Daga Emmanuel Onyango
A daidai lokacin da suka bijire wa matsin lambar da suke fuskanta daga kasashen yamma da na yammacin Afirka, ƙasahen Mali, Burkina Faso da Nijar a wannan makon sun yi bikin cika shekara ta farko da ballewa da kuma kafa ƙungiyar Sahel Alliance (wadda aka fi sani da AES a Faransanci).
A wani ɓangare na bikin, ƙasashen sun sanar da samar da sabon fasfo wanda jama’ar ƙasashen uku za su rinƙa amfani da shi a ƙarƙashin wannan sabuwar haɗakar tasu.
Wannan ne mataki na baya-bayan nan da ya ƙara tabbatar da cewa waɗannan shugabannin na soji a shirye suke domin ƙarfafa junansu.
A bara, sun ɗauki matakin barin ƙungiyar Ecowas, wadda suke ganin tana da alaƙa ta ƙut da ƙut da ƙasashen yamma, haka kuma ta kasa magance matsalar tsaro a yankin.
Haka kuma ƙasashen uku sun juya wa ƙawensu na yamma baya waɗanda suka haɗa da tsohuwar uwar goyonsu wato Faransa inda suka karkata zuwa ga ƙasashe irin su Turkiyya da Rasha da China.
Duk da cewa ba a kammala batun ficewar ƙasashen daga Ecowas a hukumance ba, amma sanar da wannan sabon fasfo ɗin na haɗin gwiwa, wanda ake sa ran za a soma amfani da shi a kwanaki masu zuwa, wata alama ce ta kawo ƙarshen duk wata dangantaka da ƙasashen suke da ita da ƙungiyar ta Ecowas, kamar yadda masana suka bayyana.
Tuni Burkina Faso ta fitar da sabon fasfo ba tare da tambarin Ecowas ba.
Sai dai ƙawancen na ƙasashen uku ya bayyana cewa ba wai suna ware kansu bane amma ya ce sun samar da sabon faso ɗin ne domin ƙara haɗa kan yankin, kamar yadda Kemi Seba ya bayyana, wanda mai bayar da shawara ne na musamman ga shugaban mulkin soja na Nijar Abdourahamane Tiani.
"Yana da kyau a fahimci cewa hakan ba zai ware ƙasashen uku daga ƙasashen Ecowas ba, sai dai bayar da dama ga ƙasashen su ƙara samun haɗin kai a cikin yankin,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Zai iya zama ware kai idan manufar ita ce yanke alaƙa da sauran ƙasashe na yammacin Afirka, amma ba haka lamarin yake ba. Ba haka yake ba, kuma za ku ga cewa su (ƙasashen Yammacin Afirka) za su ƙara haɗa kansu,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Ga wasu abubuwan da zuwa yanzu ya kamata ku sani game da sabon fasfo ɗin, da tasirinsa da kuma yadda jami’an ƙasashen makwabta ke mayar da martani a kansa:
Me ya sa ake buƙatar sabon fasfo?
Ƙaddamar da sabon fasfon na daga cikin shirin ƙasashen uku na ficewa daga ƙungiyar Ecowas.
Kanal Assimi Goita na Mali, wanda a yanzu shi ne shugaban riƙo na ƙungiyar ta Sahel Alliance ya ce za a soma amfani da sabon fasfo ɗin domin ƙara sauƙaƙa tafiye-tafiye a tsakanin ƙasashen uku. Haka kuma ya bayyana cewa sabon fasfon zai taimaka wa ‘yan ƙasashen wurin tafiye-tafiye a faɗin duniya.
Ana kallon wannan fasfon a matsayin wani martani daga ƙasashen domin su nuna ƙarfinsu, kamar yadda masana ke bayyanawa, inda suka ɗora alhakin taɓarɓarewar al’amura irin waɗannan da riƙon sakainar kashi da Ecowas ta yi wa lamarin.
“Ina da tantama kan cewa ita kanta Ecowas tana da abin da za ta gyara da kanta,” in ji Desire Asogbavi, wanda ƙwararre ne ta fannin ci gaban ƙasa da ƙasa wanda ke zaune a Dakar babban birnin Senegal.
“A bayyane take kan cewa matakin da Ecowas ta ɗauka ya samo asali ne daga wani wuri (daga waje)...babban nuna halin ko in kula ne,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ta yaya zai yi aiki?
Kasashen uku dai sun kasance mambobi ne na kungiyoyi biyu na yankin - Ecowas da kungiyar West African Economic and Monetary Union (wanda aka fi sani da sunan UEMOA da Faransanci).
