Samora Machel ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a shekarar 1986. Hoto: Getty Images

Daga Susan Mwongeli

Shekaru 36 da suka gabata, duniya ta yi asarar wani gwarzo na juyin juya hali. Samora Machel suna ne da har yanzu ke ci gaba da bayyana a kudancin Afirka a matsayin wata alama mai ƙarfi ta 'yanci da kuma adawa da mulkin mallaka.

An haife shi a ranar 29 ga Satumba 1933 a garin Chilembene na Mozambique, inda a can Machel ya fara rayuwarsa da ta zama silar zamowarsa jagora mara tsoro, gwarzon 'yanci, kuma jarumi wanda ya kalubalanci zalunci na mulkin mallaka.

Machel shi ne shugaban kasar Mozambique na farko bayan samun 'yancin kai.

Ya kasance cikin shugabanni masu hangen nesa irin su Patrice Lumumba na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Thomas Sankara na Burkina Faso.

Ƙuruciya mai daɗi

Machel ya shirya wa mutanensa hanyar samun 'yancin kai. Tasirinsa ya kasance mai ƙarfi. Sai dai shi da wasu ministocinsa da dama sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Afirka ta Kudu a ranar 19 ga Oktoban 1986, a lokacin da suke tafiya daga Zambiya zuwa Maputo, babban birnin Mozambique.

Da dama dai sun yi amanna cewa gwamnatin mulkin wariyar launin fata na 'yan tsiraru na Afirka ta Kudu ce ta haddasa hatsarin jirgin. Ya musanta zargin.

Tarihin ya nuna Machel ya taso a mai tawali'u. Iyalinsa, kamar sauran jama'a, mulkin mallaka na Portugal ya raba su da muhallansu a cikin shekarun 1950, wanda ya tilasta musu su jure mummunar gaskiyar mulkin daular.

A lokacin yana matashi. Amma duk da haka, ya samu ɗaukaka duk da ɗumbin ƙalubalen da ya ci karo da su na a jagorantar ƙungiyar 'yantar da Mozambique (FRELIMO) don yaƙi da mulkin mallaka ta Portugal.

Machel ya jagoranci Mozambique samun 'yancin kai a watan Yuni 1975, tare da juriya da ƙarfin hali.

Ƙungiyar 'yan gwagwarmaya

A matsayinsa na shugaban kasa na farko, ya ba da fifiko a fannin ilimi da kiwon lafiya, da sake fasalin kasa, inda ya tsara tsarin gurguzu wanda ya ƙara wa talakawa ƙarfi.

Samaro Machel ya fara gwagwarmaya ne bayan ‘yan mulkin mallaka sun tarwatsa danginsa da wasu da dama: Hoto: Getty Images

Tun a wancan lokaci FRELIMO ke mulkin kasar da ke Kudancin Afirka. Duk da tashe-tashen hankula na cikin gida da kuma tsoma bakin kasashen waje, jagoran kishin Afrikan mai kwarjini ya tsaya tsayin daka kan burinsa na samun 'yanci da dogaro da kai.

Tasirin Machel ya wuce iyakar Mozambique. Ya kasance fitilar bege ga wadanda ake zalunta a yankin kudancin Afirka.

Ya ba da mafaka ga masu fafutukar 'yanci daga kasashe irin su Zimbabwe, da Afirka ta Kudu da Angola, inda ya taimaka wajen gina wata babbar hanyar tinkarar 'yan mulkin mallaka da wariyar launin fata.

Machel shi ne shugaban kasar Mozambique na farko bayan samun 'yancin kai. Hoto: Getty Images

Tarihin Machel zai dauwama, yana ƙarfafa mutane don yin gwagwarmaya don 'yanci da adalci. Jajircewarsa ta 'yanci da cin gashin kansa ya tabbatar da matsayinsa na ɗaya daga cikin shugabannin Afirka da ake girmamawa.

TRT Afrika