara 35, shi ne shugaban kungiyar rawa ta AKDT.

Wannan kokari ya fara ne bayan Koffi ya ziyarci gidan marayu na Atakpame, wanda shi ne na birni na shida mafi girma a Togo, don gudanar da rawa. abin da ya ga ni a wajen - yara mabukata da mata da suke cikin wahala - ne suka sanya shi fara daukar mataki.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Na ga bukatar wadannan yaran da kuma yadda matan suke kaunar su, duk da cewa ba su da wata dama a rayuwa. Kasancewar Atakpame garin da aka haifi mahaifiyata, na ji cewar ni ma dan garin ne. Na yanke hukuncin daukar nauyin wadannan yara. Sai na fara kokarin tattara kudade."

An fara da kadan-kadan

A baya a Lome, inda AKDT ta samu wajen zama a 2017, Koffi na yawo a kan tituna da gabar teku don kira ga yaran da ke son kyautata rayuwarsu.

Koffi Mensah Agbelessessi

A yayin da yake amfani da kudaden da yake samu daga rawa, ya kama hayar daki a unguwar Bè-Ahligo Dekadjev don samarwa wadannan yara da ba su da wajen zama gurin fake wa.

Yaran cikin nuna kauna na kiran sa da "coach", shaidar yadda suke girmama shi kuma suka aminta da shi.

A cibiyar AKDT, yaran da aka samo a kan tituna na koyon rawa, tare da sake gdawo da kimar su. Wasu ma na sake koma wa ga danginsu.

Amma ba koyaushe abubuwa suke da sauki ba. Wasu yaran ba sa son bayyana me suka fuskanta a baya; wasu lokutan, iyalansu na yin shiru kawai.

Gina amintaka

Domin samar da yanayi na gaskiya da rikon amana, Koffi da jama'arsa sun dinga yin tattaunawa da yaran. Maza na horar da yara maza; mata kuma na bayar da shawarwari ga yara mata. Ba wani batu da ba a tattaunawa a kai.

Ana tattauna wa kan komai a bayyane cikin gaskiya, daga kula da tsaftar jiki zuwa batutuwan lafiya, labarai da al'amuran rayuwa.

Koffi na kera 'yan kunne, sarka da sauran kayan ado na mata daga robobi, kwalaye da tufafi don taimaka wa kungiyar. Ana sayar da wadannan kayayyaki a Turai da wuraren baje-koli, inda ake samun karin kudade don taimaka wa wadannan yara da hana su koma wa kan tituna.

AKDT ta bunkasa tsawon shekaru, kuma na da tunanin kafa kungiyar rawa da yara.

Sun samu kwarin gwiwa daga yadda shugabansu yake rawa, yaran sun nemi da ya koya musu rawar.

Koffi ya fara hakan cikin farin ciki, yana sayo kayan rawa ga yaran, suna koyon abinda daga baya ya zama rawar kungiyar AKDT.

Abin ya wuce rawa kawai

Ana amfani da kudaden da aka samu a wajen rawa don ayyukan ilmantar da yaran, wadanda ba su da iyaye, ko ba za su iya koma wa wajen su ba.

A cibiyoyin koyon sana'a da dama, Koffi ya horar da yaran da aka kubutar.. Hoto: TRT Afrika

Koffi na amfani da shafukan sadarwa na zamani wajen tattara taimako ga wannan aiki da yake yi na sake dawo da su cikin al'umma. Kokarinsa na samun nasara inda yara da dama sun samu gyara rayuwarsu tare da dawo wa cikin al'umma.

Ba dukkan labarai ne ke karshe mai dadin ji ba. Wasu yaran, da sun taba zama karkashin kulawar matashin mai kirki na Togo, sun sake koma wa kan tituna suna garari.

Koffi ya dimautu da wannan matsala, ya san irin hatsarin da yaran nan ke fuskanta - kamar rashin tsaro, muzantawa da sauran nau'ikan fataucin yara.

UNICEF ta bayyana cewa, yara kanana kimanin miliyan 30 a Afirka na gararamba a kan titunan Afirka. A Togo kawai, da ke da yawan mutane miliyan takwas, akwai yara kanana kusan dubu 7,000 da ke gararamba a kan tituna.

AKDT ta zama wajen inganta rayuwar yaran nan, suna koya musu abubuwa sama da yin rawa da koyarwa; har da sana'o'i a bangarori irin su gyaran gashi, dafa abinci da gyaran ababan hawa. Ana yin dukkan wadannan abubuwa da taimakon masu bayar da gudunmowa.

A yayin da wannan kokari bai zama mai sauki ba, kyautayin wasu mutanen na bawa Koffi damar ci gaba da gudanar da ayyukansa. Daya daga cikin su mace ce mai suna Marie, wadda ta samu masu bayar da tallafi a Faransa da suke aiko da kudade kowanne wata. Suna aiko wa kowanne yaron CFA 20,000.

Koffi ya fada wa TRT Afirka cewa "Ana amfani da wannan kudi don sayen abinci da magunguna, tabbatar da an biya bukatun wadannan yara."

"Wasu daga cikin wadannan yara na tafiya kan tituna suna gararamba saboda matsalolin da ke da alaka da rikici ko shan muggan kwayoyi a cikin iyalansu, wasu kuma sun fuskanci muzantawa ne."

TRT Afrika