Daga Sylvia Chebet
Tsawon watanni, Jabulani Ttsibande ya fara jin tsoro game da maganin da dogara da shi don magance ciwon da ke damun sa.
Mahaifin yara uku da ke da shekara 50 na fama da ciwon tarin fuka da ke bijirewa magunguna, kuma wanda maganinsa ke iya kai kusan shekaru biyu.
Jabulani ya fada wa TRT Afirka cewa "A baya ina shan kwayoyin maganin har guda 24 kowacce rana, sannan ga wani abun sha na gari d ake cikin wata leda da ake kira Palser da ba shi da dadin dandano, ba za ka iya sha ba tare a yogot ba."
Wannan ana maganar shekarar 2018 ne. Shan maganin ya zama wata tafiya da kamar ba z ata kawo karshe ba.
An mayar da shi zuwa asibitin gwamnati na Sizwe da ke Johannesburg, a lokacin da likitansa a asibitin Kudanci ya rasu sakamakon kamuwa da ciwon tarin fuka da ba ya jin magani (XDR-TB).
Damuwa
Yana tsaka da damuwa kan rasa likitansa da ya yi ne wasu masu bincike a Jami'ar Witwatsersrand da Kungiyar TB Alliance, wata kungiya mai zaman kanta suka saka shi a cikin wadanda za a yi gwajin sabon maganin cutar a kansu.
Alkawarin wa'adi kankani na shan magani, kuma a sha kadan, kasa da yadda aka saba sha a baya, kuma ciwon ba ya bijire masa. Hakan ya sanya shiga aikin gwaji na 'ZeNix' wand aa lokaci guda a Rasha, Jojiya da Maldova ma ana gwajin sa.
Yadda tarin fika ke wahalar da duniya ne ya sanya masana kimiyya neman wasu hanyoyi mafiya tasiri, marasa gajiyarwa da karancin shan wahala don tabbatar da mutane da dama sun samu cikakkiyar kulawa.
Tarin fika da ke bijirewa magani
Rahoton baya bayan nan kan Tarin Fuka na Duniya ya bayyana cewa, ciwon na TB ya yi ajalin mutane miliyan 1.3 a 2022, wanda ya sanya shi zama ciwo na biyu mafi kisa a duniya a shekarar bayan Covid-19 (Ya haura cuta mai katya garkuwar jiki).
Tarin fika cuta ce da ake dauka a cikin iska idan mai dauke da ita ya yi tari ko atishawa.
Cuta ce mai wahalar warkarwa, wadda ke bukatar marasa lafiya su sha magunguna kala-kala a tsawon watanni hudu zuwa shida.
Amma kuma marasa lafiya na iya fuskantar bijirewar maganin idan ya yi tsallake ko gaza amfani da shi yadda ya kamata.
"Nau'in tarin fika da ke bijirewa magani ya zama ruwan dare. Idan tarin fika da ba ya jin magani ya shiga wani gida, kowa na cikin hatsari," in ji Dr Moronfolu Olugbosi, Babban Darakta a Cibiyar Yaki da tarin Fuka, yayin tattaunawarsa da TRT Afirka.
Budadden sirri
A duk duniya an yi hasashen a 2022 an samu mutane 410,000 da ke dauke da nau'ikan ciwon tarin fuka da ba sa jin magani.
Dr Olugbosi na da ra'ayin cewa budadden sirri ne dalilin da ya sanya marasa lafiya da dama ke shan wahala.
"Babu hanyoyin magani da yawa, sun yi tsada kuma na daukar lokaci - na bukatar mara lafiya ya sha kwayoyi sama da 20 kowacce rana a tsawon watanni 9 zuwa 20."
An yi gwaje-gwajen ne a kasashen Indonesia, Kyrgizistan, Filifin, Uzbekistan da Vietnam da suke da yawan masu dauke da cutar tarin fika da ke bijirewa magani.
Kulawa mai inganci
Sakamakon da aka gabatar a Babban Taron Kungiyar Masu Fama da Ciwukan Huhu a Paris a watan November ya bayyana cewa amfani da maganin yadda aka tsara na warkar da ciwon da kaso 95, inda aka gwada shi kan marasa lafiya 319, kuma an saka musu idanu sosai a yayin maganin a kuma bayan kammalawa.
