Daga Abdulwasiu Hassan
Tun bayan da rahotanni suka ambato Ministan Watsa Labaran Nijeriya, Lai Mohammed, yana cewa za a iya tuhumar Peter Obi, mutumin da ya yi wa jam’iyyar Labour Party takarar shugabancin kasa a zaben da ya gabata, da laifin cin amanar kasa, mutane suka soma yin muhawara kan batun.
A wata hira ta wayar salula da Peter Obi da ya yi da fitaccen malamin addinin Kirista Davidi Oyedepo, wadda ta watsu a shafukan sada zumunta, an jiyo shi yana rokon malamin ya taimaka masa ya ci zabe.
Obi ya roke shi da ya lallashi Kiristocin wani bangare na kasar su tabbatar sun zabe shi domin hakan tamkar “yaki ne da za su yi wa addini”.
Wadannan kalamai sun yi matukar haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan Nijeriya inda wasu ke ganin tsohon gwamnan na jihar Anambra ya sanya addini a cikin harkokin siyasa, ko da yake wasu sun goyi bayansa.
Sai dai a wani jawabi da Ministan Watsa Labarai Lai Mohammed ya yi yayin wata ziyara da ya kai Amurka, ya ce kalaman Mr Obi sun yi daidai da cin amanar kasa. A cewarsa, za a iya tuhumarsa da lafin cin amanar Nijeriya.
“Ana cin amanar kasa ne ta hanyar yunkuri da gwagwarmayar cire halastacciyar gwamnati ko kuma na wani bangaren kasa ba tare da bin doka ba, ko taimaka wa wani yin amfani da diflomasiyya wajen cin amanar kasa."
Shi dai Peter Obi ya mayar wa Lai Mohammed martani cewar shi bai aikata abin da za a iya ce wa cin amanar kasa ba.
A wasu sakonnin da ya wallafa shafins ana Twitter, Peter Obi ya ce sakon muryar da ake alakanta shi da shi na bogi ne, yana mai cewa bai yi yakin neman zabe bisa kabilanci ko addini ba.
Mene ne cin amanar kasa a Nijeriya?
Mun yi nazari game da ma’anar cin amanar Nijeriya da kuma abin da hakan ke nufi idan aka tuhumi mutum da aikata haka, inda muka tuntubi lauyoyi game da hakan.
Buhari Yusuf, wani lauya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ya shaida wa TRT Afirka Hausa cewa tuhumar cin amanar kasar iri biyu ce: akwai cin amanar kasa, wato treason a turance da kuma niyyar cin amanar kasa wato treasonable felony.
Ya ce idan aka tuhumi mutum da laifin yunkuri da niyyar cin amanar kasa, za a iya ba da belinsa, amma idan aka tuhumi mutum da laifin cin amanar kasa ba za aba da belinsa ba.
Ya kara da cewa laifin cin amanar kasa ya fi laifin niyyar cin amanar kasa muni a dokar Nijeriya.
Shi dai laifin cin amanar kasa an bayyana shi ne a matsayin kaddamar da yaki kan kasa mai cin gashin kanta ta hanyar amfani da makami ko rubutu da zummar dagula lamura a kasar.
“Ana cin amanar kasa ne ta hanyar yunkuri da gwagwarmayar cire halastacciyar gwamnati ko kuma na wani bangaren kasa ba tare da bin doka ba, ko taimaka wa wani yin amfani da diflomasiyya wajen cin amanar kasa,” kamar yadda wani lauya, Mainasara Umar ya bayyana hira da TRT Afrika Hausa.
Dokokin da Nijeriya ta tanada
Nijeriya ta yi fama da masu neman raba kasar ko kuma yi wa kasar zagon-kasa kamar yadda ta yi tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 inda aka yi yakin basasa a kasar.
Yakin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum miliyan uku da rabi.
Don guje wa irin wannan matsalar ne kasar ta tanadi dokoki da dama da suka yi bayani game da yadda kasar take da kuma yadda za a yi da wanda ya yi wa kasar zagon-kasa.
“Dokokin sun hana nuna bambanci na addini ko kabilanci na jinsi ko na bangaranci a kasar don a kauce wa irin abin da ya faru a baya,” in ji Mainasara Umar.
“A tsarin mulkin Nijeriya, sashi na daya da na biyu da na uku sun yi bayanin tsare-tsaren yadda gwamnatin Nijeriya za ta kasance,” a cewar lauyan.
Ya kara da cewar dokar ta yi “bayanin cewar duk wani matakin da mutum zai nema idan bai yi daidai da tsarin mulki ba kuma bai yi daidai da tanade-tanaden dokoki ba, to haramtacce ne kuma mataki ne mai neman kawo zagon-kasa game da zaman lafiyar kasa.”
Duk da cewa dokar kasar ta ba da ‘yancin fadar albarkacin baki, lauyan ya ce wannan ba hujja ba ce idan har mutum ya aikata abin da zai haddasa yamutsi ko tashin hankali domin dokar da ta ba da ‘yanci ita ce ta takaita ‘yancin tofa albarkacin baki kan lamarin yi wa kasa zagon-kasa.
Wacce kotu ce za ta iya sauraren karar?
A Nijeriya sau da yawa idan aka kai wanda ake tuhuma da laifin cin amanar kasa kotun majistire, akan janye ta a mayar da ita babbar kotu ta tarayya.
Wani lauya Abdurrauf Atiku ya ce babbar kotun tarayya ce take da hurumin sauraron kara ta cin amanar kasa.
Shi ma Buhari Yusuf yana da wannan ra’ayin cewa babbar kotun tarayya ce kadai ke da hurumin sauraron irin wannan kara.
Shi kuwa Mainasara Umar ya ce sauraren karar ya danganta ne da tsananin laifin da ake tuhumar mutum da shi.
Yadda za a wanke wanda ake thuma da laifin cin amanar kasa Cin amanar kasa babban laifi ne wanda idan kotu ta samu mutum da shi za ta iya yanke wasa hukuncin kisa.
Tun da ba a ba da belin wanda ake tuhuma da laifin, ta yaya zai kubuta? Lauya Buhari Yusuf ya ce za a wanke wanda ya ci amanar kasa ne kawai idan shaidu da lauyan mai gabatar da kara suka gaza alakanta shi da laifin.
Ya kara da cewa wannan na nufin cewa za a iya sakarsa ne kawai idan ba za a iya tabbatar da cewa yana da hannun a laifin ba.
Shi kuwa Mainasara Umar ya ce kubutar wanda ake tuhuma da laifin yi wa kasa zagon-kasa ta danganta ne da kwarewa da kuma jajircewar lauyan da yake kare shi.