Wasu bayanai daga Ma’aikatar Tanadi, da Ma’aikatar Kudi ta kasar Nijar, sun nuna cewa tattalin arzikin kasar ya habaka da kashi 15 cikin 100 a shekarar 2022, a bisa ma'aunin GDP.
A kiyasin da aka fitar, kimar habakar da aka samu a GDP ta karu daga FCFA biliyan 8,270.8 a shekarar 2021, zuwa FCFA biliyan 9,569.9 a shekarar 2022. Wannan ya nuna an samu karin kashi 15.7 cikin 100 a cikin shekara guda.
To ko yaya aka yi Nijar ta samu wannan nasara? Wane siddabaru ta yi ko wane kokari ne ya kai ta ga hakan?
Malam Soly Abdoulaye, masanin tattalin arziki mazaunin Niemay, babban birnin kasar Nijar, ya ce bai yi mamakin wannan cigaba ba.
Ya shaida wa TRT Afrika cewa, “Ban yi mamakin jin wannan labari ba, duba da wasu kudurori na gwamnati mai ci ta Shugaba Mohamed Bazoum”.
“Gwamnatin Nijar ta dauki azamar inganta arzikin kasa ta hanyar takaita barna, da toshe cin hanci da rashawa, da kawar da almubazzaranci a harkokin gwamnati. Wadannan suna rage raunin tattalin arzikin kasa”.
Masanin, wanda ya saba sharhi kan harkokin ci gaban tattalin arziki a Nijar da Afirka, ya kara da cewa, “Kasancewar Nijar kasa ce mai arzikin man fetur, kara gangunan mai da ake tonowa a kullum zai habaka arzikinmu”.
“Akwai shirin gwamnati na rubanya tonon mai, daga ganga 20 zuwa ganga sama da 200. Sannan ga kuma shirin shimfida bututun mai daga yankin Agadem zuwa gabar teku a kasar Benin”.
Ko jama'a suna gani a kasa?
Tun da tattalin arziki ya habaka, ko al’ummar kasar ta Nijar sun ga wani sauyi a rayuwarsu ko kasuwancinsu, ko wasu harkokin gwamnati?
“A gaskiya ba a iya ganin wani sauyi a zahiri, kuma mutane ma ba duka suka san da labarin wannan cigaban ba”, kamar yadda AbdoulRazak Ibrahima Maila, wani dan jarida mazaunin Niemay ya gaya wa TRT Afrika.
Malam Soly Abdoulaye kara haske kan wannan inda ya ce, “Tabbas ya kamata habakar tattalin arziki ta bayyana a yanayi iri-iri, kamar ma’aikata su samu karin albashi, ‘yan kasuwa da mutanen gari su samu wutar lantarki da ruwan sha da magunguna a asibiti”.
“Sai dai abin dubawa shi ne, ba a faye ganin wannan sauyi cikin sauri ba ko a zahiri. Amma wani ci gaban da za a tsumayi bayyanar tasirinsa a fili shi ne aiwatar da aikin binne bututun mai tsawon kilomita 3,000, zai samar da aiki ga mutane”.
Shin ci gaban mai dorewa ne?
Bayanai daga Bankin Duniya da kuma Asusun ba da Lamuni na Duniya, sun nuna cewa ana sa ran ci gaban tattalin arzikin kasar Nijar zai haura kashi tara cikin ‘yan shekaru masu zuwa.
Wannan hasashen ya ta’allaka kan ci gaban da za a samu kan karin adadin gangunan mai da kasar ke samarwa.
Sauran matakan da za su janyo dorewar cigaban Nijar su ne zaman lafiya da fara samar da makamashin green hydrogen, da ayyukan inganta noma da kiwo.
Su ma masanan da TRT Afrika ta tuntuba, duka sun nuna fatansu na cewa matukar sanadin habakar bai ruguje ba, cigaban da ake samu a tattalin arzikin Nijar zai dore har jam’a su fara cin gajiyarsa a fili.
Sai dai kuma ba dole kiyasin ya tabbata ba gaba dayansa.