"A yau tsarin kula da lafiya zan iya samar da amfani da BPaL ga marasa lafiya bisa yakin cewa maganin zai warkar da cutar matukar aka yi amfani da shi yadda ya kamata," in ji Olugbosi daga Kungiyar TB Alliance.
Kasancewar an gwada dukkan tsarin amfani d amaganin na baya da na yanzu, Jabulani ya ce bambancin a bayyane yake karara.
"Ya sanya na ji dadin zamana a asibitin Sizwe. Na fara jin dadin maganin tarin fikar da ake yi min."
Kwayoyin magani 24 da yake sha a kowacce rana sun dawo guda biyar a mako, kuma kwayoyi biyu ne ake sha a sauran kwanaki hudun.
Kuma abun da ya fi dadi shi ne tsarin na bukatar a sha magungunan a kasa da watanni shida.
'Babu wata illa'
Jabulani ya kara da cewa "Babu wata matsala da na ke iya tuna ta same ni a lokacin da na ke amfani da maganin tun bayan fara amfani da shi a 2019. Na warke gaba daya."
Kafin BPaL, ana duakar sama da watanni 18, tare da yin allurori wajen yakar ciwon tarin fuka da ke bijirewa magunguna - inda kuma suke warkar da ciwon da kaso 50," in ji Dr Olugbosi.
Samun maganin BPaL na taimakawa sosai wajen yakar tarin fuka da ke bijirewa magani, wanda WHO ta bayyana a matsayin mummunar cutar da ke addabar dan'adam.
Kwararru na bayyana nasarar BPaL da tsarin amfani da maganin a gajeren lokaci, shan kwayoyi kadan da saukin amfani. in ji Dr Olugbosi. "Wannan zai sanya mutane da dama su dinga samun waraka daga cutar."
Karin bincike
Alkaluman WHO sun bayyana cewa ya zuwa karshen 2022 kasashen duniya 40 sun gwada amfani da tsarin na watanni shida don kula da masu dauke da ciwon tarin fuka da ba ya jin magani cikin sauri.
A gefe guda, ana ci gaba da gudanar da bincike don samar da maganin da ya fi wannan inganci da saukin amfani don yakar duk wani nau'i na cutar.
Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya na fatan cewa samar da sabon tsarin gano cutar, alluran riga-kafi da hanyoyin magance ta zai taimaka a yake ta gaba daya.
Shugaban na WHO ya kuma ce "Tsawon shekaru, kakanninmu sun wahala tare da mutuwa saboda ciwon tarin fika, ba tare da sanin cutar ce ta kashe su ba,"
"A yau, muna da ilimi da masaniyar abubuwan da su sai dai a mafarki su gani. Muna da shugabanci, muna da damarmakin da babu wani zamani da ya samu irin su a tarihin dan'adam: akwai damar rubuta tarihin kakkabe cutar tarin fuka gaba daya."
Karancin kudade
A yayin da ake da makoma mai kyau, har yanzu dai shugabannin ba yin yadda ya kamata. Fitar da kudade don yaki da tarin fuka ba ya biyan bukatar da ake so, kuma a kasashe masu karancin kudade, lamarin yana kasa da yadda ake tsammani tun 2019.
"A 2022 dala biliyan $5.8 kawai aka tanada don gano tarin fika, magance shi da riga-kafin cutar, kasa d arabin kudin da ake bukata na dala biliyan 13.
Zuba kudade a bincike kan cutar tarin fika yana kasa da dala biliyan daya a shekara, wanda shi ma kasa da rabin dala biliyan biyu da ake bukata ne a Tsarin duniya da aka yi.
Batun kawo karshen cutar tarin fika nan da 2030 ya ta'allaka ga jajircewar shugabanni.
Za a iya cimma wannan buri - amma fa idan ana da isassun kudade, in ji Dr Olugbose. Ya kara da cewa "Cigaba irin na samar da BPaL na nuni da akwai yiwuwar cimma manufar."
A jawabin da ta yi a wajen kaddamar da Rahoton Tarin Fuka na 2023, daraktar yaki da cutar ta WHO Dr Tereza Kasaeva ta ce "Muna bukatar a hada hannaye waje guda don cimma burin yakar cutar tarin fika baki aya."