UEMOA ƙungiya ce wadda ta ƙunshi ƙasashe takwas waɗanda dukansu waɗanda ake magana da Faransanci kuma suna amfani da kuɗi iri ɗaya wato CFA Franc.
A ɗayan hannun kuma, Ecowas, wadda ke da ƙasashe 15 a Yammacin Afirka wadda ke da manufar tsattalin arziƙi da siyasa da tsaro iri ɗaya, na da fasfo iri ɗaya da kuma damar shiga ƙasashen ba tare da wani shinge ba.
Mali da Burkina Faso da Nijar ba su warware ƙawancesu da UEMOA ba haka kuma sun bayar da tabbacin cewa za su ci gaba da ƙawance da ita.
Akwai yiwuwar samar da sabbin yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka a yankin.
“Ina da tabbaci kan cewa tafiya ba za ta zama matsala na,” kamar yadda Asogbavi ya bayyana.
Idan kuka kalli yadda waɗannan mutanen suke, sun kasance tamkar iyali ɗaya da suke ƙasashe daban-daban inda aksarin iyakokin, sun kasance iyakokin je ka na yi ka waɗanda Turawan mulkin mallaka suka sa.
“Ina da tabbaci (Sahel Alliance) za su tattauna kan batun hada-hadar mutane a yankin ba tare da shinge ba; haka kuma su ma ƙasashen na Ecowas za su ci gaba da bayar da dama ga mutane daga ƙasashen uku su rinƙa kasuwanci,” kamar yadda ya yi bayani.
Wane tasiri zai yi a kan tattalin arziki?
Kasashen uku dai na da yawan al'umma miliyan 72, kuma dukkansu ba su da teku. Suna da wadata ta ma'adanai kuma sun kasance suna gano mai
Tattalin arzikinsu yana da kusanci da kasashen Mauritania, Senegal, Gambia, Guinea, Cote d'Ivoire, Ghana, Togo, Benin da Nijeriya wadanda kasashe ne da suke da damar shiga Tekun Atlantika.
Duk da yanke hulda da kungiyar kasashen yammacin Afirka, har yanzu kasashen uku suna da wasu hanyoyin fitar da kaya zuwa kasashen waje ta Mauritania da Aljeriya, wadanda ba su cikin ECOWAS.
Haka kuma ƙawancen Kasashen Sahel ɗin kuma yana kulla huldar kasuwanci da abokan huldar da ba ƙawayen ƙasashen yamma ba kamar Turkiyya, Rasha da China.
Asogbavi ya ce "Ba na tunanin wata za a samu baƙin ciki ko wata ƙasa ta tsangwami maƙwabciyarta saboda halin da ake ciki.
"Suna da makwabta waɗanda a shirye suke su taimaka musu, misali kasashen uku suna da kyakkyawar alaka da Togo wadda tana da hanyar shiga teku, an samu matsala da kasar Benin amma mun ga wasu alamu masu kyau na warware wannan lamarin.
“Rashin damar iko da teku na dagula lamura, amma ba na ganin Senegal za ta hana su amfani da tashoshin ruwanta,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Tsarin cinikayya maras shinge tsakanin ƙasashen Afirka, wanda ya kawar da shinge tsakanin ƙasashen nahiyar, a halin yanzu ana aiwatar da shi a faɗin nahiyar. Hakan na ƙara tabbatar wa shugabannin sojin ƙasashen damar shiga wasu kasuwannin a nahiyar tare da rage dogaro kan makwabtansu na kusa.
Yaƙi da masu tayar da ƙayar baya
Tabarbarewar matsalar tsaro da kungiyoyi masu dauke da makamai da ke a yankin Sahel ke haifarwa na daya daga cikin dalilan da shugabannin sojojin suka bayar na kwace mulki.
Kungiyar ECOWAS ta ce barazanar da kasashen uku ke yi na ficewa daga kungiyar za ta gurgunta musayar bayanan sirri, ganin yadda rikicin ya bazu a kan iyakokin kasashen.
Sai dai masana sun ce kungiyar Tarayyar Afirka AU ta ba da wata hanyar da za ta magance rikicin yankin Sahel.
“Sun yi alƙawarin kawo ƙarshen rikici a nahiyar zuwa shekarar 2030. Ina ganin wannan dama ce ta nuna wa duniya da Afirka cewa akwai wata ƙungiya a nahiyar wadda ta damu da zaman lafiya da tsaron nahiyar,” in ji Asogbavi.
“Ina ganin akwai buƙatar shugabanin AU su shiga wannan lamarin domin samar da tsarin tattaunawa da kuma jawo kowane bangare domin hawa teburin sulhu.