Daga Abdulwasiu Hassan
A zahirance dai, ka'idar tsarin Robin Hood - na karɓa daga masu arziki a ba wa takalawa - zai zama mafitar da ake buƙata wajen magance matsalar rashin daidaito na tattalin arziki.
Muhawarar ita ce, harajin nawa ne zai isa a iya samar da wannan sauƙin, a abin da ɗan siyasar Amurka Benjamin Franlklin ya ce, ''A duniyar nan, babu wani abu da yake da tabbas, face mutuwa da haraji.''
A baya-bayan nan ne dai, ɗaya daga cikin hamshaƙan attajirai a duniya wanda ya kafa Microsoft wato Bill Gates, ya tayar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a Nijeriya bayan wata shawara da ya bayar kan cewa, dole sai ƙasashen Yammacin Afirka su kara yawan haraji da al'ummarsu suke biya.
"Adadin kuɗin haraji da ake karba a Nijeriya ya yi kadan sosai ," in ji Gates yayin ziyarar tasa.
Gates dai ba shi bane mutum na farko da ya taba fitowa ya yi magana kan batun ƙarancin harajin da Nijeriya ke karba ba idan aka kwatanta da ma'aunin tatttalin arzikin kasar na GDP.
Kazalika cibiyoyi irin su Asusun ba da lamuni na duniya IMF sun bayyana matsayar da wasu masana ke ganin ba daidai bane.
''A shekarar 2023, Nijeriya ta ƙara kashi 9.4 cikin 100 na ƙudaden shigarta na GDP. Wannan na ɗaya daga cikin mafi ƙarancin kaso da ake iya samu daga duniya da kuma nahiyar,'' kamar yadda shugaban shirin IMF a Nijeriya, Alex Schimmelpfennig ya bayyana.
''Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati tana da ƙarancin kudaden da za ta kashe wajen ciyar da al'ummarta gaba a fannin ci gaban kiwon lafiya da ilimi da sauran kayayyakin more rayuwa da dai sauransu.''
Gwada wasu sharuɗoɗi
Cire tallafin man fetur da aka yi a bara da kuma ƙarewar darajar kuɗin ƙasar na Naira sun janyo tashin farashin kayayyaki.
‘Yan Nijeriya da dama sun yi ta kokawa kan yadda za su samu abin dogaro da kai.
A kwanakin baya shugaban kwamitin kasafin kuɗi da sake fasalin haraji na shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa kwamitin ya gabatar wa gwamnati shawarar a cire harajin VAT gabaki ɗaya akan kayayyakin abinci da lafiya da ilimi da wuraren haya da sufuri da kuma ƙananan ‘yan kasuwa.
''Ɗaya daga cikin abubuwan da muka gano su ne, yawancin ma’aikata masu aiki ne kawai suke biyan haraji a Nijeriya,” inji shi.
''Don haka lokaci ya yi da suma za su huta, kuma hakan na nufin sai mun sake yin duba kan tsarin domin sauƙe nauyin da ke kan marasa ƙarfi ciki har da masu kananan sana'o'i.
Masu matsakaitan karfi da sauran masu arziki kuma za su iya biya a ƙarkashin ka'idar ci gaba kan haraji.''
Oyedele ya bayyana cewa kwamitin ya yi daftari na wasu sauye-sauyen da za su iya sake fasalin kuɗin kasar.
Dole sai shugaba Bola Tinubu ya mika wa majalisar ƙasar domin ta zartar ya zama ɗoka.
Raguwar masu matsakaitan ƙarfi
Ba kowa ba ne ke da kwarin giwa kamar Oyedele kan yiwuwar wannan tsarin haraji don cike gibin kuɗaɗen shiga na ƙasar.
Dakta Usman Bello na shashin tattalin arziki a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya na ɗaya daga cikin waɗanda suka yi imanin cewa, sanya haraji kan matsakaita da masu arziki don samun kuɗaden shiga yana cike da kalubale.
''Dole ne ku fahimci cewa, ba za ku iya ɗora haraji kan tattalin arzikin da tuni yake fuskantar koma baya ba, don haka shawarar cewa za a iya kara haraji kan kudaɗen masu yawa da ake samu zai sa tattalin arzikin ya dagule har ya zama ba za a iya jurewa da shi ba," kamar yadda Dakta Bello ya shaida wa TRT Afrika.
Ya bayyana cewa yawancin 'yan Nijeriya da ke yin balaguro zuwa ƙasashe wajen masu matsakaitan arfi ne.
''Sanya harajin kan masu matsakaitan ƙarfi zai kara yawan waɗannan suke barin ƙasar da suna samun rayuwa maiu kyau, Don haka, babu yadda gwamnati za ta iya tafiyar da manufofin sassaucin ra'ayi da ke da koma baya, inda ake tunanin cewa ƙarin haraji shi ne mafi kyawun hanyar samun kudaɗen shiga na gwamnati."
Rashin bin ka'idojin tara haraji
Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da suka shafi haraji a Nijeriya shi ne yadda mutane waɗanda ba sa aikin gwamnati ba sa biyan haraji.
Yayin da masu sukar batun ke korafin rashin bin ka'idar biyan haraji a tsakanin 'yan Nijeriya da dama, masu sharhi na ɗora alhakin farko kan riƙon sakainar kashi daga ɓangaren 'yan siyasa.
Ɗaya daga cikin ka'idojin farko na haraji shi ne nuna gaskiya. Na biyu shi ne mai biyan haraji ya san cewa ana amfani da kuɗinsa wajen tara kudaɗen ciyar da ƙasa gaba,” in ji Dokta Bello.
Ridwan Salisu Imam wanda ke sana’ar sayar da kayan abinci a Kano na daga cikin masu neman amsar tambayoyinsu kafin su biya haraji.
"Ina da hakkin sanin ko kuɗin da na biya a matsayin haraji ana amfani da su ta hanyar da ta dace, komai yana ɗaɗa komawa baya, yayin da jami'an gwamnati ke ginawa ko kuma su sayi gidaje masu daraja suna tura 'ya'yansu zuwa makaranta a ƙasashen waje, tsarin karatunmu yana cikin rudani." kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Ya kamata a kara yawan harajin da manyan kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kudaɗe kamar bankuna da kamfanonin kasa da kasa za su biya."
Sanya haraji kan masu arziki
Akwai masu ra’ayin cewa ƙara yawan haraji da masu arziki za su biya ba zai yi wani tasiri sosai ba kan matakin gwamnati na samun ƙudaɗen shiga tun da yawan masu arziki daga ƙasar ya kunshi mutane 'yan kadan ne daga cikin al’ummar Nijeriya mai mutum miliyan 218.
Wata ka’ida kuma ita ce, Nijeriya za ta iya cin gajiyar harajin kayayyaki da ayyuka na alfarma. Ɗaya daga cikin waɗannan kuwa shi ne, jiragen sama masu zaman kansu.
A baya-bayan nan ne Hukumar Ƙwastam ta yi kira ga masu gudanar da ayyukan hayar jiragen kan su samar da cikakkun takardu na jiragensu.
Kazalika gwamnati ta yi barazanar hana ayyukan kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu a shekarar 2021, sai dai ba a samu wani ƙwaƙwaran sakamako kan yunƙurin ba.