Daga Susan Mwongeli
TRT Afrika, Adana, Türkiyya
Teknofest, gagarumin bikin fasahar sararin samaniya mafi girma a Turkiyya, yana ci gaba da gudana a birnin Adana na kudancin kasar. An fara bikin fasahar na kwanaki biyar a ranar Laraba ta hanyar baje-kolin jiragen sama daban-daban.
Akwai jirage masu saukar ungulu da jiragen yaƙi, da kananan jirage marasa matuƙa UAVs - da ma wasu da yawa, kamar yadda aka baje kolinsu ta hanyar yin gasa da nune-nune da ƙara wa juna sani da sauran su.
Amma baje kolin ba a kan na'urori masu tashi kawai ya tsaya ba. An nuna ababen hawa na zamani da samfuran rokoki da, fasahar ƙere-ƙere, da jirage marasa matuƙa na ƙarƙashin ruwa. '
'A duk faɗin duniya fasaha na da muhimmanci. A yau ne ake baje kolin Teknofest a Adana na Turkiyya,'' in ji Yavuz Selim Köşger, gwamnan lardin Adana a hirarsa da TRT Afrika.
‘’Wannan biki ya nuna cewa Turkiyya ta kai wani matsayi mai matukar muhimmanci, musamman ta fuskar fasahar tsaro. Don haka, muna bukatar matasa su fahimci iyawar kasarsu,” in ji shi.
Gidauniyar Fasaha ta Turkiyya (T3) da ma'aikatar masana'antu da fasaha ta Turkiyya ne suka fara shirya taron tun shekarar 2018 tare da hadin gwiwar ma'aikatu da dama, da cibiyoyin gwamnati, da kamfanoni masu zaman kansu, da jami'o'i.
Mahalarta suna samun damar ganin duk wani abu da ya shafi sabbin fasahohin zamani kuma akwai gasa mai yawa da ke faruwa tare da masu ƙirƙira daga ko ina cikin duniya.
‘’Yau na zo nan daga tafiyar da makaranta ta shirya mana don ganin abin da kasata ke yi. Kuma na ga jirage da dukkan kayayyaki, kuma ina alfahari da kasata. Suna zaburar da ni sosai don in bayyana ra’ayoyina da kuma fito da abubuwa kamar haka,’’ in ji wani dalibi da ke halartar wasan kwaikwayon ya shaida wa TRT Afrika.
A ranar farko ta fara taron fasahar ƙere-ƙeren, sabon jirgin yaƙi mara matuki kirar Baykar na mai ƙera jiragen sama na Turkiyya Baykar ya fito a bainar jama'a.
Jirgin ya fara tashi ne shekara guda da ta wuce. A ranar Laraba ne Bayraktar TB3 ya yi tashinsa na farko a bainar jama'a tare da Bayraktar Akinci, wani UAV da Baykar ke ƙerawa, a taron Teknofest da ake yi a lardin Adana na kudancin Turkiyya.
Haka kuma an baje kolin wasu injunan sabbin na'urori, da suka hada da robobi na ban mamaki da jirage marasa matuka.
Daga manyan gasanni zuwa nunin ma'amala, da nunin abin hawa da iska, da gaske akwai wani abu ga kowa a nan.
Teknofest shi ne inda makomar ke bayyana - a zahiri. An fara ƙaddamar da shi a cikin 2018 kuma yana haɓaka tun daga lokacin, yana jan hankalin jama'a da yawa har ma da bunkasar fasaha a kowace shekara.
Wani abin burgewa shi ne, taron bai tsaya wuri guda ba. Ya yi rangadi a garuruwa daban-daban na Turkiyya. Bulaguro ne na kallon yadda fasaha ke tafiya.
A shekarar da ta gabata, domin tunawa da cika shekaru 100 na Jamhuriyar Turkiyya, bikin ya gudana ne a wurare uku: Istanbul, babban birnin kasar Ankara, da kuma birnin Izmir na Aegean.
Taron Adana da ke gudana shi ne karo na goma na Teknofest, ciki har da wanda aka gudanar a Azerbaijan shekaru biyu da suka wuce.